FALALAR RANAR JUMA'A

_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

       _*FALALAR RANAR JUMA'A*_
       ➖➖➖➖➖➖➖➖

_Kamar Yanda Muka Sani Ranar Juma'a Ranace da *Allah* Ya Fifitata Akan Sauran Ranaku, Wanda Hadisai da Dama Sunyi Bayani Game da Wannan Fifikon. Kadan Daga Cikin Falalar Ranar Juma'a Sun Hada da:_

_*1. Gafarar Zunubai:* Yana Daga Cikin Falalar Juma'a Shine Ana Gafarta Zunuban Bayi a Cikinta. Hadisi Ya Tabbata *Manzon Allah(ﷺ)* Yana Cewa:_

*ﻋَﻦْ ﺃَﺑِﻲ ﻫُﺮَﻳْﺮَﺓَ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺃَﻥَّ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻗَﺎﻝَ : ‏( ﺍﻟﺼَّﻼﺓُ ﺍﻟْﺨَﻤْﺲُ، ﻭَﺍﻟْﺠُﻤْﻌَﺔُ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟْﺠُﻤْﻌَﺔِ ، ﻛَﻔَّﺎﺭَﺓٌ ﻟِﻤَﺎ ﺑَﻴْﻨَﻬُﻦَّ ﻣَﺎ ﻟَﻢْ ﺗُﻐْﺶَ ﺍﻟْﻜَﺒَﺎﺋِﺮُ} (مسلم:٢٣٣)*

_An Kar6o Daga *Abi-Hurairah (ra)* Yace: *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: *{Sallolin Farillai Biyar, da Juma'a Zuwa Juma'a, Suna Kankare Abinda Ke tsakaninsu, Idan Aka Nisanci Manyan Zubai}* (Muslim:233)._

_*2. A Cikinta Ne Mafi Falalar Sallah Take:* Hadisi Ya Tabbata Daga *Ibn-Umar* Yana Cewa:_

*ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ‏( ﺃﻓﻀﻞ ﺍﻟﺼﻠﻮﺍﺕ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﺼﺒﺢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻓﻲ ﺟﻤﺎﻋﺔ ‏) . ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﻴﻬﻘﻲ ﻓﻲ " ﺷﻌﺐ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ " . ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ‏( ١١١٩ ‏) .*

_An Kar6o Daga *Ibn Umar (ra)* Yace: *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: *{Mafi Falalar Sallah a Wurin Allah Itace Sallar Asubah ta Ranar Juma'a a cikin Jam'i}* (Baihaqee). *Albany* Ya Ingantashi a Cikin Sahihil Jami'i (1119)._

_Yana Daga Cikin Banbancin Sallar Asubahin Ranar Juma'a da Sauran Ranakun Shine Anso a Karanta *Suratul Sajadah* a Raka'ar Farko; a Raka'a ta Biyu kuma a Karanta *Suratu Insan*._

_*3. Duk Wanda Ya Mutu Ranar Juma'a Za'a Kareshi Daga Fitinar Kabari:* An Kar6o Hadisi Daga *Abdullahi bn Amru (ra)* Manzon Allah Yana Cewa:_

*ﻋﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ ﻗَﺎﻝَ : ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ : ‏( ﻣَﺎ ﻣِﻦْ ﻣُﺴْﻠِﻢٍ ﻳَﻤُﻮﺕُ ﻳَﻮْﻡَ ﺍﻟْﺠُﻤُﻌَﺔِ ﺃَﻭْ ﻟَﻴْﻠَﺔَ ﺍﻟْﺠُﻤُﻌَﺔِ ﺇِﻻ ﻭَﻗَﺎﻩُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻓِﺘْﻨَﺔَ ﺍﻟْﻘَﺒْﺮِ ‏) . ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ‏(١٠٧٤ ‏) . ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ " ﺃﺣﻜﺎﻡ ﺍﻟﺠﻨﺎﺋﺰ " ‏( ﺹ٤٩-٥٠ ‏) .*

_An Kar6o Daga *Abdullahi bn Amru :ra)* Yace *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: *{Babu Wani Musulmi da Zai Mutu Ranar Juma'a ko Daren Juma'a, Face Allah Ya Kareshi Fitinar Kabari}* (Tirmizi: 1074). *Albany* Ya Ingantashi a Cikin Ahkamul Janã'iz._

_*4. An Sunnata Yin Wanka a Cikinta:* Hadisi Ingantacce Ya Tabbata Game da Umurni Dayin Wanka Ranar Juma'a._

*ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺳﻌﻴﺪ ﺍﻟﺨﺪﺭﻱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝُ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : )) ﺍﻟﻐُﺴْﻞُ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻭﺍﺟﺐٌ ﻋﻠﻰ ﻛﻞِّ ﻣﺤﺘﻠﻢ، ﻭﺃﻥ ﻳﺴﺘﻦَّ، ﻭﺃﻥ ﻳﻤﺲَّ ﻃﻴﺒًﺎ، ﺇﻥ ﻭﺟﺪ (( ؛ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ .*


_An Kar6o Daga *Abi-Sa'eedil Khudry (ra)* Yace: *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: *{Wankan Juma'a Wajibi ne Akan Dukkan Balagi, Kuma Ya Sanya Tufafi Masu Kyau, Ya Shafa Turare Idan Ya Samu}* (Sahihul Jami'i)._

_*5. Sammako Zuwa Masallaci:* Hadisi Ya Tabbata *Manzon Allah* Yace:_

*ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓَ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝَ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ : )) ﻣَﻦ ﺍﻏﺘﺴﻞ ﻳﻮﻡَ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻏُﺴْﻞ ﺍﻟﺠَﻨﺎﺑﺔ، ﺛﻢ ﺭﺍﺡ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﺎﻋﺔ ﺍﻷﻭﻟﻰ، ﻓﻜﺄﻧﻤﺎ ﻗﺮَّﺏ ﺑَﺪَﻧﺔ، ﻭﻣَﻦ ﺭﺍﺡ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﺎﻋﺔ ﺍﻟﺜﺎﻧﻴﺔ، ﻓﻜﺄﻧﻤﺎ ﻗﺮَّﺏ ﺑﻘﺮﺓ، ﻭﻣﻦ ﺭﺍﺡَ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﺎﻋﺔ ﺍﻟﺜﺎﻟﺜﺔ ﻓﻜﺄﻧﻤﺎ ﻗﺮَّﺏ ﻛﺒﺸًﺎ ﺃﻗﺮﻥَ، ﻭﻣﻦ ﺭﺍﺡ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﺎﻋﺔ ﺍﻟﺮﺍﺑﻌﺔ ﻓﻜﺄﻧﻤﺎ ﻗﺮَّﺏ ﺩﺟﺎﺟﺔً، ﻭﻣَﻦ ﺭﺍﺡ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﺎﻋﺔ ﺍﻟﺨﺎﻣﺴﺔِ ﻓﻜﺄﻧَّﻤﺎ ﻗﺮَّﺏ ﺑﻴﻀﺔ، ﻓﺈﺫﺍ ﺧﺮﺝ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺣﻀﺮﺕ ﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ؛ ﻳﺴﺘﻤﻌﻮﻥ ﺍﻟﺬﻛﺮَ (( ؛ ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺎﻟﻚ، ﻭﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، ﻭﻣﺴﻠﻢ، ﻭﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ، ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱُّ، ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲُّ، ﻭﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ .*

_An Kar6o Daga *Abi-Hurairah (ra)* Yace: *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: *{Duk Wanda Yayi Wanka Ranar Juma'a Irin Wankan Janaba, Sannan Yayi Sammako a Sa'a ta Farko, Kamar Ya Gabatar da Rakumi Ne. Wanda Yayi Sammako a Sa'a ta Biyu Kamar Ya Bayar da Saniya Ne. Wanda Yayi Sammako a Sa'a ta Uku Kamar Ya Sadaukar da Rago Mai Kaho Ne. Wanda Yayi Sammako a Sa'a ta Hudu Kuma Kamar Ya Bayar da Kaza Ne. Wanda Yayi Sammako Kuma a Sa'a ta Biyar Tamkar Ya Sadaukar da Kwai Ne. Idan Liman Yazo, sai Mala'iku Su Halarto Suna Sauraren Zikiri}*. (Malik, Bukhari, Muslim, Abu-Daud, Tirmizi, Nisa'i da Ibn-Majah)._

_*6. Tana Daga Cikin Yinin da Aikin Alkhairi a Cikinta Ke Sabbaba Shiga Aljannah:*

*ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺳﻌﻴﺪٍ ﺍﻟﺨﺪﺭﻱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : )) ﺧﻤﺲٌ ﻣَﻦ ﻋﻤﻠﻬﻦَّ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﻛﺘﺒَﻪ ﺍﻟﻠﻪُ ﻣﻦ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺠﻨﺔ : ﻣَﻦ ﻋﺎﺩ ﻣﺮﻳﻀًﺎ، ﻭﺷَﻬِﺪ ﺟِﻨﺎﺯﺓً، ﻭﺻﺎﻡ ﻳﻮﻣًﺎ، ﻭﺭﺍﺡ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ، ﻭﺃﻋﺘﻖ ﺭﻗﺒﺔً (( ؛ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ .*

-8 ﻳُﺴﻦُّ ﻛﺜﺮﺓُ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲِّ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻴﻪ، ﻭﻣَﻦ ﺻﻠَّﻰ ﻋﻠﻴﻪ ﺻﻼﺓ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻋﺸﺮًﺍ :
ﻋﻦ ﺃﻧﺲ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝَ ﺍﻟﻠﻪِ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ : )) ﺃَﻛﺜِﺮﻭﺍ ﺍﻟﺼﻼﺓَ ﻋﻠﻲَّ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔِ ﻭﻟﻴﻠﺔ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ، ﻓﻤَﻦ ﺻﻠَّﻰ ﻋﻠﻲَّ ﺻﻼﺓً ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻋﺸﺮًﺍ (( ؛ ﺳﻠﺴﻠﺔ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ .
_An Kar6o Daga *Anas (ra)* Yace *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: *"Ku Yawaita Salati a Gareni a Yinin Juma'a da Daren Juma'a. Duk Wanda Yayimin Salati Guda Allah Zaiyi Masa Guda Goma"*. (Silsilatul Ahadisis Sahiha)._

_*✍Ahmad Dabai*_


Post a Comment (0)