BA HAKA BANE KAWAI, AKWAI DALILI

🔮 *BA HAKANAN BANE KAWAI, AKWAI DALILI.* 🔮

🔮 *Annabi Yusuf (A. S)* ya kasance a kurkuku, tare da shi akwai wasu samari su biyu. *Annabi Yusuf (A.s)* ya fisu zuciya mai kyau, saboda shi ba wani laifi ya aikata ba wanda ya cancanci akaishi kurkukun ba, tare da cewa kuma Allah ya fi ƙaunarSHi sama da su. 

🔮 Amma cikin iko da hukuncin Allah, sai Allah yafitar da su (samarin biyu) kafin SHI. Ɗayan an fitar da shi ne domin yayiwa Sarki hidima, ɗayan kuma anfitar da shi ne domin akashe shi.

🔮 Amma shi *Annabi Yusuf* ya zauna acikin kurkukun ne har tsawon wasu shekaru, yana jiran a fito da shi, duk da cewar yana da gaskiya. Sai ga shi jinkirin ya zamar masa *Alkhairi*, yafito daga kurkukun kuma akarshe sai yazama *Babban Sarkin Masar*.

*DARASI....*

🔮 Allah zai iya jinkirta maka wasu abubuwan, ba wai saboda ba ya sonka ba, ko ya manta da kai, ko ba ya jin Addu'ar da kakeyi ba, a'ah sai dai saboda yabaka waɗanda suka fi abinda kake tambaya ko buri, ko waɗanda suka fisu kyau ko Alkhairi. Saboda haka: *ka cigaba da haƙuri kuma karika kyautatawa Allah zato*. Nan kusa ko nesa za'a biya maka bukatunka cikin yardar Allah.


Allah yasa mudace kuma yakara tsare mana Imaninmu.


✍🏻 *Idris M Rismawy*


Post a Comment (0)