BABU KASUWA

BABU KASUWA




A baya Malamai mun shana, indai za'ayi yanka🐑🔪 to mu za'a kira idan dabba takai goma in muka yanka kai da kafa namune, sbd mune mukasan addu'an yanka. Haka duk idan akayi haihuwa🤰🏻🤱🏻 mu ake kira mu radawa yaro suna a biyamu... 

Idan akayi mutuwa🛌🏼, nanma ranar sadakan uku da na bakwai dana Arba'in duk sai an biya mukeyin addu'a. Lokacin gidan kowani malami baya rabo da farfesu, aljihun ko wani malami baya rabo da kudi...

Ana haka sai ga wasu sambin malaman zamani👳🏾‍♂👳🏾‍♀, masu zakin karatu, duk sukabi mutane suka koya masu karatun yanka😭... Sannan suka fadawa iyayen yara da kansu zasuna radawa jariransu suna👨🏻👶🏻. Suka gano wani hadisi wanda ya hana zaman makoki, 'yar shinkafan da muke diba wajen zaman makoki suka hana a zauna ballantana a zuba mana ita.

Da kullum da safe sai naji kira akan za'a rada suna, to amma tun bullo wansu ban karajin kira ba, wani yaronma sai ya girma🧑🏻 nake sanin waye ubansa...

Idan anyi mutuwa sunce 'ya'yan mamacin zasuma ubansu addu'a da kansu, mu kuma ko daga ina mukayi Allah zai amsa basai mun zauna a kofar gidan mamacin ba...

Rabona danasa yankan nama a bakina tun sallahn bara, babu wani mai kiranmu ya bamu yanka sai dai ma mujiyo kamshin suya a makota...

Hatta Almajiran da ake kawowa karatu wajen mu, sunce sosamu yaro yayi karatu a gaban ubansa...

Yanzu hanyar samun kudi biyu ta rage, kodai na zama malamin siyasa ko kuma na kama noma.

_Allah jikan malaman mu na Sunnah..._

*_Sheichkul Islam Allama Malam Geenty Zaria_*
Post a Comment (0)