ƘWAI MAI NI'IMA

*KI KULA DA KANKI GROUP*👰

*KWAI MAI SA NI'IMA*
 
*KAYAN DA KIKE BUKATA*

Kwai
Tumatir 
Maggi
Kanumfari
Man zaitun 
Gadali ko farar albasa

*YADDA AKE YI*

Yar uwa ki samu roba ki fasa kwai a ciki (iya yawan da zaki iya cinyewa,kamar biyu haka)sai ki wanke gadali ko farar albasa ko kuma dika biyun ki yanyanka a kan kwan ki barbaďa maggi ki kawo garin kanumfari ki sa sai ki yanyanka tumatir a ciki sai ki kaďa da kyau, ki ďora farantin suya a kan wuta ki zuba man zaitun (Dan bada man gyada zaki soya ba)idan ya ďau zafi sai ki zuba kwan a ciki ki soya amma kar ki bari ya 'kame ki barshi da ruwa ruwa, sama sama zaki soya shi, ki sauke ki cinye abinki, ni'ima kam ba'a magana 🙈🙈🙊🙊.

*KI KULA DA KANKI GROUP*👰

Maman Usman 
_08032629076_

Ban hana a tura wa yar uwa ko kuma group ba saboda samun lada amma kar a canza min post dan ban yafe ba.


Post a Comment (0)