SHARHIN FIM ƊIN CAPTAIN AMERICA: THE FIRST AVENGER




SHARHIN FIM ƊIN CAPTAIN AMERICA: THE FIRST AVENGER 

* Bada Umarni - Joe Johnston

* Ɗaukar Nauyi - Kevin Feige

* Rubuta Labari Da Tsarawa - Christopher Markus/Stephen McFeely

 * Taken Fim - Alan Silvestri

Captain America: The First Avenger fim ɗin jarumta ne da aka fitar da shi a cikin shekara ta 2011 a Ƙasar Amurka. Labarin fim ɗin ya samo asali ne daga littattafan almara mai suna Captain America wanda Joe Simon da Jack Kirby suka wallafa a ƙarƙashin Kamfanin Marvel Comics. Marvel Studios shi ne Kamfanin da ya shirya wannan Fim, Yayinda Kamfanin Paramount Pictures ya yaɗa shi. Captain America: The First Avenger shi ne Fim na biyar daga cikin Fina Finan duniyar Marvel mai suna Marvel Cinematic Universe (MCU). 

An fara ɗaukar wannan fim ne a cikin watan Yuni 2010 awurare mabanbanta da suka haɗa da Landan, Manchester, Caerwent , Liverpool da kuma Los Angeles. An Kuma saki fim ɗin a Hollywood a ranar 19 ga watan Yuli 2011 kafin aka sake shi a ko'ina ranar 22 ga watan Yuli 2010 a zubin 3D. 

Fim ɗin ya samu gagarumar Nasara inda ya kawo kuɗi kimanin Dala Miliyan $370 a harkar Kasuwancin Fina Finan duniya baki ɗaya. Bugu da ƙari, fim ɗin ya samu yabo sosai a wurin jama'a da kuma masana a harkar Fina Finai, musamman irin ƙoƙarin da jarumin fim ɗin yayi, labarin da kuma bada umurnin fim ɗin. Sai dai duk da haka wasu sun caccaki fim ɗin. Anyi na biyu da na ukun wannan Fim. 

LABARIN FIM ƊIN 

Fim ɗin ya fara ne yayin da aka nuno wasu malaman kimiyya sun binciko wani tsohon jirgin sama da ya daskare a cikin wani kogin ƙanƙara. Daga nan kuma sai aka mai da mu 1942 inda aka nuno Wani jami'in Dakarun Nazi tare da mutanen sa sun je Norway sun sace wani mashahurin dutse da ake kira da "Tesseract", shi wannan dutse yana ɗauke ne da wani irin ƙarfin tsafi na gaban kwatance. 

A can kuma birnin New York, an ƙi ɗaukar Steve Rogers a matsayin Soja domin zuwa Yaƙin duniya ma biyu saboda ƙarancin lafiya da kuma rashin kuzarin jiki.

Yayinda suka je wajen wani taro dangane da Cigaban harkokin fasaha tare da abokinsa Saje Bucky Barnes, Rogers Sai ya ƙara yunƙurin shiga aikin soji. Nan dai su kayi ta gardama a tsakanin su, inda Rogers yake ƙara tabbatar wa da Bucky cewa shima yana so ne ya bada tasa gudunmuwar a wannan yaƙi da ake tafkawa. 

Ashe duk wannan Tattaunawa da suke yi Dr. Abraham Erskine Yana jin su, don haka sai ya bada dama aka ɗauki Rogers, sannan aka saka shi a cikin jerin sojojin da za'a fara yiwa gwajin wata Allura wacce zata ƙarawa komai na jikin su inganci. Dr. Abraham dama shi ke kula da wannan fanni tare da taimakon Kanal Chester Phillips, da kuma wata Jami'ar Birtaniya mai suna Peggy Carter.

Phillips da fari ya ƙi amincewa da batun likita Erskine kan cewa Rogers shi ne wanda yafi cancanta da wannan aiki, amma daga baya da yaga ya aikata wani aiki na rashin son kai sai ya saduda.

 Ana I gobe za'a aiwatar da wannan aiki, sai likita Erskine ya sanarwa Rogers da cewa akwai wani da ake kira da Schmidt wanda aka yiwa irin wannan aikin kafin a samu tabbaci akan sa, kuma ya samu mummunan lahani a Sakamakon hakan. 

Schmidt da Dr. Arnim Zola su kuma suna ta zuƙo ƙafin da ke jikin wannan dutse na Tesseract domin su inganta ƙere-ƙeren Zola wajen samar da makaman da zasu canja duniya baki ɗaya. Schmidt ya gano inda Erskine yake sai ya aika Fitaccen Masheƙi Heinz Kruger domin ya kashe shi. 

Yayin da Dr. Erskine ya saka Rogers akwatin yin wannan aiki sai yayi masa wata Allura ta musamman, an dai gudanar da wannan aiki cikin nasara, domin ana kammalawa sai ga Rogers ya ƙara tsayi kuma ya zama curarren jarumin namiji. Sai dai kuma nan take murna ta koma ciki sakamakon kashe Dr. Erskine da Kruger yayi. Nan fa Rogers ya bishi ya kamo shi, sai dai kafin ya tatsi bayanai daga gare shi sai ya kashe kansa. 

Kasancewar Dr. Erskine ya mutu, kuma babu wanda ya san yadda za'a iya haɗa wannan allura, sai sanatan Amurka Brandt ya sa Rogers ya dinga Zagayawa gari-gari cikin wasu kaya masu kyau a matsayin "Captain America" domin ƙarawa jama'a ƙwarin guiwa tare da kawo haɗin kai a tsakanin su dangane da wannan yaƙi da suke fuskanta. Yayin da a gefe kuma masana a fannin kimiyya suke ta Karantar sa domin su gano yadda zasu iya canja wannan aiki da akayi masa. 

A 1943, yayin da Rogers yake Zagayawa sai ya fahimci cewa tawagar su Barnes ta faɗa hannun maƙiya. Ko da jin wannan labari, sai Rogers yaƙi yarda da cewa Barnes ya mutu, don haka sai yasa Carter da Injiniya Howard Stark suka kai shi sansanin maƙiya domin ya kaiwa kamammun ɗauki shi kaɗai. 

Kafin kace kwabo Rogers ya ratsa ta cikin wannan sansani inda ya tseratar da Barnes tare da sauran waɗanda aka kama sannan ya tunkari Schmidt, anan ne Schmidt ya cire fuskar da ya saka inda Rogers yaga ashe babu komai a kansa face wani jan ƙwarangwal ɗin ƙarfe wanda hakan yasa ake masa laƙabi da RED SKULL. 

Schmidt dai ya samu damar guduwa, Yayinda shi kuma Rogers ya koma gida tare da sauran kuɓutattun sojojin da ya ceto. Daga nan kuma sai ya ɗauki Barnes, Dum Dum Dugan, Gabe Jones, Jim Morita , James Montgomery Falsworth da Kuma Jacques Dernier domin su kaiwa duk wani sansanin Hydra da suka sani. Stark shi kuma ya taimakawa Rogers da Makamai, mafi shahara ita ce garkuwar Ƙarfen sa wacce aka ƙera ta da Sinadarin Vibranium, wacce kusan tafi gaban Lalatawa. Rogers da tawagar sa sun samu damar tarwatsa Sansanonin mayaƙan Hydra da dama tare da duk wani yunƙuri da zasu yi. 

Watarana sai tawagar ta kaiwa wani jirgin ƙasa wanda ke ɗauke da Zola a cikin sa hari. Rogers da Jones sun yi nasarar kama Zola, amma Barnes ya faɗa wani ƙaton rami inda kowa yayi tsammanin ya mutu. 

Da taimakon bayanan da Zola ya bayar ne suka samu damar gano asalin matattarar Hydra tare da shirin Schmidt na ganin ya jefa makami mai linzami a manya-manyan biranen Amurka. 

 Rogers tare da waɗannan abokai nasa sun samu nasarar hana wannan ta'adi afkuwa, sannan Rogers ya hau jirgin da Schmidt yake kai inda suka fafata. A wannan fafatawa ne asalin mazubin da ke riƙe da wannan dutse na Tesseract ya lalace, Schmidt kuma da giɗi-giɗi ya riƙe shi da hannun sa. Hakan yasa ƙarfin wannan dutse ya buɗe wata ƙofa a sararin samaniya ya shige da shi, yayin da shi kuma dutsen ya ɓula jirgin ya faɗa cikin ruwa. 

Ganin cewa babu wani wuri da zai iya saukar da wannan jirgi lami-lafiya, sai Rogers ya tsunduma cikin ruwa daga shi har jirgin. Daga baya Howard Stark ya samu damar gano wannan dutse daga ƙasan login, amma babu alamar jirgin balle Rogers,hakan yasa kowa yayi tunanin ya mutu. 

Kwatsam sai Rogers ya farka a wani ɗakin asibiti mai zubi irin na 1940, amma nan take ya gane cewa akwai matsala, don haka sai ya fito a guje in da ya tsinci kansa a Gaban sha-tale-talen Time Square na yanzu, a dai dai wannan lokaci ne kuma Nick Fury wanda shi ne Daraktan ƙungiyar S.H.I.E.L.D. Yake sanar da shi cewa yayi bacci na tsawon kusan shekaru 70. 

A wata fitowa ta ƙarshe, an nuno Fury Yayinda ya tunkari Rogers da batun wani aiki wanda zai kawo ci gaban zaman lafiya baki ɗaya a duniya. 

JARUMAN FIM ƊIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SA. 

* Chris Evans - Steve Rogers / Captain America

 * Tommy Lee Jones - Chester Phillips

* Hugo Weaving - Johann Schmidt / Red Skull 

* Sebastian Stan - "Bucky" Barnes

* Hayley Atwell - Peggy Carter

* Dominic Cooper - Howard Stark 

* Neal McDonough - Timothy "Dum Dum" Dugan 

* Derek Luke - Gabe Jones

* Stanley Tucci - Abraham Erskine

* Samuel L. Jackson - Nick Fury 

* Kenneth Choi - Jim Morita

* Bruno Ricci stars Jacques Dernier

* JJ Feild - James Montgomery Falsworth

* Toby Jones - Arnim Zola

 * Lex Shrapnel - Gilmore Hodge

 * Michael Brandon - Brandt

* Natalie Dormer - Lorraine

* Jenna Coleman - Connie, 

<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________

●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees 

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees 
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...
Post a Comment (0)