TARIHIN WALI ƊAN MASANI

TARIHIN WALI DAN MASANI
Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
Sunan sa na yanka shine Abduljalil, amma anyi saɓani akan cikakken sunansa da kuma asalinsa.
A wani aulin ance shine Muhammadu ɗan Abdullahi ɗan Nuhu, babar-bare ga asali, bakatsine ga haihuwa. Shine shehun malami mai yawan sani, masanin furu'a, masanin nahawu, masanin lugga da balaga, uban Abdullahi.
Amma a wani aulin ance mahaifinsa Mallam Masani mutumin kasar Masar ne, larabawan futa-turo ne suka karɓo shi daga hannun mahaifinsa wanda yake wani babban malami ne acan masar ɗin suka zo dashi katsina. Su waɗannan larabawa, sun kasance idan zasu zo kasar Hausa fatauci daga masar, sai uban ɗan masani ya basu sa'a.
To shi wannan yaro ɗa ga Mallam masani shine ya shahara kwarai a katsina, kan sha'anin malanta har ya zamo mai ba sarkin katsina sa'a idan zai tafi yaki.
Ance wali ɗan Masani ya karantar da mutane ilimi sosai a Birnin katsina, ya rayu a karni na goma sha shidda, shine kuma akace ya raini shahararren masani Wali ɗan Marina wanda har daga baya akace jayayya ta ilimi ta taɓa wanzuwa a tsakaninsu.
Wali ɗan Masani ya rubuta wakokin Hausa da dama, dayawansu sun ɓace saboda rashin taskancewa tun tsawon zamani daya shuɗe, amma wadda aka samu a yanzu kuma ake kyautata zaton shiya rubutata itace wakar 'Yakin Badar', wadda akace a baya ta shahara a kano, inda manya da yara ke rerawa kwararo-kwararo.
Ita wakar tana magana ne akan yakin Badar wanda yake ɗaya daga yakokin da Manzon Allah (s.a.w) sukayi da sahabbansa domin tabbatuwar wannan addinin na musulunci.
Don haka, wakar tana bayyana yadda akayi gwagwarmaya da kafiran makkah a karkashin jagorancin Abu Safiyan da yadda musulmai 313 dake kafa, da guda 2 mahaya dawakai, da guda 70 mahaya rakuma sukayi nasara akan kafirai sama da 1000.
Har ila yau, Ita wakar tana sharhi ne akan abubuwan da suka faru game da yakin Badar ɗin. Ko da yake wasu abubuwan da aka ambata a yakin uhudu ne akayisu.
Wakar duka-dukanta baitoci 48 ne, 11 na farko suna nuna yabo ne ga Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gareshi wanda yazo da littafin Alkurani mai girma.
Sai kuma baitocin da suka biyo baya masu nuni da yadda rashin jituwa ya soma biyo baya tsakanin musulmai da kafiran makkah da yadda Abu Jahali ya aiki Siraka filin daga a inda ya tarar da mu'ujuzozin Annabi Muhammad (s.a.w.)
Ga kaɗan daga wannan wakar:-
1. Bismillahi Sunane na Allah Ta'ala,
Zani yabon Rasulullah, macecin mu bayi.
2. Nai haramar yabo da yawa, na duba da zurfi,
Gulbin mai ruwa tari, fito sai da jirgi.
3. Zani yabonka Gamzaki da kazo da haske,
Hasken naka nada yawa yana shafe rana.
11. Mutan Makkah sun murna da saukar fiyayye,
Amma sai da anka kara, takubba da masu.
12. Wani wawa Abu jahil dake basu karya,
Yace koway je wurin wan'in shina bashi 'yatai.
13. Anga Siraka yai gama da bai kai isa ba,
Ya kai goɗiya ta kafe wurin babu ramu.
15. Yai kara yai kuwwa yana "Ya fiyayye"
Annabi yaji kukanai, "kaje, babu komai"

Post a Comment (0)