TARBIYYAR YARA A MUSULUNCI

👩🏼♠ *MUSLIM LADIES WW* ♣👩🏼


*TUESDAY TEAM* 





*TARBIYYA A MUSULUNCI 


Da sunan Allah mai yawan Rahama mai yawan jinkai, bayan haka:Saninku ne iyaye, malaman makaranta, da masu damuwa da gyara da kuma ci gaban al’umma cewa Tarbiyya ita ce tubalin ginin dan adam, ko dai tubalin gini, ko kuma tubalin toka. Duk wata tarbiyya da ba ta musulunci ba, ko wadda ta ci karo da ita, to tubalin gininta na toka ne, ko ba jima, ko ba dade sunanta rushashshiya, tarbiyyar musulunci ita ce daki-bari, kadaura babbar inuwa, kowa ya rabe ta sai ya huta, ballantana wanda ya tashi a cikinta. TO
(1)Me ake nufi da Tarbiyya a Musulunci?
Tarbiyya a Musulunci tana nufin “Gina cikakken Mutum Sannu a hankali; don bin umarnin Allah da na manzonsa, da neman yardar Allah, da samar masa da nagarciyar rayuwa duniya da lahira, bisa tsari irin na musulunci”
(2)Menene hukuncin gina yaro Akan tarbiyyar Musulunci? Gina yaro akan tarbiyyar musulunci wajibi ne, kuma hakki ne daga daga cikin hakkokin yaro akan maifansa (ko walliyansa)Dalilai akan Haka:
1. Daga Kuri’ani: Fadin Allah Ta’ala:
‏( ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﻗﻮﺍ ﺃﻧﻔﺴﻜﻢ ﻭﺃﻫﻠﻴﻜﻢ ﻧﺎﺭﺍ ﻭﻗﻮﺩﻫﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻭﺍﻟﺤﺠﺎﺭﺓ، ﻋﻠﻴﻬﺎ ﻣﻼﺋﻜﺔ ﻏﻼﻅ ﺷﺪﺍﺩ ﻻ ﻳﻌﺼﻮﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺎ ﺃﻣﺮﻫﻢ ﻭﻳﻔﻌﻠﻮﻥ ﻣﺎ ﻳﺆﻣﺮﻭﻥ ‏) ‏( ﺍﻟﺘﺤﺮﻳﻢ : 6 ‏)
Ma’ana: “Ya ku wadanda kuka yi imani, ku dauki matakin kare kanku da iyalinku daga wuta masu tsaronta wasu irin mala’iku masu karfin bala’i da tsananin gaske, ba sa sabawa Allah abin da ya umarce su, kuma duk abin da ya umarce su shi suke aikatawa”.
1. Daga Hadisi; Fadin Annabi (SAW)
“ ﺃﻻ ﻛﻠﻜﻢ ﺭﺍﻉ، ﻭﻛﻠﻜﻢ ﻣﺴﺌﻮﻝ ﻋﻦ ﺭﻋﻴﺘﻪ … ﻭﺍﻟﺮﺟﻞ ﺭﺍﻉ ﻋﻠﻰ ﺃﻫﻞ ﺑﻴﺘﻪ، ﻭﻣﺴﺌﻮﻝ ﻋﻦ ﺭﻋﻴﺘﻪ، ﻭﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﺭﺍﻋﻴﺔ ﻋﻠﻰ ﺑﻴﺖ ﺑﻌﻠﻬﺎ ﻭﻭﻟﺪﻩ، ﻭﻫﻲ ﻣﺴﺌﻮﻝ ﻋﻨﻬﻢ … ” ‏( ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ ‏) Ma’ana: ” Kowa ya saurara ya ji: Dukkaninku masu kiwo ne, kuma kowanneku sai an tambaye shi kiwon da aka ba… namiji makiyayi ne game da mutanen gidansa, kuma sai an tambaye shi akan abin da aka ba shi kiwo, mace ma makiyiya ce a gidan mijinta, da ‘ya’yansa, kuma sai an tambayeta akansu… (Buhari da Muslim)
2. Daga Maganganun Magabata Managarta
Abdullahi dan Umar Allah ya yarda da su ya ce da wani mutum: “Ka ladabtar da danka; don Allah zai tambaye ka a kansa; me ka koya msa, shi kuma za’a tambaye shi irin biyayya da kyautatawar da ya yi maka” “ ﺍﻟﻔﻘﻴﻪ ﻭﺍﻟﻤﺘﻔﻘﻪ ﻟﻠﺨﻄﻴﺐ ﺍﻟﺒﻐﺪﺍﻱ : 1/49 ‏)
1. Daga Hankali:
Ingataccen addinin musulunci ba zai samu baa sai da tarbiyya ta gari ta musulunci.
Yawan alheren da ta kunsa
Ita mafita a yanzu, kamar yadda ta kasance mafita a da.
( 3 )Mecece mabubbugar tarbiyyar Musulunci? Mabubbugar tarbiyyar musulunci, ita mabubbugar muluncin kansa (Alkur’ani da ingatattun hadisan manzon Allah SAW) ‘Yan Rakiya:
Tarihin magabata mantarta
Rubuce rubucen wasu malaman musulunci da suka yi tun shekaru aru-aru
Bincike-bincike, da rubuce- rubucen malaman wannan fage
Lallai a tace duk wani abubuwan da wadannan abubuwa uku suka kunsa da rariyar Alkur’ani da ingatacciyar sunnar Manzon Allah (SAW)
(4)Wadanne ne tuwasun Tarbiyyar Musulunci?
1. Na farko Imani da Allah da rukunansa guda shida, da kuma yankunansa
2. Shari’ar Musulunci
3. Ingataccen ilimi mai amfani
(5)Rukunan Tarbiyyar Musulunci?
1. Mai yin tarbiyya: sharadinsa ya zama ya dace da wannan gagarumin nauyi; don haka lallai ya zama Musulmi, mai hankali, yana da sani da kuma fahimta na yadda zai iya tarbiyyar, mutumin karki, tsayayye mai hikima, da juriya, yana jin nauyin da aka dora masa, kuma a shirye yake da ya dauke shi yadda ya kamata
2. Wanda za’a yi wa tarbiyya: lallai a yi la’akari da shekarunsa, da abin da zai iya yi, da kuma (jinsisa- namiji ko mace)
3. Wurin yin tarbiyya: wadanda suka fi mahimmanci su ne: masallaci, makaranta, iyali, alummar da suke kewaye das hi, da kuma kafafan watsa labarai”
(6)Manufofin Tarbiyyar musulunci da Magaryar tukewartaManufofinta a dunkule:
1. Gina ilimi
2. Gina cikakken musulmi
3. Gina mafificiyar al’umma a bayan kasa
4. Gina wayewa da ci gaba ta musulunci mafificiya
5. Tabbatar da tsira, zaman lafia, da kyakkyawar rayuwa duniya da lahira gad an adam. Babban Abin da take nufin Tabbatarwa : Bautar Allah shi kadai ba tare da abokin tarayya ba, a rayuwar mutum shi kadai, da kuma rayuwarsa da jama’a
(7)Mahimmanci da Fa’idojin Tarbiyyar Musulunci:A dunkule:
1. Yadda shari’a ta ba ta kulawa ta musamman
2. Yadda manyan bayin Allah; Annabawa, sahabbai, magabata manatarta, manyan malamai das auran nagartattun bayin Allah suke ba ta mahimmanci na musamman.
3. Yawan alhairan da take kunshe da su duniya da lahira
Filla-filla:Fa’idojinta Game da mutum shi kansa:
1. Zai san kansa, kuma ya fahimci menene aikinsa a wannan duniya
2. Tabbatar da babbar manufar samar das hi (kadaita Allah da bauta)
3. Bautawa Allah ta hanyar abubuwan alheri da ya koya a cikinta
4. Samun nagartacciyar rayuwa duniya da lahira
5. Samun ladan duk wanda ya yi koyi da shi
6. Zai rika jin cewa shi ba dan rakiyar zuwa duniya ba ne
7. Kowa zai rika son sa yana girmama shi
Fa’idojinta game da mahaifa da ragowar dangi:
8. Biyan hakki, da sauke nauyin da ke kansu
9. Rabauta da biyayyar ‘ya’yan, da kuma kubuta daga saba musu
10. Samun damar iya sarrafa yaran
11. Kima da darajarsu za ta karu, ga kyakkyawan Ambato; saboda wadannan ‘ya’yan na gari masu tarbiyya.
12. Dalili ne na samu dauka da mangarciyar rayuwa a duniyarsu da lahirarsu
13. Ba za su rika jin kunya, da jin cewa da haihuwar wannan yaro gara barinsa ba
14. Samun lada ta fuskoki da dama
Fa’idojinta Game da sauran jama’a:
15. Yaduwar alhairai, da albarkoki, da umarni da kyakkyawan aiki da hani da mummuna
16. Samun zaman lafiya mai dorewa
17. Karanta yawan barna a cikin al’umma
18. Samar da taimakekeniya da soyayya tsakanin jama’a,
19. Samun ayyukan yi fululu, da maganin zaman banza
20. Habaka tattalin arzuki
21. Raya kasa, da tabbatar hilafar dan adam a cikinta yadda ya kamata
22. Fa’idantuwa da ‘ya’yan baiwa
23. Rinuwar zamantakewar al’umma da rini irin na ingatacciyar rayuwa ta musulunci.
Fadakarwa: Duk wani alheri a cikin kowace irin tarbiyya, to akwai irinsa ko wanda ya fi shi a tarbiyyar musulunci.Macece manufar yin wannan fadakarwa?
(8)Illolin rashin gina yaro akan tarbiyyar
Illolin rashin ginda yaro akan tarbiyyar musulunci yawansu ya isa, amma a takaicen takaicewa, duk kishiyoyin alhairan da aka ambata na gina yara akan tarbiyya ta musulunci.
(9)Fagagen Tarbiyyar Musulunci Kasancewar tarbiyyar musulunci tana kokari ne na gina mutum don ya zama kamar yadda Allah da manzonsa ta kowace fuska suke sonsa, to kowane fage da zai ba da gudunmawa wurin wannan gine, fage ne daga fagagen tarbiyyar musulunci. Kamar 1. Bangaren imani2. Zuciya da ruhi3. Bautar Allah4. Kyawawan dabi’u5.
Ilimi6. Hankali7. Jiki8.
Zamantakewa9. Sana’a10.
Jagoranci. Dss
(10)Tsakanin Tarbiyyar musulunci da watarta:Ita Tarbiyyar Musulunci
1. Daga Allah take, cike fal da annuri na shari’ar musulunci
2. Ita ce tarbiyyar Annabawa da nagartattun bayi ga ‘ya’yansu
3. Ta dace da “fidrar’ dan adam
4. Ba kuskure a cikinta; don asalin da aka gina ta akai shi ma ba kuskure a ciki
5. Tana da tabbas da izinin Allah
6. Dole ce akan kowane musulmi da musulma su yi wa ‘ya’yansu
7. Ita a karan kanta ibada ce
8. Daukaka da darajar manufofinta da magaryar tukewarta
9. Tana dacewa da kowane lokaci, zamani, wuri, da kuma yanayi
10. Ba ta tsayawa (tun kafin haihuwar mutum, har karshen rayuwarsa
11. Ta kunshi kowane sako na rayuwa, da kowane bangare da sashi na mutum
12. Komai tana ba shi hakkinsa yadda ya dace da shi
13. Sashinta yana taimakawa shashi
14. Zai yiwu a aiwatar da ita cikin sauki
15. Ta hada tsakanin dad a yanzu
16. Ba tufka da warwara a cikinta
17. A bayyane take, ba ta da wahalar fahimta
18. Tana bin komai daki-daki sannu a hankali
19. Tarbiyya ce da take nusatar da baiwa da karfin da yake cikinsa wurin da ya dace.
20. Ita ce kadai za ta iya samar da irin mutumin da ya cancanci halifancin Allah a ban kasa. dss
Ta haka za ki san tarbiyyar musulunci warin masaki ce a ba ta da abokin burmi.
(11)Salo daban daban na Tarbiyyar Musulunci Daga ciki akwai:
1. Addu’a
2. Mace ta gari
3. Kyautatawa
4. Sa ido
5. Bin abu sannu a hankali
6. Koyarwa (a ilmance)
7. Koyarwa a aikace
8. Wasiyya
9. Wa’azi
10. Buga misalai
11. Amfani da hanyoyin kara fito da bayani
12. Ba da kyakkyawan misali
13. Tattaunawa
14. Zaman tattaunawa tsakanin iyali
15. Labari
16. Abokantakar yaro
17. Samarda “dan sandan ciki”
18. Ciyar da yara daga halal
19. Kwadaitarwa da tsoratarwa
20. Sakawa da alheri da ukuba.
(12)Abubuwa Masu Tasiri a Tarbiyya
1. Kaddara
2. Addini
3. Wurin da mutum yake raye
4. Mutanen da mutum yake cikinsu
5. Gado (shi kuma hawa uku)
Gadon abubuwan da suka shafi halitta
Abubuwan da suka shafi hankali da tunani
Gadon abubuwan da suka shafi halaye da dabi’u
(13)Mahimman abubuwan da za su taimaka mana wurin gina ‘ya’yanmu akan Tarbiyyar musulunci 1. Dogaro da Allah da neman taimakonsa2.
Ilimi3. Himma da tashi tsaye4.
Fahimtar dabi’u da bambamcen da ke tsakanin ‘ya’ya5. Bin hanyoyin da suka dace don tarbiyyantarsu. ﺭﺑﻨﺎ ﻫﺐ ﻟﻨﺎ ﻣﻦ ﺃﺯﻭﺍﺟﻨﺎ ﻭﺫﺭﻳﺎﺗﻨﺎ ﻗﺮﺓ ﺃﻋﻴﻦ ﻭﺍﺟﻌﻠﻨﺎ ﻟﻠﻤﺘﻘﻴﻦ ﺇﻣﺎﻣﺎ ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻧﺒﻴﻨﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ ‏( 24/10/1428 ‏) ﺍﻟﻤﻮﺍﻓﻖ ‏( 4/11/2007 ‏)
Muhammad Nur Abdullahi






*SHDG*
_(SMASHER,HUBBEEY,DIDEEYLOV & GENTLE)_



Post a Comment (0)