TAURIN BASHI

TAURIN BASHI !!!
 
Dukkanin mutumin da ya taimaka maka da bashin kudi ko masrufi alokacin da kake cikin buqata,lallai mutumin mai tausayin ka ne kuma mai qaunar ka ne.
Hakan ya kamata kaima ka kasance mai mutuntawa da girmamawa a gareshi ta hanyar biyan sa bashin nan akan lokaci

Al'amarin bashi abu ne mai girma da ya kamata mu kula dashi saboda girman sa Allah ta'ala ya saukar da Aya mafi tsayi a cikin alqur'ani mai girma cikin suratul baqarah aya ta 282 gudun kada na tsawaita rubutun yasa ban kawo ta ba. 
Hadisai da dama sun gabata akan batun bashi , 
Kadan daga cikin hadisain akwai
وجأفي صحح
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال عن النبي صلى الله عليه وسلم قال"من أخذا أموال الناس يريد أداءها أدّى الله عنه ،ومن أخذ يريد إتلافها أتلفه الله تعالى"
Ma'ana"daga Abiy Hurairah r.a. yace dag Annabi s.a.w yace(Wanda ya karbi dukiyar mutane da nufin ya mayar da ita Allah zai bashi Wanda ko ya karba da nufin hana su Allah zai hana shi)
وروا مسلم
عن أبي رافع رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم إستسلف من رجل بكر فقدما عليه إبل من إبل صدقة فأمر أبارافع يقضي الجل بكره فقال لاأجد إلا خيار رباعيا، فقال "أعطه أياه،فإن خيار الناس أحسنهم قضاء"
Daga Abiy raafi'in r.a. "haqiqa Annabi s.a.w. ya ranci dan raqumi daga wani mutum sai aka kawo masa raquma daga raquma n zakkah sai ya umarci Aba raafi'in daya biya mutumin dan raqumin sa , sai yace ban samu ba sai zababben raqumin daya shiga shekara ta bakwai sai yace( bashi shi din domin haqiqa zababbun mutane sune masu kyautatawa wurin biyan bashi).
A wani athar din kuma yace 
إنما جزاء السلف الحمد والقضاء
Kadai sakamakon bashi godiya da biya ne
Wani qaulin kuma yace
مطل الغني ظلما 
Tsawaitawar (jinkirin biyan bashi ) na mawadaci zalinci ne

To Yan uwa duk da irin wadannan nassin amma kariqe dukiyar al'umma ka qi basu da dama daga cikin masu bin ka bashi suna cikin tsananin buqatar haqqin su, kaara,da girmamawa yasa basu tambaye ka ba, daure ka sauke nauyin nan daga kan ka, 
Kada kace sai ka gama biyan buqatun dake gaban ka tukunna, har mutuwa baza ka rabu da al'i'iraadh ba

Ka biya bashin dake kanka!!! Da zarar dama ta samu,
Kada kace tukunna!
Tukunna sai yaushe kenan? 
Sai za ka mutu kayi wasiyya a biya maka?
Kana da tabbacin za a biya makan? 
Kasan irin mutuwar da zakayi 
Baka Tunanin mutuwar FUJU'A?

Yi qoqari ka Kare kanka daga zama MAFLUS ranar alqiyaamah 

Saboda girman bashi fa Annabin Rahma s.a.w duk soyayyar sa da sahabban sa amma baya yiwa Wanda ake bi bashi sallah sai idan an samu Wanda ya dauki nauyin biyan bashi.

Hauwa Tijjani Musa
19-8-2017

Post a Comment (0)