Tambaya ta (422)
:
Shin a Shari'ance Mene ne hukuncin Musulmi yayi Inshora (Insurance)??
:
Amsa
:
Ita dai Inshōra kamar yadda a Lārabci ake ƙiranta da suna (التأمين التجاري) ta kasu ne kashi-kashi, akwai Inshōrar da ake yiwa abin hawa kamar Mōta, Bābur, da makamantan su, ta yadda in wani Haɗari ya faru akan su za'a gyara maka su ko kuma a saya ma wani sābo, wasu kuma sukan yi wa gidajen su ko gurin kāsuwancin su Inshōra ne saboda ɓācin rānā, Sannan akwai Inshōrar da ake yiwa rāyuwa ko kuma lāfiya ta yadda in Mutum yayi wani Haɗari ko wata jinya mai tsanani, to sai kamfanin da yake Inshōra da shi ya ɗauki nauyin duk wani aiki da za ayi masa, ko kuma ya biya diyya idan mutuwa akayi, yā danganta da yadda akayi ƙā'ida ko yarjejeniyā da Mutum, dan haka dai akwai nau'uka na Inshōra dabam-dabam māsu yawa da Mutāne suke amfani dasu,_
:
To amma dangane da abinda ya shāfi hukuncin yin Inshōra a Shari'ance kuwa shine, Mālamai su kace dukkan wani nau'i na Inshōra harāmun ne bai halatta ba, saboda illolin dake cikin sa, domin kuwa a cikin Inshōra akwai garari, wato rashin tabbas na abinda aka ƙulla cinikayyar akan sa, kamar Misāli ace masu Inshōra suyi yarjejeniya da Mutum akan Inshōra na shekara ɗaya, sai ace da shi ana so dukkan bāyan wata guda zai bāda (₦100) dan haka a cikin wannan shekarar duk abinda ya faru na accident akan Mōtar sa ko Bābur ɗin sa za'a biya shi, to gararin dake ciki shi ne, bābu tabbas ɗin cewa Haɗarin zai iya fāruwa da shi a cikin wannan shekarar, bāya ga haka mai yin Inshōra a fakaice kamar yana kore dukkan wata Ƙaddara ne daga Aʟʟāн(ﷻ) da zata iya faruwa akan sa, a madadin yayi tawakkali ga Aʟʟāн(ﷻ) akan duk wani abu da ya faru da shi,
:
Sannan akwai nau'uka na Riba har guda biyu a cikin Inshōra, wato Ribar-Fīfīko da kuma Ribar-Jinkiri, domin ta yiwu bayan an gama yarjejeniya da Mutum ya bada kuɗin watan farko misāli (₦100) sai kuma yayi Haɗarin da wataƙila sai an kashe masa (₦2,000) akan sa, ko kuma ya kasance Mutum yā daɗe yana bada kuɗin sa har sun kai kamar (₦1,000) sai kuma yayi Haɗarin da bai wuce a kashe masa (₦100) kacal ba, Sannan kuma bugu da ƙāri shi ne, yin Inshōra dai dai yake da yin Cāca, domin kuwa yadda Ɗan-Cāca bā shi da tabbas haka shima mai Inshōra bā shi da tabbas, domin kana iya bada kuɗāɗen ka māsu yawa daga ƙarshe su iya zama maka asāra ba tāre da ka amfāni komai a cikin su ba, haka nan kuma kana iya bāda kuɗin ka misālin (₦100) kawai amma ka iya sāmun (₦10,000) a dalilin su, dan haka dukkan waɗancan illoli da aka ambata, gabā ɗayan su harāmun ne da Nassōsin Alƙur'āni da Hadīsai, Sai dai abinda Mālamai su kace shi ne, idan Mutum ya riga ya shiga Inshōra ba tāre da ya san cewa haramun bane sai kuma daga bāya ilimi yazo masa, to wājibi ne ya fita daga ciki, kuma koda wani abu ya faru da shi an bashi kuɗi, to zaiyi amfāni ne da iyākar adadin kuɗin da ya bayar ne kawai,
:
Amma idan ya kasance an tīlastā wa Mutum ne akan yayi Inshōra ba tāre da son ran sa ba, kamar yadda a wasu guraren akan samu hukumomin da suke tīlastā wa ma'aikatan su suyi Inshōra ta hanyar a riƙa yankar wani abu a cikin albāshin su duk wata ba tare da son ran su ba, to a irin wannan yanayi su waɗanda aka tīlastāwa ɗin ba su da laifi a wajen Aʟʟāн(ﷻ), laifi yana kan waɗanda suka tīlastā musu,
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
→AMSAWA←
Mυѕтαρнα Uѕмαn
08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
:
Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:
↓↓↓
:
"فتاوى إسلامية" (2/42)
:
"اللجنة الدائمة" (15/10)
:
"أبحاث هيئة كبار العلماء" (4/330)
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Daga Zaυren
Fιƙ-нυl-Iвãdãт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Tags:
Tambaya Mabudin Ilimi