TUN KAFIN AURE 35

TUN KAFIN AURE💐35



Washegari wayar Junaid ce ta tasheta daga bacci da asuba. Ko da ta dau wayar sai taga an rubuta J dear. Lallaima wato har wani saving sunansa yayi a haka. Ta daga cikin muryar bacci tace waye ne waya da asussuba kamar me karbar bashi. Murmushi yayi yana shafa kansa ai zaki biya bashi ne Hafsi Hafsi amma not now. Yanzu dai ya kika kwana? Ya jikin? Da sauki  ta ams itama murmushin take. Wani son Junaid takeji yana ratsa ta. Amma babu yadda zatayi yanzu sai sun kawar da su Talatu daga gidan.

Karfe 9 na safe aka sanar da su Mommy zuwan baban Talatu Mal Jibo da kannensa biyu. Senator ta tayar daga baccin da sai bayan asuba ya sami runtsawa saboda tunani. Doguwar riga ya saka ya mike. Ki aika a kira min Junaid tun jiya ban sanar dashi maganar auren ba saboda kada ya daga min hankali. Shi ya jawo matsalar nan so he has to deal with it. Mommy tace amma yallabai baka ganin kara dulmiya shi zamuyi kaga baya sonta kuma basu da kamanin mutumci. Hannu ya daga ya dakatar da ita...haba Salma duk shi baiyi tunanin haka ba sanda yake bin duk macen da ya gani. Ai duk rayuwar da mutum yayi kafin aure indai ba Allah Ya kare ba sai kiga tana bibiyarsa. Ko kadan ita dai abin baiyi mata dadi ba amma dole tayiwa mijinta biyayya. Haka suka sauka kasa ya fita wani falo ya tarar dasu a zaune sun kusa cinye duk abinda aka kawo musu  na tarar baki. Bayan doguwar muhawara Senator Rufai wanda rashin son tonon asiri yasa babu wanda ya iya sanarwa halin da ake ciki cikin abokansa da yan uwa ya tsayar da magana akan zaa daura auren Junaid da Talatu nan da sati biyu. Mal Jibon karya yace ranka ya dade ni dai gara a daura auren nan asabar mai zuwa saboda kada ya lallaba ya sake banka mata wani cikin. Wata irin tsawa Senator Rufai ya daka masa ya mike tsaye...kada ka dauki saukin kaina a matsayin shashanci mana. Ina binku ne a hankali kawai don in tayaku sayawa yarku mutumci. Idan kuka shige gonar da ba taku ba wallahi ina da karfin da zansa duk a neme ku a rasa. Duk abinda nake yi saboda girman Allah nake yi so be careful , be very careful.  Yana gama magana ya fita Tanimu yace kai baaba kaji yadda hantar cikina ke kadawa kuwa. Baaba yace ai sai da nayi dana sanin magana ma. Wallahi idan Rosie bata biyamu da kyau ba jikinta ne zai fada mata. Kaga yadda yake muzurai kuwa. GG dake gefe yace ai ni na fiku tsurewa yadda yace zai batar damu gani nake kamar ya gama gane mu ma.

Baffa ya dauki wayarsa dake faman ringing tun yana sallar walha ya duba sai yaya sirikinsa ne. Bayan sun gama gaisawa Senator ya labarta masa dukkan abinda ke faruwa a gidan nasa. Mal Aminu dai yau ya rasa bakin magana saboda takaici yanzu irin gidan da Hafsan sa ta tare kenan. Senator ya cigaba da bashi hakuri da neman shawara. Mal Aminu duk yadda ransa ke kuna yace dole ayi abinda ya dace don a rufa asiri kuma shi yanzu kullum Junaid yana kiransa kuma ya yarda da irin shiryuwar da yake ji tare dashi. Haka suka yi ta shawara Senator yace idan ba damuwa ko zaku iya zuwa zuwa Jumaa kai da Alh Bashir saboda bani da wanda zan iya tonawa sirrina. Lallai rayuwa babu yadda bata zuwa ga bawa. Allah Ya kara rufa mana asiri. Daga nan Senator ya nemi dansa ya sanar dashi shawarar daya yanke. Junaid mikewa yayi cikin rudani yana daga murya...wallahi wallahi Alhaji bazan auri Tilly ba, karuwa ce fa.




Batul Mamman💖

Post a Comment (0)