SHARUDDAN HIJABI A MUSULUNCI:
1. Ya rufe dukkan jiki sai abinda aka togace(wato tafin hannu da fuska).
2. Ya Zama mai kauri ba shara - shara ba.
3. Kada hijabi ya zama mai ado(kwalliya)
4. Ya zama yalwatacce ba mai kunci ko matsatsse ba.
5. Ka da a sanya masa turare.
6. Kada hijabi ya yi Kama da tufafin maza.
7. Kada hijabi yayi kama da tufafin Arna (Kafirai).
8. Kada ya zama tufafin alfahari ko na shuhra.
9. Kar a sa masa hoto (musamman na abu mai rai).
10. kar ya yi kama da na ‘yan bidi’a.
Allaah Yasa matan mu su gane.