ABDULKADIR SALADIN 21

21. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.wordpress.com
...
Mahadi, a waje kam, da ganinsa ka ga Musulmi tamman. Duk irin abin da ya hana yi, shi ke fara bari, wanda ya ki bari kuwa, kisa ne ko bulala. Amma a cikin gidansa, in ka ga irin bidi'ar da a ke yi, ai sai gidan dan daudu ko gidan magajiya. Da shi da 'yanuwansa da halifansa, duk haka su ke. Irin gyaran da ya yi wa Sudan ke nan, ya halaka rayuka dubbai don ya sami ikon hana shan giya, da hana zuwa hajji, da kona littattafan shari’a !
MULKIN HALIFA ABDULLAHI
Bayan an kare zaman makokin Mahadi na kwana shida, ran nan sai Halifa ya komo gida. Nan da nan babu ko 'yar kara ya fita sha’anin mutuwa, ya shiga shirya mulkinsa. Yau fa duk Sudan a karkashinsa ta ke, shi ke ce a yi, shi ke ce a bari. Amma don ya nuna ban girma tsakaninsa da Mahadi, sai ya ce yana so ya yi wa kabarinsa kubba, watau gini wanda zai zama abin tunawa a tsawon zamani. Aka buge dakin da kabarin ke ciki, aka gyara filin wurin, aka shata kubbar. Halifa da kansa ya dauki cebur ya sari kasa inda za a saka tubalin farko. Daga nan sai ya wuce bakin rafi, mutum fiye da dubu talatin suna biye da shi. Suka je inda aka tara duwatsun ginin, Halifa ya dauki guda ya saba a kafada. Ganin haka duk mutanen nan sai muka shiga wasoson dutsen. Wadansu don doki har suka dauko duwatsun da suka fi karfinsu, suka yi ta ji wa kansu ciwo. Nan da nan aka tara dutse fiye da dubu talatin a dauka daya kurum. Da kayan aiki ya hadu, aka sa tushen gini.
Ranar da za a sa tushen nan, ran nan Halifa da kansa ya sa aka yi shela, ya ce jama’a duk su taru a gun kushewar Mahadi. Mutum, malam, kamar tururuwa. Sa’an nan Halifa ya zo ya dauki cebur ya fara tono kasa daga ramin harsashin ginin, sa’an nan kuma ya saka dutsen farko na harsashin gini. Daga nan fa birkiloli suka shiga aiki. Cikin ’yam mako kadan gini ya gamu. Ya yi kyau kwarai da gasken gaske. Ko ina ka bullo sai ka hangi tulluwarsa fara fat, an shafe da washiwashi.
Kusan in ce wannan gini shine kadai abin kirkin da Halifa Abudullahi ya yi cikin mulkinsa. Babu wani abin da ya isa a tuna da shi a mulkin nan, don babu kome cikinsa sai kashe kashen rayukan mutane, da cin amanu, da zalunci, da bidi’a. Halin da a ke ciki ke nan, a kullum sai an yi wa wani makirci, an cuce shi. Su Larabawa ba su taba zama ba, sai da gulmatar ’yanuwansu.
Ana cikin haka, ran nan sai aka yi kirana cikin fada. Na je na fadi a gaban Halifa. Sai ya ce ga takardar gwamnan Suakin ya aiko da ita, an ce wai tawa ce. Ya mika mini, ya kuma ce sai im bude ta a nan wurin im fada masa abin da ta ce. Na keta ambulon, na zaro takarda, na karanta. Na ga ashe ’yanuwana ne suka rubuto su gaya mini tsohuwarmu ta rasu. Ina cikin karantawa ashe Halifa ya kosa, sai ya ce im fada masa wanda ya rubuto ta, da abin da ke ciki maza. Na ce, “Kannena maza da mata su suka rubuto mini ita daga Turai. Sun ce tsohuwarmu ta mutu, kuma da sunana a baka ta mutu. Ta ce ta yi bakin ciki da ba mu sadu da ita ba, ga shi har za ta tafi gidan gaskiya. Kullum tana addu'a ga Allah, in sami kaina in koma gida, don bakin cikin rashina kusa da ita ya kara gaggauta mutuwarta."
Babu abin da ya fito bakin Halifa sai ya ce, “Rabu da ita. Ta mutu kafira, sabo da haka kada ka yi ko juyayin mutuwarta. Kai kana tutar Mahadi ne, ita tuwa wuta za a jefa ta. Babu abin da zai hada ku duniya da lahira." Jin haka hankalina ya tashi, sai ya ce im fita. Ni dai ban taba jin maganar da ta bugi zuciyata, irin wannan wadda Halifa ya yi mini ba. Tsakanin uwa ne fa da da. Da na koma gidana, na yi rigingine a bisa gado, na jawo takardan nan na sake karantawa. Hawaye na zurara a idona. Babu abin da ya kara sa ni kuka, kamar tuna jawabin da tsohuwan nan tawa ta yi mini, a lokacin da zan fito in zo Sudan. Da ta ga na dokanta bisa im baro gida, sai ta ce, “Kai, Rudolf, na ga dai kana son shiga duniya. Za ka tafi kasar da ba ka san kowa ba, kuma babu wanda ya san ka. Akwai ranar da za ka ce da ma a gida ka ke.” Ka ga jawabinta yau ya zama gaskiya.
Kashegari Halifa ya sake cewa in karanta masa takardan nan. Da na karanta sai ya ce im ba su amsa, cewa ni kam ina nan lafiya, ba na kukan kome, babu abin da ya dame ni. Bisa tilas na rubuta wannan karya. Na ce ga ni nan a kusa da Halifa babu abin da ya sha mini kai. Na yabi Halifa, amma yabon fatar baki. Domin a ko wace kalma ta yabo na sa alama, na nuna kishiyarta na ke nufi. Har wa yau kuma, na ce da ’yanuwana su rubuto wa Halifa takardar godiya, su aiko masa da kyauta, ni kuma su aiko mini da fam metan, da agogan hannu goma sha biyu don raba wa fadawan Halifa. Da na gama na mika masa, shi kuma ya tashi manzo sai gidan waya a Suakin.
Kafin in kare ba da labarin Halifa, ya kamata im bayyana wani aikin rashin imani wanda ban taba ganin irinsa ba, a zamana na duniya. Akwai wata kabila wai ita Bahatin wadda ba ta karbi kiran caffa da wuri zuwa Omdurman ba. Sabo da haka sai aka daura hari, aka tafi garin, aka kwaso mutum sittin da bakwai duk da matansu da ’ya’yansu. Aka kai su gaban shari’a, bayan Halifa ya rigaya ya fada wa alkalai irin hukuncin da za a yi musu. Nan da nan aka zartad da laifin tawaye a kansu. Halifa ya tambayi alkali da muhutansa ya ce, “Mane ne hukuncin tawaye ?" Suka ce, “Kisa.” Sai ya ce a koma da mutanen nan kurkuku sai gobe.
Kafin gobe an kafa maratayi uku da itatuwa masu gwafa a kasuwa. Aka daura igiya mai karfi, a ko wanne. Gobe tana yi, da hantsi sai aka shiga buga gangar yaki, ana tara mutane. Da jama’a ta taru, Halifa ya hawo dokinsa ya zo wurin, sa'an nan ya ce a kawo mutanen nan. Aka fito da su, mutum sittin da bakwai, duk an daure hannayensu a baya, haunawa suna biye. Daga baya kuma ga matansu da ’ya’yansu suna biye suna kara, suna ihu, suna faduwa. Halifa ya ce a ware iyalin a koma da su. Mu dai sai ido kurum muka zuba, mu ga abin da zai faru. Aka kasa mutanen nan uku, aka rataye kashi guda, aka sare kawunan kashi guda, daya kashin kuwa duk aka yanke musu hannayensu na dama da kafafunsu na hagu.
Ko wane maratayi ka duba, sai ka ga mutum uku ko hudu ko biyar suna lilo. Daga kasa ga haunawa sun zage dantse suna fillar kai, kamar ana fille dawa. A waje daya ga masu yanke hannu da kafa, su kuma suna dadara wuka kamar masu yankar doya. Kai, kafin lokaci kadan dai babu abin da ya rufe wurin, daga gawa sai guragun tilas. Amma ko wanne cikin mutanen nan da aka kashe, ya yi mutuwar jaruntaka. Ko kadan ba su nuna karayar zuci ba. Wadansu ma don karfin rai, kafin takobi ya sauka a wuyansu, har su kan yi wa kansu kirari. Su kan dubi ’yan kallo su ce, “Wanda bai taba ganin mutuwar jarumi ba, ya dubo nan.” Suna rufe baki sai a gutsure kan. Bayan an kare kaf, Halifa ya nufi gida, muna biye da shi. Duk cikimmu, im ba shi ba, kila ba mai sauran laka a jikinsa, sai ko haunawansa masu mummunar sana’a, ta cire kan mutane. Su kam ba su kula ba.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)