HALLACCIN SANYA ZOBE A HANNUN DAMA KO HAGU

_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

```HALACCIN SANYA ZOBE A HANNUN DAMA KO A HANNUN HAGU```
➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖

_Ya halatta Musulmi ya sanya zobe ko dai a yatsar hannunsa na dama ko kuwa a yatsar hannunsa na hagu, saboda wadannan dalilai:-_

_1. Imamu Muslim ya ruwaito hadithi na 2094 daga *Sahabi Anas Dan Malik* cewa:-_

*(( ﺍﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻟﺒﺲ ﺧﺎﺗﻢ ﻓﻀﺔ ﻓﻲ ﻳﻤﻴﻨﻪ ﻓﻴﻪ ﻓﺺ ﺣﺒﺸﻲ ﻛﺎﻥ ﻳﺠﻌﻞ ﻓﺼﻪ ﻣﻤﺎ ﻳﻠﻲ ﻛﻔﻪ )).*

_Ma’ana: *((Lalle Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya sanya zoben azurfa a damarsa cikinsa akwai mahadar zobe na irin na habasha, ya kasance ya kan sanya mahadar zoben ta bangaren tafin hannunsa)).*_

_2. Imamu Muslim har yanzu ya ruwaito hadithi na 2095 daga Sahabi *Anas Dan Malik* cewa ya ce:-_

*(( ﻛﺎﻥ ﺧﺎﺗﻢ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻲ ﻫﺬﻩ، ﻭﺃﺷﺎﺭ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺨﻨﺼﺮ ﻣﻦ ﻳﺪﻩ ﺍﻟﻴﺴﺮﻯ )).* 

_Ma’ana: *((Zoben Annabi mai tsira da amincin Allah ya kasance ne cikin wannan, sai ya yi ishara zuwa ga karamar yatsa daga hannunsa na hagu)).*_

_3. Imamu Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 4229 daga *Ibnu Ishaqa* ya ce:-_

*(( ﺭﺃﻳﺖ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺼﻠﺖ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺧﺎﺗﻤﺎ ﻓﻲ ﺧﻨﺼﺮﻩ ﺍﻟﻴﻤﻨﻰ ﻓﻘﻠﺖ : ﻣﺎ ﻫﺬﺍ؟ ﻗﺎﻝ : ﺭﺃﻳﺖ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﻳﻠﺒﺲ ﺧﺎﺗﻤﻪ ﻫﻜﺬﺍ ﻭﺟﻌﻞ ﻓﺼﻪ ﻋﻠﻰ ﻇﻬﺮﻫﺎ، ﻗﺎﻝ : ﻭﻻ ﻳﺨﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﺍﻻ ﻛﺎﻥ ﻳﺬﻛﺮ ﺍﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ. ﻳﻠﺒﺲ ﺧﺎﺗﻤﻪ ﻛﺬﻟﻚ )).*

_Ma’ana: *((Na ga wani zobe tare Salt Dan Abdullah cikin karamar yatsarsa ta hannun dama, sai na ce: Mene ne wannan? Sai ya ce: Na ga Dan Abbas ya kan sanya zobensa kamar haka ya sanya mahadar zoben nasa ta bayan tafinsa. Ya ce: Ba a tsammanin Ibnu Abbas face ya kasance yana ambaton cewa lalle Manzon Allah mai tsira da amincin Allah haka ya kasance yake sanya zobensa)).*_
_Wannan Hadithi *Albani* ya inganta shi._

_4. Ya zo cikin littafin Aljaami’us Sagir Wa Ziyaadatihi, Hadithi na 4899 kamar haka:-_
*(( ﻛﺎﻥ ﻳﺘﺨﺘﻢ ﻓﻲ ﻳﺴﺎﺭﻩ )).*

_Ma’ana: *((“Annabi” Ya kasance yana sanya zobe a hagunsa)).* Albani ya inganta shi._

_5. Har yanzu ya zo cikin Littafin Aljaami’us Sagir Wa Ziyaadatihi, Hadithi na 4900 kamar haka:-_

*(( ﻛﺎﻥ ﻳﺘﺨﺘﻢ ﻓﻲ ﻳﻤﻴﻨﻪ )).*

_Ma’ana: *((“Annabi” Ya kasance yana sanya zobe ta damarsa)).* Albani ya inganta shi._

```TA INA AKE SANYA “Fassin zobe”? WATAU MAHADAR ZOBEN WANDA YAWANCI AKE MASA ADO NA 
MUSAMMAN?```

_*Amsa:* Kana iya sanya shi ta bangaren cikin tafin hannu, haka nan kana iya sanya shi ta bangaren bayan tafin hannu; saboda Hadithan da muka ambata a sama._

```A WACE YATSA CE YA KAMATA NAMIJI KO MACE SU SANYA ZOBEN NASU?```

_*Amsa:* Imamun Nawawi ya ce cikin littafinsa “Sharhun Nawawi Alaa Sahihi Muslim”7/188 kamar haka:-_

*(( ﺍﺟﻤﻊ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻥ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺟﻌﻞ ﺧﺎﺗﻢ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻓﻲ ﺍﻟﺨﻨﺼﺮ، ﻭﺃﻣﺎ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﻓﺈﻧﻬﺎ ﺗﺘﺨﺬ ﺧﻮﺍﺗﻴﻢ ﻓﻲ ﺃﺻﺎﺑﻊ )).*

_Ma’ana: *((Musulmi sun yi Ijmaa’i a kan cewa Sunnah ita ce namiji ya sanya zobe a karamar yatsa, amma ita mace tana iya sanya zobba. cikin yatsu dayawa)).*_

```SHIN ZOBEN AZURFA NE KAWAI. YAKE HALATTA?```

_Amsa: *((Zoben zinare da azurfa da ma ko mene ne yana halatta ga Mata. Sannan zance mafi inganci shi ne: Ko wane zobe yana halatta ga Maza ma amma banda zoben zinare)).*_

_Yana daga cikin hujjar wannan magana tamu abin da *Imamun Nawawi* ya ce cikin littafinsa “Sharhun Nawawi Alaa Sahihi Musulim”7/177 :-_

*(( ﺍﺟﻤﻊ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺇﺑﺎﺣﺔ ﺧﺎﺗﻢ ﺍﻟﺬﻫﺐ ﻟﻠﻨﺴﺎﺀ، ﻭﺃﺟﻤﻌﻮﺍ ﻋﻠﻰ ﺗﺤﺮﻳﻤﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ )).* 

_Ma’ana: *((Musulmi sun Ijmaa’i a kan halaccin zoben zinare ga Mata, sannan sun yi Ijmaa’i a kan haramcinsa a kan Maza)).*_

```Akwai wasu hujjojin daban banda wannan.```

_*✍🏼Dr. Ibrahim Jalo Jalingo*_
Post a Comment (0)