TAMBAYA TA 3712

*Assalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 3,712:*
=
Awasu masallatan naga idan suna sallar wutri idan aka dago daga ruku'u ana addu'a idan aka xo wajan yiwa Annabi salati da liman da mamu duka sai a amsa da (s a w) ku kuma idan aka karanta ayar karshi ta suratul fathi.Shin yin hakan daidai ne?
=
=
Amsa
=
_Toh dangane da irin wannan qunutin wanda mukeyi a masallatanmu ayau nidai bance waniba, amma ni nan gaskiya nafi jingina irin wannan qunutin zuwaga bidi'a domin kuwa nasan dai ba sunnah bane, a sunnah babu inda zaka samu ance Annabi (s.a.w) a sallar witri yakai minti biyu yana yin qunuti kuma babu inda akace a sallar witri Annabi yana rera addu'a, amma mu yau abun har gasa akeyi kaji ana daukar abun harma a kaset limam yaita faman rera addu'a kusan minti talatin ko awa daya yanata rera addu'a to gaskiya wannan dai kam tabbas ba sunnah bane sedai anema masa muhalli a wani waje domin abun har nema yake yazama neman kudi kawai aita buga kasuna na addu'ar qunuti ana siyarwa wannan ko shakka babu cewa bidi'ane. Hakama yin salati idan ankaranta wannan ayarda ka ambata, shinma wai meyasa basayin sallatin idan an karanta ya Ayyuhan nabiyyu ko Ayyuhal muzammil? Ko Ayyuharrasul duk meyasa basayi anan sedai a wannan ayar ita kadai? Saboda haka wannan babu shakka shima bidi'ane****_
   _Aduba Fatawa Muhimma ta Sheikh Usaimin za'aga karin bayani_
=
=
Allah Yasa mudace
 .
.
*DAGA ZAUREN*

*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔 
Watsaps
08036222795
09031200070
.

22-09-1439
07-06-2018
=
=
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaikai


Post a Comment (0)