ANNABI DA SAHABBANSA // 013



_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

       _*ANNABI DA SAHABBANSA // 013*_
.
_Lokacin Da Annabi Saw Ya Kai Shekara 35 A Sannan Ne Quraishawa Suka Yi Tunanin Sake Gina Qa'aba, Domin A Lokacin Ginin Gaba Dayansa Zira'i Tara Ne Tun Zamanin Annabi Isma'il As, Kuma Bai Da Rufi, Wannan Damar Ta Sa Wasu Barayi Suka Shiga Suka Sace Kayan Dake Ciki, Banda Wannan Kuma Dakin Dadadde Ne Ya Shekara Dubbai Dole Katangunsa Su Tsattsage, Baya Ga Bayan Ma An Yi Ambaliyar Aram Wace Ta Kai Gare Shi Har Ta Kusa Rusa Shi Gaba Daya, Shi Ne Quraishawa Suka Yi Niyyar Sake Gina Shi Don Kare Matsayinsu Na Masu Kula Da Shi._
.
_Sai Dai Abin Mamaki Sun Kafa Sharadin Cewa Kar Wani Kudi Ko Kaya Ya Shiga Cikin Ginin Sai Na Halas, Ba A Buqatar Kudin Karuwa, Kudin Riba, Ko Kudin Da Aka Cuci Wani, Da Aka Zo Fara Aikin Sai Suka Ji Tsoron Rusa Dakin Har Sai Da Walid Bnl Mugira Almakhzumi, Wato Mahaifin Khalid Ya Fara Rusawa, Da Sauran Suka Ga Ba Abin Da Ya Same Shi Sai Su Ma Suka Sa Hannu Har Sai Da Suka Kai Fondishon Din Da Annabi Ibrahim As Ya Yi, Daganan Suka Yi Shirin Daukar Gini, Sai Suka Rarraba Aikin Aka Ba Wa Kowace Qabila Aikin Da Za Ta Yi._
.
_Da Haka Kowace Qabila Ta Tara Bulullukanta Ta Fara Aiki Qarqashin Wani Injiniya Dan Rum Mai Suna Baqum, Lokacin Da Ginin Ya Kai Inda Za A Aza Wannan Baqin Dutsen Da Ake Kira Alhajarul Aswad Nan Ne Aka Sami Hayaniya Ta Tsawon Kwana Hudu Kan Tantance Wanda Zai Sanya Shi A Dakin, Shin Daga Wace Qabila Yake? Abin Ya Kusa Ya Zama Musu Babban Yaqi, Sai Da Abu Umayya Bnl Mugirah Almakhzumiy Ya Ba Su Shawarar Cewa Su Tsayar Da Abu Daya Kan Duk Wanda Ya Fara Shigowa Ta Qofar Masallacin Ko Daga Wace Qabila Ya Fito Shi Ne Zai Fadi Yadda Za A Yi._
.
_Duk Qabilun Suka Amince Da Haka, Cikin Ikon Allah Sai Ga Annabi Saw Ya Shkgo, Suna Ganinsa Sai Duk Suka Yi Shewa Gaba Daya: "Wannan Ai Amintacce Ne, Mun Yarda Da Shi" Lokacin Da Ya Qarisa Wurinsu Suka Gaya Masa Abin Da Ke Faruwa Da Wanda Suke Buqata, Shi Ne Ya Nemi Su Kawo Shimfida, Ya Dauki Dutsen Ya Dora A Tsakiya, Sauran Qabilun Duk Suka Kama Gefen Shimfidan Suka Kai Wurin Da Za A Saka, Ya Dauki Dutsen Da Hannunsa Ya Dora, Koda Yake Jayayyarsu Ta Kawo Haka, Amma Allah Sw Ya Riga Yanke Cewa Manzonsa Zai Dora Dutsen._
.
_Annabi Saw Kafin Annabci Ya Tara Duk Abubuwan Da Mutum Zai Nema Don Ya Zama Na Gari, Yana Da Lafiyayyen Tunani, Kyakkyawan Hangen Nesa, Ga Manufa Mai Kyau, Bai Yin Magana Sai Da Dalili, Wannan Ya Ba Shi Dama Sosai Wajen Jujjuya Abin Da Zai Kai Ya Komo, Ga Gaskiya A Duk Lamarinsa, Wadannan Baiwa Da Allah Ya Yi Masa Ya Gano Rayuwar Jama'a A Wuri Daban-daban, Ya Iya Fayyace Abubuwan Da Suka Dace Ya Shiga A Yi Da Shi, Da Wadan Da Ba Su Dace Da Shi Ba Ya Nisance Su, Bai Taba Shan Giya Ba, Bai Ci Dabbar Da Aka Yanka Wa Gumaka Ba, Bai Taba Zuwa Taron Bautar Gunki Na Shekara-shekara Ba Bare Wani Party, Tun Tasowarsa Bai Yarda Da Su Ba._
.
_Babban Abin Da Annabi Saw Ya Tsana Shi Ne Bautar Gumaka, Yana Da Haquri Matuqa Amma Bai Yarda Da Rantsuwa Da Lata Ko Uzza Ba, Kamewarsa Kuwa Tabbatacce Ne Kuma Tsararre Daga Allah Sw, A Hadisin Da Buhari Ya Rawaito Ya Ce: Lokacin Da Ake Ginin Qa'aba Annabi Saw Da Abbas Suka Fara Dauko Bululluka, Sai Abbas Ya Ce Wa Annabi Saw "Tattaro Zanenka Ka Nade Wuyarka Sabo Da Bulon Da Kake Dauka" Nan Take Ya Fadi Qasa, Idonsa Ya Yi Sama, Da Ya Farfado Ne Ya Ce "Zanena, Ku Ba Ni Zanena" Aka Daura Masa Zanen._
.
_Da Wannan Zamu Iya Cewa: Annabi Saw Ya Fi Kowa A Zamaninsa Kyakkyawan Hali, Dadin Zance, Mutuntuka, Kyawun Maqwabtaka, Haquri, Gaskiya A Wurin Magana, Sauqin Hali, Kamewa, Karamci, Aiki Mai Kyau, Alkawari, Amana A Kan Amanar Har Ana Kiransa Amin, Matarsa Khadija Ra Tana Cewa: "Yakan Dauki Nauyin Jama'a, Ya Kawo Abin Da Babu, Ya Taimaki Baqo, Ya Agaza A Kan Wasu Masifu" Tabbas Irin Dabi'un Da Annabi Saw Ya Tattara Ya Wuce Duk Inda Mutum Yake Zato Tun Bai Girma Ba, Da Haka Allah Sw Ya Turo Shi Zuwa Ga Daukacin Jama'a Gaba Daya._
.
_Lokacin Da Ya Kusa Kaiwa Shekara 40, Wadannan Halaye Da Dabi'u Sun Gama Riskar Jama'a, Kowa Ya San Shi Da Su, Har Ya Zama Abin Qauna Ga Kowa Sama Da Yadda 'yan Nigeria Suke Qaunar Buhari Sabo Da Dabi'unsa, A Daidai Wannan Shekarar Ce Annabi Saw Ya Fara Son Kadaituwa Don Ibada, Sai Ya Riqa Daukar Soyayyen Gari Da Ruwa Ya Nufi Kogon Hira, Wanda Yake Wani Babban Dutse Da Ake Ce Masa Jabalun-nur, Yana Nesa Ne Makka Da Kusan Mil 2, Tsawon Dutsen Ya Kai Zira'i 4, Fadinsa Kuma Zira'i 3._
.
_*✍🏼Baban Manar Alqasim*_
Post a Comment (0)