HIKAYAR GIMBIYAR HINDU SAHBITRIYA
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Wannan hikaya ta fito ne daga kundin hikayoyin hindu mai suna 'Mahabharata' wanda akace an tattarashi a zamanin Rayuwar Annabi Isa A.S
Hikayar ta soma da cewa:-
A hindu, an taba yin wani sarki mai suna Nadarana. Wannan sarki yana da tarin dukiya gami da mataye, amma kuma bai taba samun haihuwa ba.
Saboda haka ya dukufa kai kukansa wajen abin bautarsa. A kullum cikin addua yake safe, rana da dare.
Watarana yana bacci da dare, sai yayi wani mafarki. A cikin mafarkin ne yaga wani farin mutum ya sauko gareshi daga sama, yana masa albishir da cewa zai sami haihuwar diya mace wadda ba irin ta a kyau, amma kuma idan aka tilasta mata auren wani zata mutu, idan kuma ta auri wani ba sarki ba zai mutu bayan shekara daya.
Sarki yayi firgigit ya tashi yana juyayi. Ya fara tunanin abubuwan da aka sanar dashi acikin mafarkin. Zuwa can ya yanke shawarar zuba ido kurum don ganin abinda zai faru. Tun daga nan bai sanar da kowa wannan mafarki ba.
A kwana atashi, sai kuwa wata matarsa da yake matukar so ta dauki ciki. Murna wurin sarki Nadarana ba zata misaltu ba. Da lokacin haifuwa tayi, aka haifi mace kyakkyawar gaske. Sarki yasa mata suna Sahbitriya.
Tun tasowar wannan yarinya aka fuskanci baiwar da take da ita. Domin ta kasance hazika, gata kuma kyakkyawar gaske wadda duk wanda ya kalla sai yaso ya kara dora idanunsa akan fuskarta. Gata gwanarvfara'a da girmama mutane. Tun tana karama sarakuna ke tasowa izuwa ga sarki Nadarana da zimmar neman aurenta idan ta girma, a haka har Gimbiya Sahbitriya ta zama budurwa.
Da Sarki yaga diyarsa ta isa aure, sai yasa a tambayeta ko tana da wanda take so ta aura. Sahbitriya tace babu. Daga nan sai sarki yace to ya bata damar ta nemo da kanta duk wanda take ganin zata iya rayuwa dashi amatsayin miji matsawar kammalallen mutum ne.
Abinda akayi kenan. Manyan mutane da sarakuna sun rinka aikowa da Gimbiya Sahbitriya kyaututtuka na kasaita da niyyar jan ra'ayinta wajen amicewa ta zabesu a matsayin miji, amma sam bata kula suba.
Wata rana ta tafi wurin bauta dake can bayan gari, tare da ita akwai fadawa da kuyanginta. Suna tafe ana mata fadanci. Duk inda ta gitta kuwa mutane zaka gani sun tsaya suna kallon ta.
Zuwa can sai ga wani saurayi yazo wucewa yana rike da wani dattijo. Saurayin bai kula da abinda mutane ke kallo ba, shidai hanya yake budawa ta cikin mutane don ya samu damar isar da dattijon nan ga wurin bauta.
Wannan abu sai yasa Gimbiya mamaki, nan take kuma ta kamu da son sa.
Abinda yasa ta mamakin shine yadda kyanta bai hana shi kula da dattijo ba, ya kuma mai da hankali wajen yin abinda ya kawo shi sabanin ragowar mutane wadanda wasu suka shashance dayin bautar daya kawosu, ita kawai suke kalla.
Komawar ta gda keda wuya ta sanar davsarki cewa ta samu wanda take so.
Sarki yayi murna da jin haka, tsammanin sa wani sarki zata ce tana so wanda babu jimawa ya turo mata da kyautar tarin dukita da bayi. Sai tace wani saurayi ne dan gidan dattijo mutumin kauye wanda ta hadu dashi a wurin bauta. Sarki yace sam baza'ayi haka ba ta canza wani.
Ita kuma tace indai auren so akeso tayi bata da zabi sai wannan. Da sarki ya tuna da mafarkin sa sai yace shikenan, amma fa tayi shirin takaba nan da shekara daya domin mijin mutuwa zaiyi bayan aure. Takabar su kuwa tana da matsanancin tsanani, saboda al'ada ta tsara cewa babu wanda zai auri macen da mijin ta ya mutu, kuma kullum cikin bakaken tufafi zata rayu, gashi ba zatayi kwalliya ba har mutuwa.
Gimbiya tace babu komai. Zata jure. Shikenan. Sarki yasa aka nemo iyayen saurayi akayi maganar aure. Sunan saurayin nan kuwa Satyabana.
Da lokacin aure yayi akayi biki gagarumi. Bayan an kare sai Satyabana yace zai tafi da matarsa kauyen su inda suke rayuwa, domin shine ke kula da mahaifinsa. Sarki yace zai basu kyautar gida gagarumi acikin gari su dawo su zauna, ko kuma zai sa a gina musu katafaren gida acan, amma dattijon nan yace shi baya so. Ashe tsohon attajiri ne wanda tawayar arziki ta sama. Ya samu daular duniya iri-iri a baya. Yanzu kuwa komai ya kare kuma babu abinda ke burgeshi sai rayuwa cikin talauci. Itama gimbiya Sahbitriya tace taji tagani, zata rayu a kauye da mijin ta abin kaunar ta.
Sarki ba yadda ya iya. Aka tafi da diyarsa kauye cikin wani tsohon gida. Anan gimbiyar ta cigaba da rayuwa.
A kwana atashi, sai maganar Sarki na mutuwar Sahyabaana ya rika tasiri a zucitar mijinta. Gashi dai kullum kara son junansu sukeyi, amma kuma kullum zullumin ta shine rasa masoyinta.
Wannan yasa ta dukufa addua ba dare ba rana. A kullum addua takeyi ga abin bauta don ya kiyaye faruwar mutuwar mijinta. Shikuwa Sahyabana har mamaki yake idan yaga yadda take shagalta wajen bauta. Ita kuma taki sanar dashi abinda ke faruwa.
Shekara daya da aurensu, wata ranabsahyabana ya dauki gatari ya sulale jikinsa izuwa daji sarar icce. Hakan ya faru sa'ar da gimbita ke bacci. Saboda tunda taga shekarar aurensu ta cika ta daina sakaci, kullum suna tare da sahyabana. Duk inda zashi sai ta bishi.
A cikin baccin ta sai aka nuna mata cewa ga wasu yammata can sun tafi da mijinta izuwa duniyar sama, zai sami kulawa kuma da martabawa acan sosai fiye da wadda yake samu anan duniyar kasa. Sai kuwa gimbiya take tayin magiya akan kada a rabata da abin son ta. Daga bisani sai akayi mata albishir da cewa albarkacin adduar da ta jima tanayi, taje yanzu da marmaza ta yayyafa ruwa a fuskar mijinta zai dawo rayayye, arziki kumabzai zo garesu babu jimawa. A iya nan ne ta farka daga baccin firgigit..
Ta fita tana kiran sunan mijin ta ba tare da taji duriyar saba. Sai wasu maaikatan gidan ke cewa sun ganshi yayi can wajen da gatari a hannunsa. Dajin haka kuwa sai ta bazama da gudu tayi wurin da aka nuna mata tana mai kwalla masa kira da dube-duben inda yake. Nutsawar ta cikin dajin keda wuya ta hango shi a kwance matacce. Ashe a halin saro iccen da yakeyi daga sama ya zame ya fado kasa matacce. Da ganin haka sai ta tuno da abinda akace mata tayi mafarki. Ta ruga gida da gudu ta kwaso ruwa. Da zuwa tazuba masa sannan ta tsaya tsam tana mai kura masa ido.
Jim kadan taji yayi ajiyar zuciya, sannan ya bude idon sa. Da kallon ta yace gimbiya yaushe kikazo nan? Kai baccin nan da nayi yana da dadi. Gimbiya sahbitriya tayi murmushi tana mai rungume shi cikin fatin ciki, sannan tace tashi mutafi gida.
Ba'a shekara ba sai da arziki ya dawwama a gare su, Sahyabana ya zamo babban attajiri wanda sunan sa ya rinka karadawa a kasashe. Sarki kuwa yayi matukar murna tare da yawan godiya ga abin bauta bisa yadda yarsa ke rayuwa cikin farin ciki da arziki.
Wannan labarin na nuna tasirin addua ne wajen samun duk abinda akeso.