DUK MALAMIN ADDINI KO USTAZUN DAZAKAGA BASHI DA SANA'A TO KATABBATAR DACEWA BA TAFARKIN ANNABAWA YAKE BI BA

DUK MALAMIN ADDINI KO USTAZUN DAZAKAGA BASHI DA SANA'A TO KATABBATAR DACEWA BA TAFARKIN ANNABAWA YAKE BI BA.


Malamai magada Annabawa ne wani mai hikima yake cewa amma insunyi aikin annabawa din kuma daga cikin aikin annabawan Allah akwai sana'a wadda ta hada da kasuwanci da dai sauransu Allah yafada mana wannan acikin Alqur'ani inda yake cewa:" Kuma bamu taba aiko da wani manzo ba face yana cin abinci kuma yana zuwa kasuwanni(dan kasuwanci)..........zuwa karshe. Sanannen abune manzo s.a.w dan kasuwane yayi kasuwanci, Sayyadina Abubakar ma haka Sayyadina Umar shi har fashin makaranta yake sai ya wakilta makocinsa shi kuma yaje kasuwa watarana kuma shi sayyadina umar ya zauna a makaranta shi makocin nashi yaje kasuwa da sauran sahabbai duk sun kasance suna sana'a. Saboda haka qalubale gareku ku ustazai kasan wani ya dauka talaucima Ustazanci wannan fahimta kuskurece tsantsa a tashi asamu sana'a Allah zai samata albarka kaga ga sunnah ga rufin asiri masha Allah

Post a Comment (0)