♝■ http://sirinrikemiji.blogspot.com/?m=1* ■♝
♜ Sirrin ■ rike ■ miji ♜
✎+2348037538596
™www.sirinrikemiji.com
▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒▒
✎. Matsalar Rashin Bayyanar Da Soyayya
Wannan matsala ta rashin bayyanar da soyayya ta zama ruwan dare a cikin rayuwar auratattar Hausawa, ta yadda ma’aurata kalilan ne suke rayuwar aure mai cike da nuna so da kauna a cikinsa. Ko a cikin iyali za a tarar yara kanana ne kadai ke samun dadaddiyar soyayya ta hanyar wasa da ake musu, yawan runguma da sumba; kalamai masu dadi da yawan yaba masu da sanya su murna ta hanyar murmushi da dariyarsu, haka da zarar ransu ya baci kuwa nan da nan za a rarrashe su, kuma ko sun yi laifi ba a rikonsu da laifin har ya sa a daina bayyanar musu da
kaunar da ake masu.
Amma su ma din suna girma irin wannan abubuwan suna raguwa har sai ta kai soyayyar da ake nuna masu kadai ita ce ta samar masu da duk abubuwan bukatarsu amma ba irin dadadan abubuwan da akan yi masu lokacin da suke kanana.
Idan muka yi nazari za mu fahimci duk rai na dan Adam na bukatar irin wannan dadadan abubuwa, ba dan Adam kadai ba, duk halittun
Allah SWT na bukatar yanayin kulawa irin haka.
Wannan fili ya yi ta samun koken wasu daga cikin
ma’aurata kan yadda suke fuskantar wannan matsala daga wajen abokan zamansu:
■✎. Al’ada: Yanayin al’ada na taka muhimmiyyar rawa sosai wajen rashin bayyanar da soyyaya a cikin rayuwar aure.
A al’adance ba wata soyayyar da ake yi da ya wuce namiji ya samar da kayan bukatun rayuwa ita kuma mace ta kula da gida da yara; kowa yadda ya tashi ya ga ana yi a gidansu, a garinsu, haka zai yi, wanda ko duk aka ga ya fita daban ta hanyar yin abubuwan nuna kauna da kulawa nan da nan za a sami wani lakabin da aka yi masa saboda hakan.
■✎. Halin Mazantaka: Yanayin halayyar da namiji tasa ya fi iya nuna soyayyarsa da kulawarsa ta bangare daya kawai, shi ne ta hanyar sadaukar da dukiyarsa, lokacinsa da karfinsa ga iyalinsa; wannan kam lallai shi ya fi muhimmanci kuma ya fi amfani, amma dayan da ba su cika Yi ba, shi ya fi dadi da sa kwanciyar hankali da aminci a zuciya.
■✎. Tsoro: Wannan shi ne ja gaba daga cikin abubuwan da ke hana ma’aurata bayyanar da soyayya tsakaninsu; yawanci ma’aurata maza na ganin bayyanar da soyayya, kamar bayyanar da rauninsu ne, kuma hakan zai sa matan
su raina su, su kuma daina ba su kima. Su kuma matan na tsoron in su cika bayyana soyayyarsu, mazan za su dauke su ba bakin komai ba, kuma ba za su samu irin kulawar da suke so ba daga gare su.
✎. Rikon laifi: Kasawar wasu ma’auratan ga yafe laifin da
ma’auransu suka yi musu na hana su iya bayyanar da
soyayyarsu, domin rikon laifi na dakushe soyayya ko ma ya sumar da ita gaba daya.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba insha Allah, da fatan
Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe,
amin.
*Islamic medical center*
*・ Sirrin・���������ιrε・ℳiji*
���� +2348037538596
sirrinrikemiji@gmail.com
Latsa wannan domin samun Read more: