HAƘURI DA MIJI

Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596

☏+2348037538596
Sirrinrikemiji@gmail.com
Sirinrikemiji@gmail.com
Islamic medicine center

'Yan'uwa Mata idan muka duba muka gani, zamu gano cewa gaba daya rayuwar aure hakuri ne a cikin ta, Kuma ita kanta kalmar aure, hakuri ne, Dan haka muddin ki Na Neman biyun bukata.

Tofa sai kin hada da hakuri, Saboda idan ki kayi aure, Zaki ga abubuwa da yawa, da ba ki sansu ba, Ko Kuma Baki saba ganin Sa ba, to Amma idan ki kayi hakuri, sai ki ga abin yazo ya wuce kamar ba'ayi ba, Kuma kiyi hakuri Mai yawa sosai.
Domin Zaki fi samun Nasara, idan Ko ki kayi gajen hakuri, to sai dai ma wasu al'amura su kara jagulewa, kiyi hakuri, Kama daga kansa shi Mai gidan, iyayensa,yayyinsa,kanansa,ya'yansa,da duk Wanda ya kamata.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
・HAKURI DA MIJI・

'yar'uwa ya zama miki dole, Don kuwa duk inda mace take,Tana karkashin da namiji,Kuma duk kyanki, kudinki, iliminki,da duk girman kanki, to dole ne ki ajiye gefe, ki bi mijinki, idan Har kin yarda aure bautar ubangiji ne, Kuma tunda mu ikon su ne,kamar yadda Allah yace to dole ne mu bi Abinda suke so, matukar bai sabawa shari'ah ba.

・ BIN SA SAU DA KAFA・

wannan ma ya zama mana dole, tunda Aljanna mu muke nema, Kuma Allah subhanahu wata'ala ya Fadi mana cewa, "Aljanna Ku Tana karkashin kafar su, Kuma ya umarce mu da bin dokar su, in dai Har ba shari'ah ta saba ma ba.

・ HAKURI DA DANGINSA DA KISHIYA・

wannan ma yana da muhimmanci, sannan Kuma duk abindaa zasu miki, kiyi hakuri, ki roki Allah mafita, kar Kuma ki dinga biye masu Ku Na cacan Baki, don kuwa duk Inda kishiya take da dangin miji, sai an yi hakuri zama da su.

・LADABI・

ki dinga yima mijinki ladabi, a duk Inda kike, domin ki nuna ma duniya irin zaman arzikin da ki ke yi dashi,Dan haka kar ki zama Mai gajiyawa ,ki zama mace Mai ladabi a duk Inda kika shiga.

・ BIYAYYA ・

ki kasance Mai biyayya, watau Mai bin duk abindaa mijinki yake so dake, Saboda guje ma fushinsa, da Kuma fushin ubangiji, domin Allah yana cewa, "da zai iya sa'ayi wani sujada, Bayan shi, to da mace ne zai Sa tayiwa mijinta sujada, Don haka sai a Lura,wannan Na da matukar muhimmanci.

・ KI IYA KWANCIYA YANA DA MUHIMMANCI GA RAYUWAR AURE・

wannan shine babbar matsalar yawancin Mata a gidajen aurensu, Don haka a Lura da kyau sosai, duk abindaa kika San mijinki yafi so a wurin kwanciyarki, kiyi kokarin yi masa, Kuma ki kokarin ki San salo-salo Na kwanciya da miji.
   Saboda idan Yau Kinyi wannan kalar, to gobe da irin kalar kwanciyar da Zaki yi masa, Kuma ki dinga kokarin nuna masa rashin gajiyawarki, a lokacin kwanciya, kar ki zama Mai raki,a Kuma dinga amfani da abubuwa kara Ni'ima,Don koda ki Na da kyau, ki kara da wanka.

・ yar'uwa wannan shine jigon zaman auran mu ,Kada mu dinga wasa da shi, Saboda shi namiji yafi so a lokacin da yake tare dake, ki nuna masa duk duniya babu Wanda kike so irin Sa.

・ TSAFTA・

komai naki yar'uwa ya kasance Mai tsafta yadda Mai gida ba zai dinga jin kyamarki da Kayan amfani ki,komai a tsaftace, Zaki dinga barinsa, Kama daga kan jikinki, bayi ( toilet) ,suttura, abincin, kicin, ya'yan ki, dakin kwanciyar Ku da sauransu.

Shima Don Allah karki dinga barinsa da hula a karkace, Ko Kuma da Kaya a yamutse, Kuma kema ki dinga kasancewa Kullum cikin wanka a Rana, ya kasance kina yi Sau Biyu Ko Sau uku musamman ma idan kina al'ada.

・ KI BA MAI-GIDA KULAWA TA MUSAMMAN ・

yar'uwa ki kula, duk Inda namiji yake, to fa so yake ki dinga tarairayarsa kamar jariri,ma'ana ki dinga Lura da shi kamar yadda uwa take Lura da yaronta, ki naji da shi kamar karamin Yaro, kina bashi abincin, a Baki, ki dinga yi masa wanka.

Kada ki zama Yar kyauye a cikin al'umma.

        ・HAKKIN MIJINKI ・

ki kasance Mai kula da hakkin mijinki, idan Kuma ba haka ba, to koda kina masa wadannan abubuwan Dana lissafa, to fa zai dinga Neman matan Banza a waje, Wanda ba'a fata !

Amma kuma laifinki ne, tunda ba kya iya sauke masa bukatarsa, domin sai kin zage dantse ki kasance Mai juriya, tun ba in Allah ya Baki miji Mai yawan bukata ba ( hariji ) to fa kina da aiki sai kin yi hakuri da sannu Zaki saba.

Duk hakkin miji da ya hau kanki, Wanda ki Ka San ya zama dole a gareki, ki sauke masa, to dole ne ki ba shi hakkin Sa, musamman wurin kwanciya, domin idan ya fara Neman Mata a waje, sai kin fi kowa bakin ciki, ga yadda cutuka sukayi yawa, yaje ya dauko ki ya shafe ki sai a kula.

・ BABBAR MATSALA MATAN HAUSAWA・

wata babbar matsala itace, da farkon aure, sai Ka ga soyayya da kulawa ga mai-gida kamar a cinye juna.

Amma kash ! Sai dai daga baya, da zarar mace ta fara samun yara, sai Kuma labari ya sha bamban, a juyawa Mai gida. Baya.

Duk wata kulawa sai ta kau, sai Wanda ya zama dole, ita Kullum hankalin ta yana wurin yaranta.

Kuskure ne babba matan hausawa muke yi, domin Ai komai da muhallinta, yara dai koda yaushe kuna tare, ba Kuma cewa akayi Kada ki kula dasu ba. Amma yayin da mai-gida uban gayya ya dawo, ya dace ya samu kulawar data dace.

Sirrin rike miji
✆ WhatsApp
☏+2348037538596

Don hakan ma da wasu keyi, yana Sa mai-gida ya fita harkaki, ya koma wajen matan banza, Ko Kuma yaje wajen hira, sai kin yi barci ya dawo tunda ya san Ko ya dawo da wuri ,ba wata kulawa zai samu a gunki ba. To meye ribarki da Kai da Kaya fa, duk mallakar wuya ne, ma'ana dake da yaran duk zamansa kuke yi, sai a kula, matukar kina son kina son kaunar mijinki.

Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: ☏+2348037538596


Post a Comment (0)