*AZUMI GARKUWA NE*
A jiya idan ‘yan Uwa suna biye damu, mun tsaya a bayani ne kan yadda Azumi ya zama Garkuwa daga sha’awa, da kuma Wuta, to wannan sakamakon mai ɗimbin yawa da Bawa zai samu, da falala mai girma, ana iya ganin bayanan su filla-filla a cikin Hadisai Ingantattu masu zuwa:
Manzon Allah ﷺ ya umarci wanda sha’awar sa ta saduwa da Mace ta tsananta, amma bai samu ikon Aure ba, da yayi Azumi, kuma ya sanya shi a matsayin Garkuwa daga wannan sha’awar, domin yana kwantar da kowace buƙata ga barin afkawa son zuciya ta hanyar sanya mata linzamin sa da takunkumin sa. Babu shakka, abu ne tabbatacce cewa Azumi yana da baiwa mai ban mamaki wajen kiyaye gabobi waɗanda suke a fili, da tasiri na boye. Saboda haka ne ma Manzon Allah ﷺ yace:
_
“Ya ku taron Matasa wanda duk ya samu ikon yin Aure daga cikin ku, to yayi domin yin sa shine mafi rintse gani, kuma shine mafi karewa ga Farji, wanda kuwa bai samu iko ba, to yayi Azumi, domin yin sa GARKUWA NE gareshi”._
A wani gurin kuma Manzon Allah ﷺ ya bayyana cewa: Aljannah a kewaye take da abubuwan da rai bata so, Wuta kuma an kewaye ta ne da abubuwan sha’awa.
To idan ka fahimci cewa Azumi yana takure sha’awa yana tursasa ta, alhali kuwa itace take shashantar da Mutum kuma take kusantar dashi ga Wuta, kaga kenan Azumi ya zama katangar Ƙarfe tsakanin Mutum da Wuta. Saboda haka ne ma, Hadisan suka zo suna masu bayyana cewa Azumi tsari ne kuma garkuwa ne da Bawa yake kare kansa dashi daga Wuta.
*AZUMI YANA SHIGAR DA MUTUM ALJANNAH:*
Yanzu dai ya kai mai biyayya ga Allah, Allah yayi maka gam-da-katar wajen biyayya gare Shi, ya ƙarafafe ka da ikon Sa, ka san cewa Azumi yana nesanta ma’abocin sa daga Wuta, wannan ya nuna kenan cewa yana kusantar da ma’abocin sa ga Aljannah.
An karbo daga Baban Umama (Saddy dan Ajlaan) (Allah ya kara masa yarda) yace: nazo wajen Manzon Allah ﷺ, sai nace: ka Umarce ni da wani abu da zan riƙa daga gareka, sai Manzon Allah ﷺ yace: “Ina maka Wasiyyar kayi riƙo da yawaita yin Azumi, babu kamar sa a cikin aiyuka”
[Imamun-Nisa'i ne ya ruwaito shi].
#Article02
#RamadanMubarak
#Asha_Ruwa_Lahiya
Domin Samun jerangiyar wa'innan articles din sai ka bi wannan link din
https://t.me/annasihatvchannel/3734