HUKUNCIN WACCE TA CIRE CIKI YANA ƊAN WATA HUƊU

TAMBAYA
=========
👇
Assalamu alaikum, Allah ya saka wa malam da gidan aljanna,tambayata wacce ta cire ciki bayan ya kai wata hudu kuma dan na sunna ne,daga baya tana son neman gafarar Allah,shin azumi sittin zata yi ko kuma istigfari zatana yi, a taimaka mana da amsa malam.


AMSA
======
👇
Lalle ta aikata babban zunubi, abinda yake kanta shine, ta nemi yafiyar Ubangiji akan Allah ya yafe mata, musamman ma a irin wata Na Ramadana mai tarin Albarka, wanda yake dauke da budaddun kofofin Rahama da gafara da yafiya daga mahaliccinmu Subhanahu wata'ala.
 Allah ya gafarta mana gabaki daya.

Allah shine masani 


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876


Post a Comment (0)