GYARA KAYANKA /KI

GYARA KAYANKA /KI


 
.
Lokaci yazo mana da wata irin wayewa ta
ban mamaki. Wayewar da take jefa maza
da
mata halaka mai muni.
.
Kaso 95% cikin 100% na soyayyar yanzun
saika samu daya daga cikin abubuwan nan
ukku dana lissafa.
.
Macen data kama kanta. Bata son saurayi
yai
mata maganar banza itace bagida jiya.
Itace
bata waye ba.
.
Acikin abokai. Namijin da duk baya
wannan
shine ya zama koma baya. Shine wanda
bai
iya tsara mace ba.
.
*SHAN MINTI* kama daga kan kisses yan
rungume rungume da shafe shafen juna
da
masoyan yanzun suka dauka ba komai
bane
sai hanyar nunama juna tsantsar soyaysai hanyar
nunama juna tsantsar soyayya
da
yardar dake tsakaninsu.
.
Zakaji da yawan samari na ce ma yan
matan
su "Haba sai kace baki yarda dani ba.
Wannan tsakaninmunne fa. Waya gani
balle
yaji?"
.
Seriously? Da gaske babu wanda yagani?
Da
gaske babu wanda yaji?
.
Tambaya uku nake dashi.
.
1. Zaku iya wannan a gaban iyayenku?
.
2. Zaku iya a gaban bainar jama.a?
.
3. Saboda me ba zaku iya ba?
.
Yan uwa ku zauna ku nutsu kuyi ma kanku
wannan tambayoyin. Idan har ba zaku iya
a
gaban wa.annan mutanen ba. Saboda jin
kunyar idanuwansu ko akasin hakan.
.
Saboda me zaku yi a gaban wanda ya
halicci
wa.annan mutanen. A gaban Allah da
yake
ganin dukkan barnar da kuke aikawa?
.
Duk wannan barnar bata isa ba. Bayan an
gama ta an koma gida sai kuma a dauki
waya...
.
A kama abin nan da ake kira da *SEX
CHAT*
maganganu na fitsara da rashin kunya.
.
Haba yan uwa? Ina koyarwarku ta addini?
Ina tarbiyar ban da iyaye keta kokarin
doraku akai?
.
A wannan *SEX CHAT* dinne ake aikata
badala iri iri bayan maganganu na batsa
har
da hotuna.
.
Ya Allah kai mana tsari daga shaidan da
tarkokinsa. Babu kunya babu tsorob Allah.
Babu tsoron kwanciyar kabari inda babu
wanda zai kawo maka dauki sai
halayyarka.
.
Haka za.a daga camera ana daukar
hotunan
jiki ana turama juna.
.
Yar uwa ina hankalinki ya tafi? Ina
kunyarki?
Ina adaninki da lullubi da tattalin jikin da
kike yi na shekaru?
.
Saboda me soyayya zata rude ki har haka?
Wanne tabbaci kike dashi hotunan nan ba
zasu kai gaba ba?
.
Wanne tabbaci kike dashi cewar shi zaki
aura? Idan ma kin aure shi me yai saura a
jikinki da zakiyi masa ado dashi?
.
Idan baki aure shi ba da wanne ido zaki
ware ki sauke kan mijin da kika aura?
Bayan
kinsan cewa jikin nan da kikazo mishi
dashi
waniya dade da kallewa harma da
tabawa?
.
Ya Allah. Yar uwa ki farka dan girman
Allah.
Ki tuba ki gane illar abubuwan nan tun
kamun lokaci ya kure miki
.
Haba dan uwa. Haba dan uwa. Dan kasan
tana sonka sai ya baka dama kajata zuwa
ga
halaka?
.
Baka da kannai ne? Me zaka ji in akai
musu
haka? Da wanne ido zaka kalli
Mahaliccinka?
.
Zaka haifa wata rana. Wallahi inhar baka
tuba ba zunubanka ba kanka kawai zasu
tsaya ba. Zaka shafa ma makusantanka.
.
Shin ina kuka ajiye *Tsinuwa* da Allah
yaima wanda ya kalli tsiraicin wani? Ko
kuna
tunanin ba zata same ku ba?
.
Duk wannan abubuwan sai an kara da
*PHONE SEX* ?
.
Duk kuma sai ku daura alhakin abubuwan
da kuke aikata akan *SHA.AWA* ko?
.
Me akace kayi in sha.awa na damunka?
Allah
yace zai kare ka idan ka kame kanka da
yin
azumi ko da sau biyune a mako.
.
Idan ka tsarkake idanuwanka da zuciyarka
da kunnuwanka daga jin abubuwan da
zaka
tsokano ma kanka fitina.
.
Babban takaici sai kuma kaji ance tunda
har
ba.a kusanci juna ba. Ba *Zina* bace ba
ko?
.
Daga kan *Romance* *Sex chat* *Phone
sex* gabaki daya *zina* ce.
.
Allah Yace "KA DA MU KUSANCI ZINA"
.
Domin illolinta suna da yawa.
A)fuskantar fushin
Allah idai ba'a tuba ba
.
B)zubewar mutuncin junansu da
kuma wadanda suka san sun
aikata haka.
.
C)QeQashewar
zuciya da zai haifar da rashin
kunya da tsoran Allah,da
rashin ganin Qimar
sabon
.
D)Lalata tarbiyyar
Al'umma da yadan fasadi.ba
abin da yake saurin Lalata
tarbiyyar Al'umma cikin
gaggawa irin zina.*manzo
Allah(s.a.w)yana cewa"Allah
ya haramta zina saboda abin
da take haifarwa na barna
tana jawo kisan kai da rashin
adalci da rashin
tarbiyya"
.
E) Tana jawo talauci
da fatara a cikin
Al'umma
.
F) tana haifar da
miyagun cututtuka a cikin
Al'umma misali cutar HIV
(AIDS)da sauransu,Manzo
Allah yana cewa,idan zina tayi
yawa a Qarshen duniya sai
ake mutuwa bagatatan(farat
daya)
.
G)Zubar da darajar aure
misali duk mazinaci da
mazinaciya basa ganin darajar
aure
.
H) kashe dandanon
ma'auranta.ita zina tana hana
wa mai yin ta jin dadin
matarsa ta gida ko mijinta na
gida.shi yasa ma manzo Allah
(s)yake cewa."kada ku yi zina
sa ta gusar muku da dandanon
matanku da kamun
kansu.
.
*KWANCIYAR KABARI* yan uwa abune
mai
girma wallahi. Ka tuna yanda kake ji
yanzun
haka lokacin zafi.
.
Kana tsakar gida inda yake a bude
ballantana a cikin kasa. Inda babu ko kafar
da allura zata shiga. Babu komai face
kyawawan halayenka.
.
Nikam zan tsaya anan.
.
Allah ka yafe mana ka bamu ikon gyarawa.
Allah ka sa mufi karfin zuc
Post a Comment (0)