SANARWA MAI MUHIMMANCI

SANARWA MAI MUHIMMANCI
**********
Ka karanta tabbas Zai amfaneka idan ma bai amfaneka ba zai amfani 'danka, 'yarka ko kuma qanenka ko 'dan uwanka.

Tun kusan Watan January nayi Rubutu akan 'yan Mata masu 'dabi'ar yin Madigo (Lesbian), tun kusan wancen lokaci na samu kira daga wata baiwar Allah Wadda ta bayyanamin Dalilin shigarta harkar madigo da kuma halin da take ciki.

Yarinyar wacce mun dau kusan Mintuna arba'In mun waya ta shaida min dalilin shigarta Harkar madigo, In da ta bayyana min a makarantar gaba da Secondry aka koyar da Ita wannan muguwar 'dabi'ah.

"Bayan kaini makaranta mu hudu ne a dakin da nake, kuma nice karama a duk cikin wayanda muke daki 'daya da su, ranar da nazo na fara fahimtar 'yan Iska ne, domin kuwa a gado 'daya naga suna yin bacci duk da kowace nada nata gado."

"A haka har na fahimci me suke yi domin kuwa wani lokacin a gabana suke sheke ayarsu."

Yarinyar taci gaba da gayamin cewa, a hankali idan suna yi sai taji sha'awa ta taso mata, kwatsam rannan sai suka bukaci ta shiga cikinsu domin jin dadi.

Da farko sai ta nuna musu ai ita bata sha'awar wannan mu'amula kuma tana ma son ta chanja 'daki ne domin kada ta takura musu.

Anan ne suka nuna mata ai babu damuwa tayi zamanta a dakin nasu domin halayenta na burgesu.

Kwatsam sai ranan suka nuna mata ai ta shigo cikinsu yafi tunda Allah bai fadi azabar da za'ayiwa mata 'yan madigo ba sai 'yan Luwadi.

Sannan kuma tayi wannan shi ya fiye mata da taje tayi zini ko ta aikata Mistabution (ISTIMINA'I).

Ta shaida min da irin wayannan kalamai aka sanya ta a madigo kuma wallahi yanzu bata sha'awar kowane namiji, haka kuma bata sha'awar aure.

Ta kara shaidamin Cewa, Ita kadai ta lalata yara bata san adadiba, kuma yanzu tana son ta tuba amma ba ta san yanda zatayi ba.

Anan na bata wasu shawarwari tare da nuna mata muddin ta mutu bata tuba ba to kuwa akwai matsala domin Allah zai mata Ukuba fiye da yanda take tunani.

Wannan yarinyar tayi godiya ta kuma bukaci duk ranar da na samu lokaci don Allah Inyi fadakarwa game da Irin Wannan 'yan madigon Masu nunawa mutane madigo bai da wata azaba da aka tanadarwa masu yinsa, haka kuma macce zata ji dadi ba tare da ta rasa budurcin ta ba.

Bayan Wannan Jiya14 ga watan October Jaridar Aminiya ta fitarda wani rubutuna game da Maza 'yan Luwadi.

Kusan karfe 10 na dare wani bawan Allah ya kirani, daga daukan wayan na san hankalinsa a tashe yake muryarsa na karkarwa.

Ya shaidamin yana 'daya daga cikin masu neman Maza kuma kusan Shekarar sai 15 yana wannan lalata yanzu kuma kusan shekarar sa 10 da aure amma har yanzu ya kasa dainawa.

Yace min hakika babu yanda baiyi ba domin ganin ya bar wannan muguwar 'dabi'ah amma ya kasa.

Bayan gama wayar da shi tare da gama bashi shawarori akan ya tuba ya kuma kauracewa wayanda suke wannan ta'adi.

Cen kusan karfe 12 na dare wani ya kirani ya shaidamin daga wata jami'ah (dake arewa ) yake kira na, ya shaidamin yanda aka sanya shi wannan muguwar 'dabi'ah ta luwadi (Wa'Iyazubillah).

Ya gaya min Cewa, wani ne ya sanya shi wannan muguwar 'dabi'ah ta hanyar nuna masa ya zo su rika yin Romace ba tare da sun sadu ba. Wannan yafi yaje yayi zina.

Ya gayamin a hakan ya amince domin a tunaninsa Romac ba komai ba ne, ya gayamin a cikin Romace din ne kawai wata rana ya afka masa yayi masa luwadi.

Ya shaidamin hakika yanzu baya sha'awar macce, Sai dai maza, yace min wani lokaci har kashisa yake dauka ya shafa a al'aurarsa idan wannan sha'awar ta taso masa (Wa'Iyazubillahi).

Yan da kyau 'Yan Uwa mu rika Kula da Suwa Qannenmu da 'ya'yanmu da Abokananmu ke mu'amula domin gudun yin dana sanin a gaba.

Duk wanda yace maka kazo kuyi romace yafi kaje kayi Zina Wallahi karya yake maka Yana so ne kawai ya halaka maka rayuwa.

Sanan yana da kyau 'yan mata su san cewa, da madigo da Luwadi duka daya ne babu banbanci a wajen Azaba a gobe Qiyama.

Sannan yana da kyau su san anya mafi sauri ta kamuwa da cutar Infection Itace ta hanyar yin madigo (lesbian).

Sannan masu yi yana da kyau su sani daga ranar da kikayi sanadiyar fadawar Wata a cikin wannan Muguwar 'dabi'ah to kuwa duk lokacin da akayi lesbian ko luwadin da ita to sai an rubuta maki/ka zunubi koda kana Cikin kabari ne.

Wannan Muhimmiyar Sanarwa Ce, Idan ka taimaka wajen Yada ta to ka taimaka wajen ya'da Alheri. Idan kuma ka qi yadawa to ka yi hasarar tarin Ladar da Za'a samu.

Rubutawa a 
Sat 15-10-2015

Jamilu Sani Sokoto
Sat 15/10/2018


Post a Comment (0)