✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
*ABOKIN FIRA *
*Rubutawa:* _Dr. Muhammad Mansur Sokoto_
*DRS NA 013*
*DOGARO GA ALLAH JARI*
A zamanin zamunna aka yi wani mutum mai suna Hatim Al-Asammu. Hatim mutumin kirki ne mai yawan ibada da kankan da kai ga Allah. Yana sha’awar zuwa aikin Hajji sosai amma fa ba shi da guzuri ballai kuma abin da zai bar ma iyalinsa. Watarana sai rayuwarsa ta nuna masa ya yi tawakkali ga Allah ya tafi zuwa aikin Hajji. Ya yi
tanadin abinci na kwana uku sannan ya tara su ya nemi amincewar su.
Dukkan su suka ce ba su yarda ba sai wata yarinya guda daya daga cikin ‘ya’yansa, ita ce ta ce ta amince ya tafi, domin su Allah ya ishe su.
Da farko Hatim ya hakura saboda rashin amincewar iyalansa amma daga baya wannan yarinyar duk ta bi su ta yi masu wa’azi, ta ce da su su bari ya tafi kawai Allah zai ishe su. Hatim ya kama hanya ya shiga cikin ayarin masu zuwa aikin Hajji. Ba su dade da kama hanya ba sai kunama ta harbi jagoran ayarin da suke tafiya da su. Hatim ya zo ya yi masa tawada sai Allah ya ba shi sauki. Daga nan sai shugaban ya ce da shi, daga yau na dauke maka sha’anin guzurinka. Duk in da muka sauka ka zo ka ci abinci tare da ni da iyalaina har mu je mu dawo. Hatim ya yi saduda ga Allah mahalicci, ya ce, ya Allah! Wannan gatan da ka yi min kenan, saura na iyalaina.
Da kwana uku suka cika abincin gidansa ya qare, sai duk mutanen gidan suka fara kokawa suna zargin ‘yarsa da ta ba su shawara akan cewa yanzu ga halin da suka shiga. Sai kawai ta yi murmushi ta tambaye su, shin maigida mai ba da arziki ne ko mai
arziki? Suka ce ma ta shi ma kam mai cin arziki ne. Allah kadai shi ke bada arziki. Sai ta ce, to mai cin arziki ya tafi, amma mai bayar da
arziki yana nan tare da mu. Don haka ku kwantar da hankalinku. Ba a jima ba sai suka ji ana kwankwasar kofar gidansu, suka bude sai aka ce Sarki yana kiran Hatim don wata bukata. Sai suka ce ai Hatim ya tafi
aikin Hajji. Da aka gaya ma Sarki sai ya tausaya ma su. Nan take ya cire wani zobensa mai daraja da tsada ya aika masu. ‘Yan kasuwa kuwa sai suka yi tururuwa a kofar gidan suna cinikin zoben domin su je da
shi kasar waje su sayar su samu riba. Iyalan Hatim suka karbi makudan kudade wadanda ko a mafarki ba su tava ganin irin su ba. Suka ci, suka sha, suka yi sutura har Hatim ya je ya dawo ya tarar da su cikin ni’ima da walwala.
Da Hatim ya dawo suka zauna cikin raha da nishadi ana tadi ya fada ma su alherin Allah da ya gamu da shi, su kuma suka kwashe
nasu labari suka fada ma sa, kawai wannan yarinya ta fashe da kuka.
Suka yi mamakin wannan lamari nata. Suka ce, a lokacin da muke cikin
damuwa kike dariya, yanzu kuma da Allah ya kawo sauki sai kike kuka?
Sai ta ce, duk wannan jin dadi da muka samu tausayi ne na dan Adam ya janyo shi. To, ina kuma ga Allah Mahalicci idan ya ji tausayin mu!
*Darussa:*
▶ Wanda ya dogara ga Allah, Allah ya ishe shi.
▶ Rama alheri ibada ne
📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail.com
Facebook: Jibwis Katsina L.G
WhatsApp: 07062584992, 08038977817, 08034453678, 08036958490.