DARAJAR KI ABINCINKI

DAKE AKE GLOBAL🌹

🌹Darajar ki Abincin ki🌹

*BEANS BALLS* (Alala) 
Abubuwan da ake bukata:
Wake
Attaruhu
Albasa
Maggi curry
Kwai
Mai
Fulawa
Garin biredi (bread) 

*Yadda da zaki yi:*
Ki surfa wake ki wanke ki dora a tukunya, sai ya dahu (ba'a saka kanwa kwata-kwata).

Idan ya dahu sai ki zuba a matachi, idan ruwan ya tsane sai ki juye a mazubi mai tsabta, ki sa muciya ki tuke shi. Idan ya tuku sai ki zuba jajjagen attaruhu da albasa da maggi da curry duka a wannan lokaci. Sannan sai a dinga mulmula shi, ana sakawa a cikin garin fulawa, ana tsoma shi, a ruwan kwai a saka a garin biredi, sai a tsoma a mai idan yayi ya soyu alamun (golden brown) sai a kwashe. 

Ana iya cin sa da kowanne abu ko shi kadai. 

Khadija Imam
🌹Dake Ake🌹

# dakeake #DarajarkiAbincinki #KhadijaImam #hausa #hausawa

http://www.dakeake.com


Post a Comment (0)