JAN HANKALI

✨ *Jan hankali game da neman dukiya, mulki da mukami kota halin yaya.*


*Wa yace maka dan ka samu kudi hankalin zai kwanta, wa yace maka samun mulki da mukami ke sanya kyak-kyawan rayuwa a cikin zuciyan dan Adam, Ubangiji Ta'ala ne ke nufar da mutane, ya basu hakuri, ya basu dangana, koda bai basu dukiya mai yawa ba sai suji suna da wadatan zuci, sai suji suna da hutun zuciya, sai suji hankalin su akwance ba tare da sun ajiye miliyoyin kudi ba. Amma nawa-nawa ne suka tara miliyoyin kudi basa iya yin bacci sai an musu allura ko sun hadiyi kwaya, baza su kidayu ba, nawa-nawa ne suka samu muggan kudi tsakanin su da 'ya'yan su ana 'yar wasan buya, tsakanin su da matan su ana 'yar wasan buya, dan 'ya'yan suna ganin ka ci naka ya kamata ka mutu su kuma su ga-da, kai kuma kana ganin akwai saura.............*


          *Sheikh Ja'afar Mahmud Adam, rahimahullah.*


Post a Comment (0)