CAKWALA DAƊI




*❐ CHAKWALA DADIN ❐*

*❏ KADA KI YI SAKE KIYI SAKACI DA MIJINKI ❏*

*・YAR AIKI A GIDAN MIJINKI ・*
*・ GYARAN JIKI・*

☏+2348037538596
☈ www.sirinrikemiji.blogspot.com
☛www.sirrinrikemiji@gmail.com

kada Kiyi sake Kiyi sakaci da mijinki har Wata ta kwance miki shi, saboda haka ki kula sosai, sannan kuma ki rike abin ki da kyau, saboda Galibi sakacin mu na Mata shi yake sa namiji sha'awar Kara aure, ko kuma ya fada Neman matan banza, duk ire-iren wadannan sakaci ke jawosu, don haka kar ki kuskura ki sake da wadannan abubuwa:

🍲 abinci mai dadi.

🧕🏽 tsaftar gida, jikinki da dakin kwanciyarku.

🤱🏼 tarairayar miji kamar karamin yaro.

*💃🏽🚶🏽‍♂ dauke masa nauyinsa, ( wato ki bashi hadin Kai a duk lokacin daya bukace yin kwanciyar aure dake )*

*Ki kuma dinga amfani da kayan Kara ni'ima jiki.*

☛ rake.
☛ gwanda.
☛ kankana.
☛ kunun aya.
☛ farfesun kaza/kifi.

Ki dinga shan
🍯 Zuma
🥓 Kanunfari.

*Sannan kuma ki sangarta shi, yadda duk Inda yaje, zai dinga tunaninki, ya kasa sukuni har sai ya dawo gida tukun sannan zai ji dadi.*

        *●・・ YAR AIKI ・・●*

wato yan'uwa Mata abinda yasa nace a dinga Lura, to ba wani Abu bane za'a Lura dashi ba daya wuce mai aikinki da kawayanki, musamman mai aikinki da zaku zauna gida daya da ita, tunda ita kawa sai lokaci-lokacin take zuwa.

Amma dukansu abin Lura ne sosai, saboda haka a dinga taka tsan-tsan!

Idan ba haka ba kuma, to ko dai a aure miki miji, ko kuma su dinga fasikanci, ke kuma ki na nan kin Saki baki, ki na ta kwashe sirrin ki ga kawa.

Ko mai aikinki, ba ki san abinda yake faruwa ba, don haka a Lura sosai a kuma yi da gaske da su.
Don gudun abinda zai Je ya komo, Wanda bama fata .

  *❏(・SIRRIN GYARAN JIKI ・)❏*

*❒ GYARAN JIKI AMARYA ❒*

・madara.
・kwai.
・fulawa.

ki samu madarar ki garinki Rabin cokali, kwai kwanduwa daya, fulawa Rabin cokali, sai ki hade ki kwaba da ruwa ki shafawa fuskarki da dare in Zaki kwanta sai ki wanke da safe yana sa kyau fuska.

*❐ MAGANIN KURAJEN FUSKARKI 2 ❐*

▾ kurkur.
▾ Zuma.
▾ kwai.

▾ aloevera (ki bareta ruwan ake so) Ki kwaba ki shafa da dare da safe, ki wanke ki ga yadda fuskarki zata yi kyau gami da sheki.

*・HADIN SABULUN GYARAN FATA ・*

❊ sabulu Ghana.
❊ sabulu salo.
❊ dudu osun.
❊ kurkur gari.
❊ Zuma.
❊ madarar turare
❊ lalle gari.
❊ nescafe babba cokali.
・ madara gari.

*Ki hade su wuri daya, ki dake su,ki rinka dauka kina wanka, kinga yadda jikinki zai yi laushi.*

    *■ SABULUN GYARAN JIKI ■*

・dudu osun.
・black soap.
・madara gari.
・lalle.
・kurkur.
・man zaitun.
・turaren na jiki.
・kwal.

*Ki hade su ki cuccurasu, ki rinka wanke fatar jikinki, zata sauya jikinki ya yi kyau.*

          *□ WANKE GASHI □*

・ganyen ruman.
・ganyen magarya.
・ganyen aloevera.

ki tafassa su ,in sun huce ki tace ruwan ki sa kwai daya sai Zuma cokali uku, ki wanke Kai dasu yana saurin zubo da gashin.

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
      *☛・KARIN BAYANI ・☚*

*wani Karin bayani da Zan yi a nan , shine yan'uwa Mata muyi da gaske mu kame mazajen mu Daga shiga gurbatacciyar rayuwa. kuma duk Wata mai matsala a gidan auranta da ta samu,wannan post to insha Allah zata samu hanyar warware matsala ta.*
Post a Comment (0)