CIWO YA DAMENI, ZAN IYA AMSAR BASHI DA RUWA DON NA YI MAGANI?

CIWO YA DAMENI, ZAN IYA AMSAR BASHI DA RUWA DON NA YI MAGANI?



                         *Tambaya*
Assalamu alaikum, mutum ne yake cikin halin rashin lafiya, kuma al'ummah da suke tare ba masu taimakawa ne ba,gashi wannan ciwon nason ya hallaka shi, shi kuma ba shi da kudi kuma ba shi da hanyar kudi, malam shin zai iya karbar kudin LOAN na govt don surika cirewa duk wata, ko babu halin haka nagode Allah yakara karfin imani da basirah



                            *Amsa*
Wa'alaykumussalam, Ya halatta ya amshi rancen mai ruwa, mutukar abin da yake damunsa, ya kai wancan halin da ka ambata, saboda larura tana halatta abin da aka hana, saidai ya wajaba ya amsa gwargwadon bukata.

Allah ne mafi sani

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren *_📖MIFTAHUL ILMI📖_* (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren 🔑 _*MIFTAHUL ILMI*_🔑 a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)