SHARHIN FIM ƊIN IRON MAN 2

SHARHIN FIM ƊIN IRON MAN 2

* Bada Umarni - Jon Favreau

* Ɗaukar Nauyi - Kevin Feige

* Rubutawa Da Tsarawa - Justin Theroux

* Taken Fim - John Debney

* Tacewa - Dan Lebental/Richard Pearson

Iron Man 2 Fim ɗin jarumta ne da aka fitar da shi a cikin shekara ta 2010 a Ƙasar Amurka. Labarin fim ɗin ya samo asali ne daga littattafan almara mai suna Iron Man Wanda Stan Lee, Larry Leiber, Don Heck da Jack Kirby suka wallafa a ƙarƙashin Kamfanin Marvel Comics. Kamfanin Marvel Studios ne ya ɗauki nauyin shirya shi, yayin da kamfanin Paramount Pictures ya rarraba shi. Iron Man 2 shi ne na biyun Fim ɗin Iron Man (2008), kuma shi ne Fim na uku daga cikin Fina Finan duniyar Marvel mai suna Marvel Cinematic Universe. An yi na ukun Fim ɗin shi ma a 2013. 

 Kamar dai wancan na ɗaya, mafi yawancin Fim ɗin an ɗauke shi ne a California , face wani kafce mai muhimmanci da aka ɗauka a Monaco.
An fara haska Iron Man 2 ne El Capitan Theatre a ranar 26 ga watan Afrilu 2010, sannan aka sake shi a Ƙasar Amurka a ranar 7 ga watan Mayu 2010. Fim ɗin ya samu karɓuwa sosai, sannan ya kawo maƙudan kuɗaɗe kimanin Dala Miliyan $623.9 a Marhalar Kasuwancin Fina Finan duniya baki ɗaya. 


LABARIN FIM ƊIN 

Duniyar yaɗa bayanai ta watsa labarin Tony Stark Yayinda yake bayyanawa duniya cewa shi ne Iron Man. A can kuwa Rasha, Ivan Vanko, wanda Mahaifin sa Anton Vanko bai daɗe da mutuwa ba yaga wannan labari, don haka sai shima ya fara ƙera irin wannan ɗan ƙaramin Janareta irin na Stark. 

Bayan watanni shida da faruwa hakan, yanzu Tony Stark ya zama shahararre kuma Sananne a ko'ina, sannan yana amfani da wannan riga tasa ta ƙarfe wajen kwantar da tarzoma, duk da cewa gwamnati ta buƙaci ya saida wannan riga, Stark yaƙi amincewa. Stark ta ƙara farfaɗo da Taron Stark Expo domin ci gaba daga inda Mahaifinsa ya tsaya. 

A hankali-a-hankali sai Wani ƙarfe da ke taimakawa Stark wajen ci gaba da rayuwa tare da taimakawa wannan ƙaramin Janareta wajen baiwa rigar ƙarfen wuta da ke ƙirjin Stark ya fara yi masa Illa, kuma Stark ya gaza samun makwafin sa. Hakan yasa Stark ya zama mara kula tare da yin duk abinda ransa ke so saboda yana tunani mutuwar sa ta ƙarato. Don haka, sai ya naɗa Mataimakiyar sa ta musamman wato Pepper Potts a matsayin Shugabar Stark Industries, saboda baya son kowa ya san halin da yake ciki. Sannan ya ɗauki Natalie Rushman a matsayin sabuwar Mataimakiyar sa ta musamman. 

Daga nan sai Stark ya shiga gasar tseren motoci a Monaco inda Vanko ya kai masa hari ana tsaka da yin wannan gasa ɗauke da bulalun wutar Lantarki. A nan ne Stark ya saka sabuwar rigar ƙarfen sa Mark V, sai dai dukanta da Vanko yayi ta yi da waɗannan bulalun yasa tayi dameji sosai. Vanko ya bayyana cewa manufarsa ita ce ya nunawa duniya cewa Iron Man fa ba wani Gagara Badau bane kamar yadda ya ke ɗaukar kansa. 

 Jin daɗin wannan abu da Vanko yayi yasa abokin Hamayyar Stark Justin Hammer, yayi ƙaryar cewa Vanko ya mutu, amma a asirce ya sa aka fitar da shi daga magarƙama, sannan ya sashi ya ƙera wasu Sabbin rigunan ƙarfe domin su sha gaban Stark. 

A wani taro wanda Stark ya ɗauka a matsayin bikin Maulidin sa na ƙarshe, sai saka rigar ƙarfen sa ta Mark IV ya fito yana ta shagali har ya shawu. Jin haushin hakan yasa abokin sa, sojan Sama Laftanal Kanal James Rhodes ya saka rigar ƙarfen ta Mark II domin ya dakatar da shi. 

 Faɗan da suka yi a wajen ne ya janyo rarrabuwar kansu, don haka sai Rhodes ya ƙwace wannan rigar ƙarfe ta Mark II ya tafi da ita Hedikwatar Sojin Amurka na sama. Bayan nan sai Nick Fury , Daraktan Ƙungiyar S.H.I.E.L.D. , ya tunkari Tony Stark, harma ya bayyana masa cewa "Rushman" ba kowa bace face Jami'a Natasha Romanoff kuma Mahaifin sa Howard Stark yana ɗaya daga cikin waɗanda suka assasa Ƙungiyar S.H.I.E.L.D. Kuma Fury ya san shi sarai. 

Sunan Fuy ya kuma bayyanawa Stark cewa mahaifinsa da Mahaifin Ivan Vanko tare suka ƙirƙiro wannan ƴar ƙaramar Na'ura, amma da Howard Stark ya gano cewa Vanko so yake yi ya siyar sai ya kore shi, yayin da jami'ai su kuma suka kulle shi a magarƙama. Daga nan sai Fury ya baiwa Stark wasu Tsofaffin kayayyakin Mahaifin sa, a ciki ne ya ga wani ɓoyayyen saƙo da ke bayani kan yadda za'a iya ƙirƙiro wani sabon sinadarin haɗa Na'ura mai Ƙarfin gaske. 

 Da taimakon Na'urar sa J.A.R.V.I.S. , Stark ya samu damar ƙirƙiro wata sabuwar na'ura wacce ya saka ta a cikin wannan ɗan janareta nashi, hakan yasa ya samu lafiya. Can shi kuma Hammer ya sa Vanko ya fito da waɗannan saƙagai da ya ƙera tare da yiwa rigar ƙarfen da Rhodes ya ɗauka ƙarin makamai yana gabatar da su wa jama'a. 

Yayinda ya gano cewa Vanko yana raye, sai ya sanya rigar sa ta Mark VI ya taho wajen domin ya Gargaɗi Rhodes, amma Kasancewar Vanko shi ne ke kula da rigunan daga can inda yake zaune, sai ya baiwa rigar Rhodes tare da waɗannan sauran saƙagai umurnin kashe Iron Man 
Jami'ai dai sun kama Hammer, Yayinda Romanoff da Happy Hogan suka kaiwa Vanko hari a ma'aikatar Hammer industries amm basu ganshi ba ya gudu, sai dai kuma Romanoff ta samu damar mayarwa da Rhodes izinin rigar da yake ciki gare shi. 

 Stark da Rhodes sai suka haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙar Vanko da saƙagan sa. Vanko ya kashe kansa ta hanyar hurawa rigar sa wuta, inda ya mutu tare da sauran saƙagan nasa. 
 
A yayin wani gani, Fury ya sanarwa Stark cewa saboda wuyar sha'ani da yake da shi, Ƙungiyar S.H.I.E.L.D. Zata yi amfani da shi ne kawai a matsayin Mashawarci. Daga nan an baiwa Stark da Rhodes Lambobin yabo saboda irin bajintar da suka nuna. 

A wata fitowa ta ƙarshe, an nuno jami'in Ƙungiyar S.H.I.E.L.D. Phil Coulson yana bada rahoton gano wata ƙatuwar Guduma da suka yi a wata Sahara da ke Mexico. 



JARUMAN FIM ƊIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SA. 



* Robert Downey Jr. - Tony Stark / Iron Man 

* Gwyneth Paltrow - Pepper Potts 

* Don Cheadle - James "Rhodey" Rhodes

* Scarlett Johansson - Natalie Rushman / Natasha Romanoff

* Sam Rockwell - Justin Hammer

* Mickey Rourke - Ivan Vanko:

* Samuel L. Jackson - Nick Fury

 * Jon Favreau - Happy Hogan

* Clark Gregg - Phil Coulson 

* Leslie Bibb - Christine Everhart 

 * John Slattery - Howard Stark

* Garry Shandling - Senator Stern,

* Paul Bettany - J.A.R.V.I.S. 

* Olivia Munn - Chess Roberts 

 *Yevgeni Lazarev - Anton Vanko

 
<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________

●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees 

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees 
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...


Post a Comment (0)