TAMBAYA TA 040


Tambaya
:
Dan Allah ina so a yimin karin bayani akan Istibrā'i.
:
Amsa
:
'Yar'uwa abinda ake kira da suna Istibrā'i shi ne, idan mace tayi zina kafin tayi aure kuma daga baya sai ta keso tayi aure to kafin a daura mata auren a na bukatar tayi jini daya don ta kubutar da mahaifarta cewa bata dauki ciki ba a dalilin zinar da tayi, to wannan jini dayan da za ta yi shi ne a ke kira Istibrā'i.
:
Malamai sunyi sabani akan hukuncin Istibrā'in matar da ta yi zina, a Mazhabin SHAFI'IYYA da kuma HANAFIYYA Suna ganin idan mace tayi zina to babu wata idda ko Istibrā'i a kanta sukace kawai ya halatta a daura mata aure kuma ya halatta mijin ya sadu da ita, sukace domin ruwan maniyyin da wanda yayi zina da ita ya zuba mata, ba shi da wata kima ko darajar da har za tasa ayi wani istibra'i saboda shi, domin a shari'ance a wajen mafi yawan Malamai dan zina baya gadon ubansa (na zina), kuma shi ma uban ba zai gajeshi ba,
:
Sannan sukace idan mace tayi zina wannan ba ya hana a daura mata aure da wani, kuma ya halatta ya sadu da ita, sai dai wasu malaman suna ganin cewa idan aka daura auren to ba zai sadu da ita ba har sai tayi jini daya tukuna, idan kuma ciki ya bayyana a gareta kafin yayi jima'i da ita to zai jira ne har ta haife cikin, amma idan ya riga ya sadu da ita sai a kaga ta haihu a tsakanin watanni 6 zuwa sama da haka a gidan mijin da ya aure ta to ashari'ance dan da ta haifa nasa ne, amma in dai ta haihu kafin watanni 6 to ba za a jingina masa dan da ta haifa ba,
:
Amma mazhabin MALIKIYYA sukace wajibi ne idan mace tayi zina to sai tayi Istibrā'i da jini daya, sukace idan kuma a ka daura mata aure kafin tayi istibra'i to wannan auren batacce ne dole tayi jini daya sannan a sake daura musu wani sabon aure.
:
Su kuma mazhabin HANABILA galibinsu sun tafi ne a kan cewa idan mace tayi zina to dole ne sai tayi idda cikakkiya irin na matar auren da a ka saketa wato jini 3 kenan, to amma magana mafi inganci cikin zantukan da malamai sukayi akan Istibrā'i sannan kuma mafi yawa daga cikin malamai suka rinjayar da ita, itace maganar da mazhabin MALIKIYYA suka tafi a kanta na cewa duk matar da tayi zina to dole ne tayi Istibrā'i kafin a daura mata aure, kuma jini daya kawai za ta yi, saboda yin hakan zaifi sa mutum ya samu nutsuwa kuma ya fita daga cikin sabanin Malamai,
:
Amma idan har an rigaya an daura mata aure kafin tayi istibra'i to galibin malamai sukace auren yayi ba za ace ya baci ba, anan sai ayi amfani da fatawar mazhabin SHAFI'IYYA kenan, amma inda ace ba ta yi auren ba to ana bukatar ta yi istibra'i don fita daga sabanin malamai.
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Post a Comment (0)