DALILAI GUDA GOMA SHA TAKWAS NA HARAMCIN MWULIDI 01

DALILAI GUDA GOMA SHA TAKWAS NA HARAMCIN YIN MAULIDI 

     Darasi na farko-(1)

Mai son gaskiya da bin gaskiya yana yarda da amincewa da dalili guda daya ya isar masa,amma mai san zuciya baka iya gamsar da shi da dalili.

1-Dalili na farko:
*Allah ya cikasa addininsa tun Manzon Allah SAW yana raye,babu abinda ya rage wanda wani zai kara a addini*
Allah Ta'ala yana fada acikin littafinsa:
*{ اليوم أكملت لكم دينكم وأتممت عليكم نعمتي ورضيت لكم الإسلام دين}* 
Ma'ana:
{A yau Nã kammalã muku addininku,Kuma Nã cika ni'imaTa a kanku,Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku}.
@المائدة 3].
Dukkan abinda zai zamaba addini a wannan yini to bazai zamaba addini ba a yau.
 

2-Dalili na biyu:
Manzon Allah ﷺ yace:
*(Dukkan wanda ya aikata wani aiki,wanda baya cikin addinin mu,to an mayar masa da shi)*
@مسلم
Kuma Annabi ﷺ yace
*(Dukkan wata Bidi'a batace)*
@مسلم

Wadan nan Hadisai guda biyu suna yi mana nuni akan:
-Dukkan abinda ba Manzon Allah ﷺ ya shar'anta shi ba,to wannan abu baya zama shari'ar da ake bautawa Allah da ita.
-Kuma wannan abun bidi'ane kuma baya zama kyakkyawan aiki har abada.

-Saboda yazo da lafazin "KULLU" wanda kullu sigace daga cikin sigogen umumi.

3-Dalili Na Ukku
Idan ka Tambayi masu yin Maulidi, *Shin Manzon Allah ﷺ yayi Maulidi ko baiyi Maulidi ba??* amsar gaskiya da zasu baka itace:
*Annabi ﷺ bai yi maulidi ba* to sai kace da su;
"Ta yaya kuke tsammanin samun lada ta hanyar aikata wani aikin da Manzon Allah ﷺ bai aikataba,wanda Manzon Allah ﷺ bai bar wata hanyar samun lada ba face sai da ya baiyanata ga wannan al'umma.

Idan kuma sun sanya sun zuciya sukace
*Manzon Allah ﷺ yayi Maulidi* to sai kuce da su
"To ku kawo hujjojinku akan hakan idan kuna da gaskiya,kamar yanda Allah Ta'ala ya fada:
*{ هاتوا برهانكم إن كنتم صادقين}*
@البقرة: 111]

4-Dalili na Hudu:
*Lallai masu yin maulidi da kuma nuna cewa yinsa ibadane kamar saura ibadu,to kamar suna Tuhumar Manzon Allah ﷺ akan ya boye wani abu acikin addini yaqi baiyanawa mutane,sai su suka zo daga baya suke baiyanawa mutane cewa wannan maulidi ibadace mai girma kuma hanyace ta samun kusanci zuwa ga Allah*.
Wannan shine abinda aikinsu da manufarsu take nufi koda kuwa basu fada a filiba.

الإمام مالك – رحمه الله -: 
yana cewa:
*"Dukkan wanda ya kirkiro wata bidi'a kuma yake ganinta abune mai kyau,to hakika yana mai riya cewa Manzon Allah ﷺ ya boye wani abu na sakon da Allah ya aiko shi bai baiyan ba, bayan kuma Allah yace cewa*
"(اليوم اكملت لكم دينكم واتممت عليكم نعمتي ورضيت لكم الاسلام دينا)"
Dukkan abinda bai zama ba addini a wannan rana babu hanyar da zai zama addini a yau.

5-Dalili na biyar
*Masu yin maulidi suna juya maulidi da kuma cewa shine alama mafi girma na son Allah da Manzon Allah ﷺ,to fadar haka ya zabawa zahiri domin Babbar alamar son Allah da Manzonsa, shine bi do koyi da Sunnar Manzon Allah ﷺ a fili da boye*Allah Ta'ala yana cewa:
(قل إن كنتم تحبون الله فاتبعوني يحببكم الله)
Domin soyayyar Manzon Allah ta gaskiya tana tabbatuwane ta hanyar bi da koyi da acikin sunnarsa,wani mawaqi yana cewa:
     تعصى الإله وأنت تظهر حبه هذا لعمرك في القياس بديع

             لو كان حبك صادقا لاطعته إن المحب لمن يحب مطيع

6-Dalili na Shida
Lallai maulidi baya kubuta daga fadawa Bidi'a ta hanya guda biyu:

-Sun dauke shi a matsayin addinine da ake neman kusanci Allah ta hanyarsa.

-Kuma baya da wani tushe ko asali ingantacce acikin addinin musulinci.
Kuma hakika Manzon Allahﷺ yace:
*(Dukkan bidi'a bata ce)*
@مسلم

      Allah ne mafi sani

mu hadu a Darasi na gaba insha Allah.

Post a Comment (0)