ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA (KASHI NA UKU) DAGA SADIQ TUKUR GWARZO




ASALIN FARA RUBUTUN BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA
(KASHI NA UKU)
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
Bunkasar Harshen Hausa
Abisa fahimta irin tamu, yaren hausa gamayya ce ta haifar dashi. Littafin Babil mai tsarki ya faɗi cewar shekaru da dama da suka gabata (misalin shekaru dubu takwas da suka gabata), mutanen duniya da harshe ɗaya kurum suke amfani, sai daga baya yaruka suka rinka samuwa ta yadda zuwa yanzu akwai kimanin yaruka dubu bakwai a faɗin duniyar nan. Ina tsammanin Littafin Alqur'ani maigirma bai yi magana irin wannan ba, amma duk da haka maganar data fito daga Babil na iya tabbatuwa a kimiyance tunda dai munsan cewa Allah Ubangiji ne ya saukar da littattafan duka guda biyu.
Samuwar harshen hausa na iya zamowa daga haɗakar kalmomi na waɗansu yaruka mabanbanta. Ma'ana, tana iya kasancewa karo-karon kalmomi daga yaruka daban-daban ne ya haɗu ya samar da yaren hausa kachokan ɗinsa, hakan kuwa na iya faruwa ne idan muka kalli hausawan su kansu zamuga cewa kabilu ne da dama suka cakuɗu suka rikiɗe tare da zamowa hausawa lokaci mai tsawo daya shuɗe.
Misali, bari mu ɗauki manyan garuruwan hausa mu ɗanyi karamin nazari akansu:-
A tarihin kafuwar kano, ance wani mai suna Dala ne ya fara zama akan wani dutse wanda daga bisani aka sanya masa suna dala. A hasashe, hakan ta faru tun a wajajen karni na bakwai. Littafin tarihin kano da ake kira 'Kano Chronicle' (Tarih baladil Laziy Musamma Kano) ya ruwaito kwatankwacin haka, har kuma ya rubuta a shafin farko "La na'alamu k'abilatihi'. Ma'ana, bamu san kabilar shi wannan Dala ɗinba wanda hakan ke nuna cewar sam-sam Dala ba Bahaushe bane. Hakan kuma na nuna cewa asalin kalmar Dala itama ba hausa bace.
Daga lokacin Dala da lokacin rayuwar zuriyarsa, kalmomi mabanbanta sun shigo cikin harshen hausa. Kamar misalin Girgije (Sunan Kakan Barbushe, kalmar kuma da hausawa ke nufin Hadari), Magaji daga Magajin Dala, da makamantansu.
Daga bisani akace Bagauda yazo Maɗatai ta kano ya kama noma. A bisa mafi rinjayen magana, Bagauda Bamaguje ne. Shima watakila Sunan kabilar sa Maguzawa, ko kuma sunan kabilar tasa ya zama yana da wani lakabi na zahiri na daban, amma an sakaya shine da sunan 'Maguzanci', kalmar da a hausa ake nufin mutanen da basu da addini. Daga wajen su kalmomi irinsu Noma, Guguwa, Hadari, Shekara da Shekarau suka fito. Waɗannan jinsi na maguzawa kuma, sune suka kafa kusan kafatanin tsoffin biranen dake kasar kano ayau, misalin Rano, Gaya, Gwarzo, Kiru da wasunsu. Koda yake, duk da muna da karancin fahimta akan jinsin Maguzawa, amma da alama suna iya zamowa kabilu mararraba tamkar yadda jinsin fulani suke ayau.
Sannan dai, a littafin 'Kano ta dabo', marubuci marigayi Alh Abubakar Dokaji (Allah ya gafarta masa amin) ya faɗi cewa a tsohuwar kano akwai kabilun Gazargawa dake zaune a jakara, Zadawa dake tsakanin jakara zuwa sontolo, Fangon dake tsakanin Sontolo da Burkum, Zaura dake tsakankanin Bompai da wasai, Dundunzuru dake tsakanin watari zuwa Ɗdutsen karya, Shiriya dake tsakanin sontolo zuwa Shinke, Sheme dake tsakanin Damargu zuwa kazaure, Tokarawa dake tsakanin karmami zuwa Ringim da wasunsu. Dukkan mafi rinjayen waɗannan kabilu sun haɗe guri ɗaya lokaci mai tsawo daya gabata, har takai yaren hausa kurum akeyi a kano, kuma a duk duniya idan kace kano, za'ace maka birnin Hausawa ne.
Mu kalli Katsina. Suma ance Durɓawa ne suka kafa garin tun a karni na sha uku. Wamban Katsina Alhaji Abba Khali ya taɓa faɗa a wata firar sa da gidan radiyon (RFi: Radio france international) cewa waɗanda suka kafa garin katsina sunzo ne daga wani gari mai suna Mani. Garin mani yana nan har yanzu a jihar katsina, to amma ana tsammanin mutanen garin Mani na farko ba hausawa bane, wata kabila ce wadda ta taso daga yankin Mali.
Haka abin yake a zaria. Littafin 'History of Zaria (1350-1902)' na Yakub Hassan ya nuna cewa asalin Birnin Zazzau mutane ne daga Kufena, kuchichchiri, Turanku, Madarkachi, Kargi da Tukur-Tukur sukayi haɗaka wajen kafashi.
Domin kuwa, duk kan waɗancan garuruwa tsoffin gurare ne da binciken akiyoloji ya tabbatar da wanzuwar mutane tun da jimawa kafin kafuwar zazzau a karni na sha uku, kuma akasari waɗancan mutanen kabilu ne mabanbanta misalin Kadarawa, da wasunsu, har dai daga bisani aka samu cewa kabilar Torankawa suka zo suka kwace iko da wurin. A yanzu kuma garin ya rikiɗe izuwa kasar hausa, masarautar su da al'adunsu duk na hausa ne. Suma dai Watakila jikokin waɗancan kabilun ne kusan zamu iyacewa suka ajiye yarukansu da al'adunsu tare da zamowa hausawa zuryan.
Itama kasar Damagaram (Zinder) wadda a yanzu da kasar hausa ake kiranta. Asalinta ance wani mafarauci ne mai suna Zundurma ya fara zama a wurin. Sannu a hankali Barnawa suka rinka kwararowa yankin saboda ance wajen ya kasance turbar kasuwanci ce, har kuma daga bisani aka samu karin kabilu mabanbanta waɗanda mafi akasari yanzu duk sun rikiɗe sun koma hausawa.
A hakika a cikin hausa ta yau akwai Barnawa da yawa. Yawan nasu ma bazai lissafu ba. Tunda an samu cewa akwai garuruwa da dama waɗanda bare-bari ne suka kafasu. yawa-yawan waɗancan bare-bari, wani dalilai ne ya taso dasu izuwa kasashen hausa, sai gashi kuma bayan zamani mai tsawo ya shuɗe, jikokin su duk sun zama hausawa, jinin jikinsu kaɗai ne na kanuri (duk da shima ya gauraya dana sauran kabilu) amma harshe da al'ada duk dana hausa suke amfani.
Irin waɗannan misalan ne a Daura, Zamfara, Gobir, Maraɗi da mafi yawan jihohin hausawa. Abin nema dai anan shine yaya akayi harshen hausa ya haɗiye yarukan waɗancan kabilu ta yadda a yanzu suka zama tarihi?
To, abisa ga falsafar marubucin tarihi Ibn Khaldun, ana gane abinda ya faru a baya ta hanyar fahimtar abinda ke faruwa a yanzu, sannan za'a iya gane menene zai faru anan gaba idan akayi duba na tsanaki bisa abubuwan dake faruwa a yanzu.
A saboda haka, nafi ganin abubuwa biyu ne manya wajen zamowa silar bunkasar harshen hausa.
Na farkon su shine rashin kyamar bakon (mutum) abu matukar bai zo da abu saɓanin fahimtar suba.
Na biyun su kuwa shine karɓar bako tare da maida shi ɗangida.
Ga abinda aka rubuta a Littafin 'waka a bakin mai ita' dangane da wannan:-
"Wani abin sha'awa shine, harshen hausa harshe ne mai iya karɓar kowanne irin salo da harshen larabci yazo dashi ya zauna daram-dam kamar anan aka halicce shi.."
Da yake littafin yana magana ne akan kamanceceniyar ma'aunan gwajin waka na larabci da namu na hausa, amma muna iya cewa wannan abin ba akan larabci da waka kaɗai ya tsaya ba. Domin idan za'a yi bincike za'a samu cewa harshen hausa yayi aro na kalmomi da hikimai daga yaruka mabanbanta, kuma sannu a hankali ya mayar da abinda ya aro ɗin ya zauna daram kamar daman tun can asali akwai shi.
A wani gagarumin bincike da akayi, Dr Aliyu Abubakar ya rubuta a littafinsa 'Al-thakafatul Arabiyya fi Nigeria' cewa yawan kalmomin larabci a cikin hausa sun kai kumusi. (kashi ɗaya bisa biyar, kamar ace aduk kalma biyar ta hausa, ɗaya daga larabci aka aro ta, to idan kuwa da za'a auna da sauran yaruka, da watakila aga wai ina ainihin hausar take?).
Ko kuma idan zamuyi hasashe, zamu iya duba cewar larabawa sun fara shigowa kasashen hausawa don mu'amala tun a wuraren karni na goma sha uku ne. Don haka muna iya cewa a iya shekaru ɗari bakwai na mu'amala tsakanin hausawa da larabawa (1300-2000), tarin kalmomin da hausa ta ara yakai 'khumusi'. Kenan, idan muka ɗauki wancan ma'aunin auna lamurori da Ibn Khaldun ya bamu zamu iyacewa daga karni na bakwai zuwa na goma sha uku (700-1300, wasu shekaru ɗari bakwai baya kenan), hausa ta ari wasu kalmomin da adadinsu zai iya riskar khumusi ko wani abu dake sama ko kasa da haka daga wasu harsunan waɗanda zuwa yanzu zaiyi wuya mu gane su..
A baya-bayan nan kuma,shigowar turawa zuryan da fara mu'amalar su a kasar hausa ta soma ne daga shekarar 1900. Zuwa yanzu Muna iya cewa yaren ingilishi ya shiga cikin hausa a iya waɗannan shekaru ɗari biyun da adadin kalmomi masu tarin yawa, tayadda zaka samu matasan mu zaiyi wuya suyi sa'a guda suna fira ba tare da sunyi amfani da kalmar aro ta ingilishi ba. Watakila kamar haka hausa ta soma a sauran yarukan, kuma muna iya cewa nan da shekaru ɗari biyar masu zuwa tsoffin kalmomin hausa da yawa na iya dulmiyewa tunda an samu musayarsu dana ingilishi.
Don haka, muna iya ganin cewa ɗaukacin kabilun dake tare da hausawa tun tale-tale sun rinka aron kalmomin hausa ne, yayin da suma kuma hausawa na dauri suka rinka aro kalmomi daga garesu, a haka har lokaci yayi da hausa ta haɗiye yawa-yawan yarukan, ta kuma mayarda yawa-yawan kalmomin aro mallakinta.
Watakila kuma saukin hausa wajen yarawa da arowar kalmomi yasa makwabtan hausawa suka fara koyon hausa a hankali-a hankali lokaci mai tsawo daya shuɗe har takai jallin da harshen hausa ya zame musu ɗan tsakiya wajen saduwa tsakanin kabilun dake da banbancin yare da juna.
Zuwa yanzu dai akwai kabilun da sun ma mance da ainihin harshensu, da hausa kurum suke amfani, yayin da wasu kuma suka rike nasu harshen suka kuma riki harshen hausa tayadda idan basuyi hankali ba, shekaru da dama masu zuwa harshen hausa zai haɗiye harshen nasu kamar yadda yayiwa waɗancan yaruka na baya.
Wannan a takaice na iya zama wani abin kamawa dangane da bunkasar harshen hausa a wannan yanki namu..
Zan tsaya anan.. Godiya da yabo ya tabbata ga Allah. Allah yyi daɗin tsira ga Annabi Muhammad (sallalahu alaihi wa sallam).
Post a Comment (0)