IDAN DAI BAKA TABA SHAN IRIN WANNAN MARI BA A WAJEN MAMANKA BA'A KASAR HAUSA KA TASHI BA

IDAN DAI BAKA TABA SHAN IRIN WANNAN MARI BA A WAJEN MAMANKA BA'A KASAR HAUSA KA TASHI BA


 😀

Alherin Allah Ya kai ga iyaye mata Hausawa, wato a kalolin mari da suke bamu muna yara a salonsu na tarbiya. Ciki akwai *TAU*, *TAS*, *RAAM*, *FAYAU*, *FAU* DA KUMA *TARAU*. 

Wadannan marukan za su sa ka fara tinanin ko dai ba ita ta haifeka ba ne😀😜

Shi dai *TARAU* zai sa ka gyara kura-kuranka nan take. 😀

Dadin *TAU* kuwa a take za ka yarda cewar ka yi laifi. 😜

*RAAM* kuwa zai sa ka fallasa duk wadanda kukayi laifin tare😂

Amma ka ga *FAU*, a take zai sa ka yi fitsari a wando. 🤣

Ance *TAS* yafi muni, domin zaisa ka rasa halinda kake ciki, ka fara tinanin ko dai mafarki kake yi ne😂

Shi kuwa *FAYAU*, lokacin da ka karbe shi za ka kasa tsayawa guri daya, kayinka zai fara yin gabar da yamma kudu da arewa kana neman me ya mareka😆

Ka ga idan ta baka daya daga cikin marukan nan, da zaran tace "mu tafi gida"! Za kace "mama gashi nan a aljihuna" 🤠

Allah Ya sakawa iyayenmu da alheri. 

Don haka duk wanda yaga sakonnan dole ya fadi wane irin mari ya taba karba.............. Ina jira👂🏻👂🏻👂🏻
Post a Comment (0)