SANIN GASKIYAR MUTUM SAI ALLAAH

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

*ABOKIN FIRA*
*Rubutawa:* _Dr. Muhammad Mansur Sokoto_

*DRS NA 004*
*Sanin Gaskiyar Mutum Sai Allah*
A wata Makaranta ne aka sace Alqalamin wata daliba. Sai ta kai kara a wurin Malaminsu. Malam ya hana kowa fita daga cikin
aji har sai an caje jakar kowa an gano wadda ta dauki wannan Alqalami. Da aka zo kan wata yarinya sai ta ki bari a buda Jakarta. Aka yi juyin duniya ta ce ita ba za ta bari a yi cajin Jakarta
ba. Da aka matsa mata sai kawai ta fara kuka. ‘Yan ajin duka sun dauka ita ta yi satar nan. Saboda haka aka ce aje ofishin shugaban Makaranta. Da suka zo Hedimasta ya tambaye ta, me ya sa kika yi sata? Sai ta ce, idan kowa ya fita zan gaya maka.
Hedimasta ya yi umurni kowa ya fita aka bar su su biyu a cikin ofis. Ko da suka fita sai ta bude ma sa Jakarta. Babu abin da ke
ciki sai gutsattsarin biredi da guntayen biskit da ‘yan Makaranta suka ci suka zubar. Hedimasta ya ce, me nake gani a nan? Ta ce,
wallahi wannan abin da nake tsinta kenan a kullum idan na je gida mu ci ni da mahaifiyata da kannena. Domin Mahaifinmu ya
rasu ba mu da kowa sai Allah! Shi ne na ji kunyar a buda wannan jakar a cikin aji abokaina su yi mani dariya.
*Darasi:* Ba kowa ne yake iya bayyana uzurinsa ba. Ka kyautata ma mutane zato. Sanin gaskiyar mutum sai Allah.

⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail.com
Facebook: Jibwis Katsina L.G
WhatsApp: 07062584992, 08038977817, 08034453678, 08036958490.

Post a Comment (0)