ABUBUWAN DA MATA ZA SU SHA DON DAUWAMAMMIYAR NI’IMA




ABUBUWAN DA MATA ZA SU SHA DON DAUWAMAMMIYAR NI’IMA

Sirrin mallakar miji
☏+2347066620951

To, Uwargida wannan satin shafin namu zai dan canja
salo duk da wadancan abubuwan gyaran jikin ma ko
rabin-rabi ba mu gama kawo su ba, amman za mu dan
waiwayi wani bangaren, inyaso wani lokacin kuma sai mu
dawo bangaren gyaran fata.

Da yawa mata su na yawan kawo min korafin daukewar
ni’ima a jikinsu, wato bushewar gaba, da daukewar
sha’awa yayin jima’I, wanda yawancinsu su kan ce da ba
haka su ke ba;
lokaci guda su ka ji sun kasance a hakan.

Yawancin mata rashin kula da kai da rashin sanin irin
abubuwan da yakamata su dinga ci domin samun
dauwamammiyar ni’ima a jikinsu don samun gamsuwar
kawunansu da jin dadin mazajen shi ke haifar mu su
da.matsalar daukewar ni’ima da kuma daukewar
sha’awa.

Wasu kuma su kan kamu da ‘toilet infection’ ne saboda
rashin tsaftar bandaki, wasu ba sa taba kula da gyaran
bandakinsu, wasu kuma su kan dauka a bandakin
hadaka..

Abubuwan da ya kamata mu mata mu dinga ci, domin
karuwar ni’imar jikinmu da da jin dadin mazajenmu:-
A na son mace ta dinga cin daya ko biyu daga cikin
wadannan abubuwan kullum a rana;

a cikinsu akwai abubuwa masu saukin kudi wadanda duk
rashin hadi ki ko rashin halin maigida, zai iya siya, kuma
wadannan abubuwa su na kara lafiya da kuzari a jikkunan
aluUmma kuma garkuwa ne ga kamuwa da wasu
cutukan. Haka kuma ya na karawa mata ni”ima da jin
dadi wajen mazajensu.

Wadannan ba wasu abubuwa ba ne illa:

☏+2347066620951

Kankana, Ayaba ,Gwanda, Goba, Lemo, Tumatir, Rake,
Aya, Kwakwa, Dafaffiyar gyada, Zuma, Nono, Madara, Madarar Shanu, Gurji, Dabino, Chukwi, Zogale, Ruman, Inibi, Tuffa, Zaitun.

Misali yau idan ki ka sami jikakkiyar ayarki ki ka ci, gobe
ki sami raken ki ki sha, jibi ki sami nunannun tumatur
dinki manya guda biyu ko uku ki shanye, gata ki sha
kankana ko nono. Ki dinga cin abu kala biyu a cikinsu, to
wallahi Ina tabbatar mi ki banda ni’ima, hatta fatar jikinki
sai ta murje ta goge ta yi kyau.

Sannan wasu daga cikin su a na shan ruwansu domin
ni’ima ta musamman ko a sarrafa wani abin da ruwan, don samun dauwamamman jin dadin ma’aurata, kamar:

Ruwan kwakwa
Ruwan zam zam
Ruwan kankana
Ruwan tumatir
Ruwan zogale
Ruwan ruman
Ruwan ayaba
Ruwan guaba
Ruwan dabino
Ruwan rake
Inibi
Ruwan kwai
Ruwan kaninfari
Ruwan itacen baure
Ruwan sassaken gamji
Ruwan madarar shanu
Ruwan zaitun
Ruwan tuffa


Shan ko wane ruwa daga cikin wadannan ya na
saukarwa da mace ni’ima mai kyau, mai kauri da yauki
irin wacce maza su ke so, kuma ko wanne ruwa akwai
yadda a ke sarrafa shi da mahadan da za su sa mai gida
sambatun dadi.

Ga kadan daga cikin yadda a ke sarrafa wasu ruwan daga
ciki:

1) Ruwan Kankana, Ayaba Manya Uku, Kankana Kwata da
Tuffa: Ki hada ki markada ki zuba madarar ruwa
gwangwani daya, zuma yadda ki ke so, ki sa kankara ya
yi sanyi, ku sha kamar juice ke da maigida. Ya na karin
ni’ima da kaurin maniyyi.

2) Ruwan Tumatir: Ki markada tumatir biyu, ki zuba
ruwan a cikin kwai uku, ki sa magi da albasa ki soya ya yi
ruwa-ruwa ki ci. Shi ma ya na saukar da ni’ima sosai da
saka jin dadin auratayya, sannan hakan ya na saka
gogewar fata.

3) Ruwan Kwakwa: Ki fasa kwakwarki ki tsiyaye ruwan
cikin kwakwar, sannan ki bare bakin bayan kwakwar ki
goga kwakwar da ‘greater’, sannan ki markada a
‘blander’, sai ki zuba ruwa a kan markadaddiyar kwakwar
ki tace ruwan ki fidda dusar.

Da ma kin bare dabinonki cikin gwangwanin madarar
ruwa daya. Ki jika dabinon ya yi laushi sai ki markada ya
yi laushi sosai, sai ki zuba a kan ruwan kwakwar, sannan
ki zuba ruwan da ki ka fasa kwakwar ya zubo a ciki. Ki
zuba zuma da garin madara cokali uku a ciki, ki juya
sosai. Ki sa a firij ya yi sanyi ko ki saka kankara. Idan ba
ki son sanyi sai ki sha a haka. Ki yini ki na sha; kar ki
barshi ya kwana. Hmmm zumdum! Ba zan ce komai ba,
sai kin gwada kawai, uwargida za ki ban labari.

4) Ruwan Zogale: Amfanin ruwan zokage ba zai lissafu
ba a maganin cututtukan da ya ke yi ma na a jikinmu.
Amma zan yi bayanin amfaninsa a bangaren karin ni’ima
a jikkunanmu ne kawai.

A- ki tsinke zogale ki wanke ki tafasa sosai ki tace ruwan
zogalen ki zuba kaninfari da citta ki tafasa. Sai ki sauke ki
dinga kurba da zafinsa kamar shayi. Ya na gyara jiki ya
saukar da ni’ima sosai. Ya na karawa mace kuzari a
jikinta sosai, sannan ya na karawa mace juriya wajen
saduwa.

B- Ki tsinke zogale ki wanke ki markada ganyen a
‘blander’ ko ki mutstsika da hannunki ki kara ruwa a kai
ki tace ki matse dusar. Ki zuba madarar ruwa gwangwani
daya a cikin ruwan zogale cikin jug daya. Ki sa zuma ta ji
sosai. Ki juya ya hadu ki dinga sha. Gaskiya ba shi da
dadin sha, sai dai akwai shi da aiki; ni’ima lutsutsu!
Domin duk bushewar gabanki da rashin ni’imarki sai
ni’ima ta zo, kuma ya na sa jin dadi sosai.

C- A nan ganyen zogalen da ki ka tafasa sai ki zuba a
faranti ki yanka tumatir manya guda uku ,ki yanka gurji
(cocumber) babba guda daya, ki saka magi, gishiri
kadan, mai kadan. Kar ki sa kulikuli. Zai yi miki maganin
basir da cikowar gaba. Zai kara mi ki ni’ima da dandano
gurin maigida.

5) Ruwan Dabino: Ki bare dabinonki rabin kwano, ki jika
da ruwa. Idan ya yi luguf sai ki markada a ‘blander’. Za ki
gan shi da kauri kirtif. Sai ki ajiye a firinji; duk sanda za ki
sha sai ki debi cokali biyu ki zuba a kofi, ki juye madarar
ruwa gwangwani daya, ki sa garin minannas karamin
cokali ki juya sosai. Idan ya yi kauri da yawa ki kara ruwa
kadan ki kuma juyawa, ki shanye duka. Bayan awa uku da
shan ki za ki tsinci kanki cikin wani yanayi na lutsutsu da
son kasancewa da maigidanki. Za ki ji dadin da ki ka
dade ba ki ji ba. Maigida kuwa zai gamsu da ke sosai.

6) Ruwan Rake: Ki bare rake ki yanka gutsu-gutsu ki daka
a turmi ko ki markada a ‘blander’ ki na yi ki na kara ruwa
a dusar raken ki na matsewa. Idan kin sami ruwan rake
kamar cikin jog daya. Sai ki sami ruwan tafasashshen
baure jog daya. Sai ruwan jangari da jangagai da alewar
mata da a ka tafasa su guri guda a ka tace su ma jog
daya. Sai ki zuba wannan ruwayen naki a wuta ki zuba
zuma kofi daya, ki yi ta dafawa har sai ruwan ya kone ya
zama kamar cikin jug daya, sai ki sauke. Amma za ki sa
kaninfari da kayan kamshi a dahuwar. Idan ya huce sai ki
juye a abu mai kyau. Ba zai lalalce ba. Kullum ki sha
ludayi daya. Zai ratsa jikinki ki sami dauwamammiyar
ni’ima. Mai gida zai dinga jin dadinki ya na gamsuwa da
ke sosai. Tsimin rake kenan.

☏+2347066620951
Jama’a ku fahimce ni; na yi wannan rubutu ba ta wata
manufa ba; burina na ceto matan da ke cikin halin rashin
sanin kansu. Don haka ba na so ya ba wa wasunku
damar yi min wani kallo, musamman ma maza, ko su yi
ta kira na su na cewa za su yi min tambaya a kai. Ku sani
filin nan an kirkire shi ne, don ’yan uwa mata. Don haka
mata ne kawai su ke da damar yimin mssg su yi
tambaya, ehe! Wasalam!


*_​​DAGA ZAUREN 👇🏻​​_*


*​🌳Sirrin°Mallakar°miji🌴​*
*​✆ Wɧat ﻯApp​*
*​❀✎•••+2347066620951​*


*─▽••──▽••──▽••──▽••──▽••─​*
*─▽••──▽••──▽••──▽••──▽••─​*

☆ミ+2347066620951

​In kina so kiyi register a group din *Sirrn•Mallakar•Miji​* sai ki ne me Mu ta wannan 👇🏾number A whatsApp​          
    ☎ ​+2347066620951​ ↙
 ```*📚​​Sirrin°mallakar°miji📚*``` 

*─▽••──▽••──▽••──▽••──▽••─*
✆ Wɧat ﻯApp
☆ミ +2347066620951
 *Banda ​ ~kira~ 📵​ Dan Allah👏🏻​* 
*─▽••──▽••──▽••──▽••──▽••─*
*👯‍♀ Group din 👯‍♀👯‍♀👯‍♀👯‍♀👯‍♀*
*👯‍♀ Mata Zallah • 👯‍♀👯‍♀* 
*👯‍♀ Banda ~Maza~ 😜*
Post a Comment (0)