KOYARWAR SALAF SHINE ADDUA'A GA SHUGABANNI DA RASHIN SHELANTA KUSAKURENSU

KOYARWAR SALAF SHINE ADDUA'A GA SHUGABANNI DA RASHIN SHELANTA KUSAKURENSU 
-


Daga dan uwa
 Sa'ad Albaniy
.
wasu suna kafa hujjada Maganar Ahmad bin hanbal ta 
الدعاء قصاص. 
Wajen yin mummunar addu'a ga shugabanni. 
 لفظ عام Sedai maganar Imam Ahmad 
ne. Lafazine me gamewa 
ومعاملة الحكام أمر خاص ، وهم ليسوا كغيرهم. 
Mu'amala da shugabanni kuma abune ke6antacce, su ba kamar kowa suke ba. Anai musu mu'amalace ta musamman. 
وقد قال العلماء أنه لا يجوز الإستدلال بالعمومات في جزئية لم يجر عليها العمل 
 Se muduba muga yaya salaf sukayi mu'amala da zalumcin shugabanni.
Da farko sahabbai sun tanbayi manxon Allah akan shugabanni azzalumai annabi Se yace 
عليكم ما حملتم وعليهم ما حملوا. أو كما قال. 
Abinda aka daura muku yana kanku, suma abinda aka daura musu yana kansu.
لم يأمرهم بالدعاء عليهم وسبهم أو الخروج عليهم بالسيف أم باللسان 

Imam hasanul basary yaji wani mutum yana addua akan hajjaj.. Se yace 

لا تفعل رحمك الله ،إنكم من أنفسكم أتيتم ،إنما نخاف إن عزل الحجاج أو مات: أن تليكم القردة والخنازير. 
Bukhary da muslim sun fitar da hadisi acikin sahihansu daga ibn mas'ud. Annabi yace 
إنها ستكون بعدي أثرة وأمور تنكرونها. 
Abinda ake nufi da أثرة 
Shine الإنفراد بالشيء عمن له فيه حق 
Kadaituwa daga inda gaskiya take 
Se sahabbai suka tambayi annabi me ze umarcesu dashi a wannan lokacin. 
Se yace 
تؤدون الحق الذي عليكم ،وتسألون الله الذي لكم. 
Ku bada haqqin dake kanku, Se ku roqi Allah hakkinku 
Imam nawawy acikin sharhinsa Na sahihu muslim.. yace 
فيه الحث علي السمع والطاعة وإن كان المتولي ظالما عسوفا ،فيعطى حقه من الطاعة ،ولا يخرج عليه ،ولا يخلع ،بل يتضرع إلي الله ،في كشف أذاه ودفع شره وإصلاحه. 
Acikinsa akwai kwadaitarwa akan ji da biyayya koda wanda yake riqe da mulkin azzalumine ,Mai tsananin zalumci, za'a bashi hakkinsa Na biyya, baza'ai masa fito Na fito ba, baza'a janye daga al'amarinsa ba ,sedai za'a qanqan da kai ne a gurin Allah domin ya yaye cutarwar sa kuma Ya tunkude sharrinsa kuma Ya shiryar dashi. 

انظر إلي كلام النووي لم يفهم قول رسول الله "وتسألون الله الذي لكم " علي أنه هو الدعاء عليهم. 
Ibn abi asim acikin littafinsa 
السنة 
Yayi babi mai suna 
باب ما أمر به النبي من الصبر عندما يرى المرء من الأمور التي يفعلها الولاة. 

Ibn Abi shaibah Ya fitar acikin musannaf da khallal acikin السنة da ibn abi zamaneen acikin أصول السنة duk sun fitar da athar da isnadi mai kyau daga suwaid ibni gafalah.  
قال لي عمر رضي الله عنه 

يا أبا أمية إني لا أدري لعلي لا ألقاك بعد عامي هذا ، فإن أمر عليك عبد حبشي مجدع ،فاسمع له وأطع ،وإن ضربك فاصبر وإن حرمك فاصبر ،وإن أراد أمرا ينقص دينك ،فقل: سمع وطاعة ؛دمي دون ديني ،ولا تفارق الجماعة. 
Umar Allah ya qara masa yarda yacemin 
Ha kai baban umayyah, bansaniba wataqila bazan sake haduwa da kai ba bayan wannan shekarar. 
Idan aka shugabantar muku da bawa dan habasha mai yankakken ga6a (hanci ko hannu ko qafa da sauransu ) toh ka saurareshi kuma kai masa biyayya, idan Ya dake kayi haquri,in Ya haramta maka abu kayi haquri, in Ya nufi wani abu da ze kawo tawaya a addininka, Se kace naji kuma nayi biyayyah gwara jinina akan addinina, kuma kar ka fita daga jama'ah 
Har yanzu dai. Ibn abdulbar acikin attamheed Ya fitar daga abi ishaq assabai'ee cewa yace.. 
ما سب قوم أميرهم ،إلا حرموا خيره 
babu wasu mutane da zasu zagi shugabansu face Se an haramta musu alkhairinsa 
Ibnul jauzy yace 
من لعن إمامه حرم عدله 

wanda Ya tsinewa shugabansa za'a haramta masa adalcinsa 
Daga cikin abinda yazo daga magabata.. Shine addua ga shugabanni ba addua akansu ba. Kai hasalima malamai suna lissafi mai addua akan shugabanni daga cikin yan son zuciya. 

Imamul barbahary acikin شرح السنة yace  
وإذا رأيت الرجل يدعوا علي السلطان ،فاعلم أنه صاحب هوى، وإذا رأيت الرجل يدعو للسلطان بالصلاح ؛فاعلم أنه صاحب سنة -إن شاء الله -.
Kuma idan kaga mutum yana addua'a (mummuna ) akan shugaban, toh ka sani dan son zuciyane, kuma idan kaga mutum yana addua ga shugaba (Na alkhairi) toh ka sani shi ma'abocin sunnah ne -in sha Allah 

Yahya ibn mansoor Alharrany Alhanbaly wanda akafi sani da ibnul hubaishy .. Ya rubuta littafi sukutum akan wajibcin addua ga shugaba 
Sunan littafin 
دعائم الإسلام في وجوب الدعاء للإمام. 
 Shi wannan malamin ibn rajab Ya kawo tarihinsa cikin ذيل طبقات الحنابلة. Daga cikin manaqib nasa. Akwai fadin gaskiya, inkarin kuskure akan wanda ya aikata, baya mudahana, yana fadan gaskiyane baruwansa kuma Ya tsaya akanta. 

Khallal Ya fitar da magana Abi muslim alkhaulany.. Acikin littafinsa السنة 
Yana mai cewa dangane da shugaba 

إنه مؤمر عليك مثلك ،فإن اهتدى فاحمد الله ،وإن عمل بغير ذلك ؛فادع له بالهدي ولا تخالفه فتضل .

Khallal Ya sake kawo maganar Ahmad bin hanbal acikin littafin nasa inda Ahmad din yake magana kan shugaba 
Yace;
وإني لأدعوا له بالتسديد والتوفيق في الليل والنهار ، والتأييد ،وأرى ذلك واجبا علي.
Kuma lallai inai mas addua Na dacewa da muwafaqa dare da rana ,kuma ina qarfafasa, kuma ina ganin hakan wajibine akaina 
Abu uthman Assabuny acikin littafinsa 
عقيدة السلف أصحاب الحديث 
Yace: 
ويرون الدعاء لهم بالإصلاح والتوفيق والصلاخ ،وبسط العدل في الرعية.

kuma suna ganin yin addua'a a garesu da shiriya da dacewa da shiriya, da yada adalci acikin wadanda ake shugabanta 
Imamul barbahary yace; 

فأمرنا أن ندعو لهم بالصلاح ،ولم نؤمر أن ندعو عليهم ،وإن ظلموا وجاروا ،لأن ظلمهم وجورهم علي أنفسهم وصلاحهم لأنفسهم وللمسلمين. 
Se aka umarce mu da muyi musu addu'a Na shiriya, kuma ba'a umarce mu muyi addua(mummuna) akansu ba koda sunyi zalumci 
Akansu yake, shiriyansu kuma domin kansu ne da sauran musulmai 

Abubakr al-isma'ily cikin اعتقاد أهل السنة 
Al-ajurry cikin الشريعة 

Duk sun bayyana cewa aqidar salaf itace addua ga shugaba Na addua akansa ba. 

Sannan adduar ibn jubair yayitane a gaban hajjaj, ba cikin mutane yazo yadinga yadawa ba.. tareda cewa a lokacin fitinar hajjaj akwai wadanda suka fita ga hajjaj a bisa iqrarin kafurcinsa ko ganin halaccin hakan. Kamar wadanda suka fita tareda ibnul Ash'ath .. wasu kuma sun fita amma suka dawo..wasu kuma sunyi nadama daga baya kamar shi ibn jubair din. 

والصحيح المقطوع به أصوليا: وجوب الإعتبار بالإجماع الحاصل بعد النزاع.

Dan uwana koh ince malamina zega nayita kawo maganal khuruji.. wala'alla yace ai banyi fito Na fito da makami ga shugababa 
Se ince khuruji ba kawai fitowa da makami bane.. malamai sunce khuruji kala biyune.. Akwai Na makami da kuma Na harshe.

Ga dalilina kamar haka 

Manzon Allah yace hannu da qafafu duk suna zina.. Se Ya bayyana siffan zinan su.. Se yace farji shike gaskata hakan 

Hakama Khuruj yana kasancewa da kalma da tunzura mutane, da qasqantar da shugaba, da ta hanyar rubuce rubuce da sauransu 

Ahankalce.. Kafin mutane su dauko makami domin yaqan shugaba.. Magana shike zuwa a farko 

Ibn hajar Ya siffanta wasu nau'i Na khawarij. 
Yace 
القعدية؛الذين يزينون الخروج علي الأئمة ولا يباشرون. 
Alqa'diyyah: sune masu qawata fito Na fito ga shugaba batareda sun yi gaba da gaba ba.

Sheikh saleh Alluhaidan yace

الخروج لا يقتصر علي الخروج بقوة السلاح أو التمرد بالأساليب المعروفة فقط، بل إن الخروج الخروج بالكلمة أشد من الخروج بالسلاح ،لأن الخروج بالسلاح والعنف لا يربيه إلا الكلمة 
Khuruji bai tsaya a iya fitowa da qarfin makami ko kangarewa da usulubai sanannu kadai ba , kai khuruji da kalma ma yafi tsanani akan khuruji da makami ,domin khuruji da makami da tsanani ba abinda ke renonsu face kalma.
Sheikh ibn uthaimeen a ta'aliqinsa akan risalar shaukany رفع الأساطين في حكم الإتصال بالسلاطين  
Bayan Ya kawo maganar manzon Allah 
إنه يخرج من ضئضئي هذا الرجل من يحقر أحدكم صلاته مع صلاته. 
Se yace 
وهذا أكبر دليل علي أن الخروج علي الإمان يكون بالسيف ،ويكون بالكلام ،وهذا ما أخذ السيف علي الرسول صلي الله عليه وسلم ،فما يوجد في بعض كتب أهل السنة من أن الخروج علي الإمام هو الخرو بالسيف ،فمرادهم بذالك الخروج النهائي.
Dan haka cabin shugaba DA aibata shi nau'ine Na khuruji kamar yadda yaxo daga maganganun malamai. 

Addua a akansu da sharri Na shi akasan magabata akai ba. 

Idan zamu sallama akan adduar wanda aka zalumta.. Toh badai yayishi a bainal jama'ah ba 

Sedai yayi shi kadai, daga shi Se Allah.. Ko kuma agabn shi shugaban. 

Aqarshe zan rufe da hadisin Manzon Allah da yace 

خيار أئمتكم الذين تحبونهم ويحبونكم ،وتصلون عليهم ويصلون عليكم 
Mafi alkhairin shugabanninku sune wadanda kuke sonsu suma suke sonku, kuma kuke musu addua suma sunai muku addua 

Allah Ya fahimtar damu gaskiya
:
Post a Comment (0)