UBA MAI HIKIMA

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
*ABOKIN FIRA �*
*Rubutawa:* _Dr. Muhammad Mansur Sokoto_

*DRS NA 022*

� *Uba Mai Hikima*
Wani matashi ne ya ji wa’azi a kan haqqin mahaifa. Ya tsima sosai, yana son ya biya mahaifinsa haqqin haifuwar sa da rainon sa da ya yi. Sai ya zo ya sami mahaifin nasa, ya ce masa: “Baba, yau ina son duk abin da kake so a duniyar nan ka gaya min shi. Zan yi maka da’a ba tare da gajiyawa ba”. Mahaifin nasa ya yi farin ciki da jin wannan
magana matuka. A nan kuma ya so ya koya ma dansa wani darasi mai girma. Sai ya ce masa, babu abin da nake sha’awa kamar lemun zaki.
Amma ina son kamar guda goma. Nan take yaron ya tashi ya zabura cikin kuzari da karsashi ya je kasuwa ya ciko kwando da lemun zaqi. Da mahaifinsa ya ga haka sai ya sa masa albarka. Ya ce, ciro min guda goma kawai. Ya sa hannu ya zaba masa nunannu guda goma.
Daga nan kuma sai mahaifin ya ce masa, ni ina sha’awar in sha lemun nan ne a saman bene. In da ma za ka goya ni ka kai ni can. Yaro ya ce, ai ba damuwa. Bismillah. Ya goya shi ya kai shi saman bene.
Sannan mahaifin ya dauki lemu guda daya ya kwalde. A maimakon ya jefa a bakinsa sai ya wurga shi kasa. Ya ce ma yaron dauko mani shi.
Yaro ya sauka ya dauko lemu a cikin mamaki da ta’ajjubi. Isowar sa ke da wuya sai ya tarar da mahaifinsa ya sake kwalde wani, kuma a gaban
idonsa ya sake wurga shi kasa. Abu dai kamar wasa sai ga shi duk �lokacin da ya hawo sai ya sake sauka don ya dauko lemun da
mahaifinsa ya jefa qasa. Nan take fuskar yaron ta fara canjawa. Kafin a kai lemu na bakwai yaron ya yi gajiyar hakuri ya ce ma babansa, mene ne haka kuma Baba? Sai mahaifin nasa ya ce, na san kana son ka rama
abin da na yi maka ne na alheri da kyautatawa. Ko ba haka ba? Ya ce, haka ne Baba. Ya ce, to, a lokacin kana karami sosai akwai watarana, ina zama na a qasa ka sa ni na je kasuwa in sayo maka kwallo. Da na kawo maka kwallon sai ka ce a saman bene kake son ka yi wasa da ita.
Kuma ka ce dole ne sai na goya ka. Da na hawo da kai sama sai ka rika jefa kwallon a kasa kana yi min kuka sai na xauko maka ita. Haka na yi ta zirga zirga yadda ka yi a yau tun bayan sallar azahar har aka kira la’asar ban ce maka na gaji ba ko na nuna maka damuwa ko kosawa.

*Darussa:*
▶ Sanin girman haqqin iyaye

▶ Kada ka gwale mutum idan bai yi daidai ba. Ka sa hikima a wajen lurar da shi da yi masa gyara�
📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail.com
Facebook: Jibwis Katsina L.G
WhatsApp: 07062584992, 08038977817, 08034453678, 08036958490.

Post a Comment (0)