GUDUN TSIRA 2 COMPLETE

Gudun tsira
Littafi na biyu 2
Complete
Na Abdulaziz sani m gini
Ebook creator::- Suleiman Zidane kd....
Whatsapp 09064179602

★GUDUN TSIRA★
Littafi Na Biyu (2)
Part A

Suleiman zidane kd....

A CAN gidan sarautar sarki Ruguzan kuwa bayan
tafiyar Muzaru sai Siyama ta umarci sauran
dakarunta su talatin da tara dasu dauko abincin
guzurinsu dake cikin jakunkunansu su ci.Ba tare
da
gardamar komai ba kuwa suka cika umarnin suna
ji
suna gani suka hakura da wannan abinci mai
dadin
gaske na alfarma wanda aka shirya musu.Itama
Siyama nata abincin guzurin taci bayan sun gama
cin abincin kowa ya kimtsa sai Siyama ta dubesu
cikin nutsuwa tace,abinda nake so daku shine
lokacin da sarki ya turo a kirawoni ku biyoni a
baya
amma kafin mu iso inda zan gana da shi,ku sulale
ku fice daga cikin gidan sarautar nan gaba daya ku
nausa daji,zan hadu daku a can Dajin Zamhar inda
kabilarmu gaba daya zasu yi zaman jiranmu na
tsawon rabin sa'a kacal.Idan har muka wuce sa'a
daya bamu riskesu ba a can to abu ne mayuwaci
ni
daku ya kasance mun tsira da rayuwarmu.Koda
Siyama tazo nan a zancenta sai hankalin gaba
dayan
dakarun nata ya tashi ainun domin a sannan ne
suka gane abinda take shirin yi.Cikin alamun firgici
daya daga cikinsu ya dubeta yace haba ya
shugabata saboda me zaki durfafi wuta alhalin
kinsan cewa baki sha maganin konewa ba?Siyama
tayi ajiyar numfashi sannan tace,ai abinda ya koro
bera ya fada cikin wuta yafi wutar zafi.Sau tari sai
mutum yayi kundumbala ya tari fadan da yafi
karfinsa sannnan yake fita daga wata
masifar.Nasan
irin jarumtakarku kuma nasan iyakar irin abinda
zaku iyayi.Ku jajurce duk wuya duk rintsi ku fice
daga cikin garin nan a raye,kada ku damu dani
don
nasan duk yanda zanyi na kare kaina.Ku sani cewa
daga yanzu mun daura damarar yakin ceto
rayuwarmu data jama'armu gaba daya da kuma
gyara rayuwar 'yan bayan mu don haka ranmu da
lafiyarmu ba a bakin komai suke ba.Siyama ba
gama fadin haka sai suka an kwankwasa musu
kofa.Take Siyama ta dubi daya daga cikin dakarun
nata tayi masa inkiya yaje ya bude kofar saiga
hadimin Sarki Ruguzan wanda ya kawosu
masaukin
ya shigo da sauri fuskarsa cike da annuri.Koda
yaga
alamar su Siyama basu ci abincin da aka kawo
musu ba sai nan take fuskarsa ta sauya yanayi ya
dubi Siyama cikin alamun tsananin damuwa yace
yake wannan ma'abociyar kyawu da kwarjini mene
ne dalilin da yasa bakuci wannan abincin da aka
kawo muku ba alhalin sarki ya karbeku hannu biyu
a matsayin manyan bakinsa ya karramaku kuma
ya
baku masaukin da yake baiwa sauran abokansa
sarakai.Koda Siyama taji wannan batu sai tayi
murmushi mai taushi ga hadimin wanda ya
kidimashi ya sukurkuce bisa ganin yadda kyawunta
ya karu ainun tace,yakai wannan babban hadimi
na
sarki ka sani cewa mu mutanen daji ne wadanda
suka saba da abincin 'ya'yan itatuwa da naman
tsuntsaye da dabbobi,bamu saba da irin wannan
abincin naku ba don haka idan muka cishi da
yawa
zai iya lalata mana cikinmu.Yanzu menene ya
kawoka garemu?Hadimin ya maidawa Siyama
martanin murmushin yace,Sarki ne yace nazo na
tafi
dake izuwa inda zaku gana dashi,domin ya gama
zantawa da 'yan majalisarsa.Koda jin haka sai
Siyama
da dakarunta suka mike tsaye suka fito daga cikin
dakin,amma sai wannan hadimi ya yasha gabansu
ya dubi Siyama yace,ai ke kadai sarki yake son
gani
don haka dole ne masu tsaron lafiyarki su jiraki a
anan.Koda jin haka sai Siyama ta sake murmushi
tace,ai bazasu shiga cikin dakin da zan gana da
Sarki ba saidai su tsaye a waje.Koda jin haka sai
Hadimin ya juya ya wuce gaba yana mai yiwa su
Siyama jagora suka nausa izuwa wani bangaren
dabam na gidan sarautar,suka rinka shiga loko
loko,sako sako masu kwanoni da lunguna masu
zurfi
wanda komai kular mutum bazai iya dawowa baya
yabi ainihin hanyar da aka biyi dashi ba,amma
Siyama tana haddace hanyoyin a cikin kanta
tamkar
akan takarda ake rubutasu da alkalami.Saida
sukayi
tafiya mai tsawo sannan suka iso kofar wani katon
gida mai tsananin fadi da tsawo wanda indai
mutum
ya shiga cikinsa zaiji kamar an jefashi a RIJIYA
GABA DUBU ne.Siyama na ganin wannan gida ta
sake aiyana zargin abinda ta ayyana a ranta.Sarki
Ruguzan ke shiryawa akanta taji ta sami tabbacin
hakan babu wani kokwanto.Da isowarsu sai
Hadimin
ya waigo domin ya gayawa Siyama cewar
dakarunta
su tsaya anan yayi mata jagora izuwa cikin
gidan,kawai sai yaga babu mutum ko daya daga
cikin dakarun nata guda talatin da tara sai ita
kadai.Abinda yai matukar bashi mamaki kenan ya
dubeta yace,ina masu tsaron lafiyar taki?Siyama
tayi
dan guntun murmushi tace,Ai tun a can baya kafin
mu fara shiga cikin sakon nan masu zurfi suka
tsaya
don kada su bace.Koda gama fadin hakan sai ya
murda kofar gidan wacce ta kasance ta bakin karfe
zalla mai nauyi da kaurin gaske.Take kofar ta bude
suka kunna kai ciki.Cikin gidan iya hangen idanun
mutum babu komai a cikinsa face ciyawa mai
taushi
wacce aka shukata a kasa ta zama kamar kilishi.A
can nesa suka hango Sarki Ruguzan zaune akan
wani gadon Sarauta ya dora kafarsa daya akan
daya
kuma yayi shigar yaki fuskarsa cike da murmushin
farinciki.Koda Siyama ta hango Sarki Ruguzan a
cikin wannan hali taga irin kirar da Allah yayi masa
ta katon sadauki mai murdadden jiki gami da tarin
kwarjini sai zuciyarta ta da karfi tsoro ya
shigeta,amma data tuno da irin hadarin da take
ciki
ita da kabilarya sai taji zuciyarta ya kekashe ga
barin tsoron kuma koda Girman Sarki Ruguzan
yakai
na tsauni bazata kasa tunkarasa ba.Lokacin da
wannan hadimi ya hango Sarki daga inda yake
zaune sai ya tsaya cak ya juyo ya dubi Siyama
yace
to nifa nazo iyakata zan juya na fita na barku keda
sarki.Siyama na jin haka sai ta dubi Hadimin tayi
murmushi tace,idan ka fita ka rufe kofar da kyau
yadda ko ni ko
Sarkinka babu wanda zai iya budeta ya gudu har
sai
dayanmu ya kar daya.Koda jin wannan batu sai
hadimin ya firgita kuma ya kamu da tsananin
mamaki bisa yadda akayi Siyama ta gane cewa
akwai wani tuggu wanda sarki ya shirya
mata.Cikin
rawar jikin hadimin ya ruga da baya ya kulle kofar
gidan ta waje yasa kuba ya dada rufeta sosai.Ita
kanta kubar da aka kulle kofar ta isa abar kallo
domin katuwa ce sosai don yaro dan shekara tara
zuwa goma bazai iya rabata da kasa ba saboda
girmanta.Sarki Ruguzan na zaune bisa wannan
gado
ya kurawa Siyama idanu yana mata murmushin
mugunta kawai sai yaga ta tunkaro inda yake kai
tsaye itama tana yi masa murmushin mugunta ba
tare da shakkar komai ba har saida ya zamana
cewa
tazarar dake tsakaninsu bata wuce goma ba
sannan
Siyama ta tsaya cak ta rike kugunta da
hannayenta
biyu kuma ta murtuke fuskarta.Koda ganin haka
sai
Sarki Ruguzan ya takarkare ya bushe da
mahaukaciyar dariya kamar bazai daina ba.Daga
can
sai ya turbune fuskarsa ya mike tsaye yana mai
dakawa Siyama tsawa yace,ke yarinya kiyi sani
cewar duk wanda ya rigaka kwana dole ne ya
rigaka
tashi.Na dade da samun labarinki kuma na dade
ina
jiran zuwan wannan rana wacce zamuyi GABA DA
GABA domin na gama dake yadda ko a tarihi ba za
a sake tunowa dake ba kuma baza a tuna da
kabilarku ba tamkar ma baku taba wanzuwa
ba.Yanzu kin kawo kanki cikin RIJIYA GABA DUBU
inda IHUNKI BANZANE,banga wanda zai iya
kubutar
dake ba daga sharrina yanzu zan sumar dake
sannan na kawar da kimarki ta 'ya mace alhalin
babu wani 'da namiji daya taba samun wannan
dama
a gareki sai ni.Bayan nan sai nayi miki KISAN
GILLA
na cire kanki na aikawa da mahaifinki domin yasan
cewa duk beran dana danawa tarkona bai isa ya
iya
tsallakewa ba.Lokacin da Sarki Ruguzan yazo nan
a
zancensa sai Siyama ta tari numfashinsa tana mai
kyalkyalewa da dariya tace,yakai wannan tsohon
azzalumin sarki kayi sani cewa kamar yadda ka
dade da sanina gami da yin bincike akan komai
nawa nima na dade da sanin komai akanka,kuma
na
dade ina tanadin hanyoyin dazan bi na kawo
karshen zaluncinka a kasar nan.Ina mai tabbatar
maka da cewar koda zaka sami nasarar tarawa
dani
to saidai ka tara da gawata.Yau kuma yanzu ko ni
ko kai saidai a dauki gawar daya a cikin wannan
gida.Na fito da nufin RAI KO MUTUWA.sai kayi
shirin
kare kanka.Siyama na gama fadin hakan sai ta
zare
takobinta ta ruga izuwa kan Sarki Ruguzan,shi
kuwa
saibua sake kishingida yana murmushi kamar ba
hari za akawo masa ba.Koda ya rage saura baifi
taku uku ba su hadu sai Siyama ta tako tsalle a
sama ta kawo masa mugun sara da nufin ta cire
masa kai.Cikin tsananin zafin nama sarki Ruguzan
ya mirgina can gefe daya.Koda takobin Siyama ta
dira akan gadon saita tsargeshi gida biyu tamkar
ansa zabira an yanka kabewa an rabata gida
biyu.Cikin ZAFIN NAMA sarki Ruguzan ya zare
tasa
takobin ya afka mata suka ruguntsume da
azababben yaki ya zamana cewa sina kaiwa
junansu
SARA DA SUKA cikin tsananin zafin nama,juriya da
bajinta ta ban al'ajabi.
Cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta ta ban
al'ajabi.Koda Sarki Ruguzan yaga cewa Siyama
tana
da horon yaki matuka gashi har sun shafe 'yan
dakiku suna gumurzu amma bai sami nasarar
koda
lakutar jikinta ba sai ransa ya baci nan take ya
shammaceta yasa kafarsa ya doki kirjinta.Saboda
karfin dukan saida tayi can gefe daya tamkar an
janyeta da majaujawa ta kife kasa da rub da ciki
tana aman jini.Koda ganin haka sai Sarki Ruguzan
ya bushe da dariyar mugunta.Kawai sai yayi jifa da
takobin hannunsa ya tofawa Siyama yawu akan
fuskarta yace zan more wannan jiki naki mai kyau
sannan na muje kyakkyawar fukskar taki..Kafin ya
gama rufe bakinsa sai yaji Siyama ta bushe da
dariya kuma ta mike tsaye zumbur kamar sifirin
tana
mai goge jinin jikinta.Itama sai tayi jifa da takobin
hannunta ta nunashi da dan yatsa tace,yakai
wannan
tsohon azzalumin Sarki,kayi sani cewa ina tabbatar
maka da cewa karfin bashine komai ba a
fada,naci,sa'a da juriya ma suna kaiga samun
nasara.Tana gama fadin hakan sai ta afkawa Sarki
Ruguzan suka sake kacamewa da sabon fada suka
rinka naushi da bugun juna.Ai kuwa ana fara
wannan gumurzun ne Siyama ta gane kurenta
domin
Sarki Ruguzan ya fita karfin damtse da zafin nama
nesa ba kusa ba kuma duk irin naushin datayi
masa
shanyeshi yakeyi,amma da zarar shi yayi mata
naushi daya sai kaga har layi take yi tana neman
faduwa,tsananin juriya ne gami da sabo da
gumurzu
yasa bata zuwa kasa.Koda Sarki Ruguzan yaga
Siyama taki zuwa kasa kuma bata fasa gabza masa
naushi ba a fuska harma ta fasa masa hanci da
baki
jini na yoyi sai ya fusata ainun ya daka tsalle sama
ya gabza nata wawan naushi a fuska da dukkan
karfinsa.Siyama ta kife kasa sumammiya ko
kyakkyawan motsi batayi ba tamkar ta zama
gawa.Cikin tsananin farinciki sarki Ruguzan ya cire
rigarsa ya tsugunna akan Siyama ya juyo da ita
yasa
hannayensa biyu ya farke rigar jikinta.Koda ya
yunkura zai afka mata sai kawai yaji ta soka masa
wani abu a wuyansa,take jini ya kama kwararowa
kasa.Sarki Ruguzan ya mike tsaye yana yin baya
taga taga yana mai dafe abinda ta soka
masa,kawai
sai ya zare abin a lokacin daya kwarara uban
ihu,sai
yaga ashe kashin wata dabba ne ta soka
masa.Nanfa
jini yaci gaba da kwararowa daga jikin wuyan nasa
amma yana tsaye bai fadi ba,sai ya rugo izuwa kan
Siyama yana mai bude hannayensa da nufin ya
damketa ya shaketa suyi MUTUWAR KASKO.Koda
ya
kawo mata sura sai ta sunkya ta shige ta karkashin
kafafunsa ta dako gadon bayansa da kafafunta ta
baya,kawai sai ya fadi kan katakon karyayyen
wannan gado.Take wani icen gadon ya tsireshi a
ciki
ya hudo ta gadon bayansa.Sarki Ruguzan ya rinka
kwarara uban ihu da kururuwa sannan idanunsa
suka kafe,jikinsa gaba daya ya sandare ya zama
gawa.A sannan ne Siyama ta mike tsaye tana layi
sakamakon jinin dake zuba a gefen kanta saboda
naushin da Sarki Ruguzan yayi mata dazu ya tsaga
mata kanta kuma har sannan hancinta bai daina
yoyon jini ba.Hakika ita kanta Siyama bata taba
zaton cewar zata tsira ba daga sharrin Sarki
Ruguzan ba,kawai ta saida ranta ne akan ko tayi
nasara kota rasa rayuwarta.Lokacin da Sarki
Ruguzan yayi mata wannan naushi a fuskar ta ta
kife
kasa ba suma tayi ba,amma ta fita daga cikin
haiyacinta saita dauke numfashinta tayi kamar
suman tayi.Damar datayi amfani da ita kenan ta
shammaceshi ta zaro wannan kashi daga cikin
aljihun wandonta cikin bakin zafin nama ta soka
masa a makoshinsa.Lokacin da Siyama ta dubi
gawar Sarki Ruguzan ta tabbatar cewar ta mutu sai
tayi murmushin farin ciki amma data juyo ta dubi
kofar gidan ta tabbatar da cewar bazata iya budeta
ta
fita ba sai hankalinta ya dugunzuma ainun sannan
ta
dubi ko ina a cikin gidan taga babu ta inda zata
iya
fita sannan ta tuno cewar idan fa aka sake jimawa
akaji shiru za a bude kofar dakaru su shigo,in
kuwa
aka shigo aka ga ta kashe Sarki itama rubdugu za
a
yi mata a kasheta kuma tabbasa sarkin yawa yafi
sarkin karfi.Kuma bayan an kasheta za a bi sawun
dukkanin jama'arsu a hallakasu.Koda tazo nan a
tunaninta sai hankalin ya kara dugunzuma fiye da
ko
yaushe ta rasa abinda ke mata dadi a duniya,nanfa
ta kama kai kawo a cikin gidan tana mai ci gaba
da
kalle kalle da tunani.Tana cikin hakane ta daga
kanta
ta kallo rufin saman gidan saita ga ashe na katako
ne.Nan take farin ciki ya lullubeta kawai saita daka
tsalle sama ta kama rufin tayi ta tafiya a kansa da
hannayenta da kafafunta tamkar kadangaruwa har
saida ta iso wani wuri inda ta dan hango hasken
wata yar karamar huda sannan tasa hannunta ta
doki
wajen take katakon daya rufe wajen ya burme.Tana
zura kanta ciki ta shigo sai gashi ta fito a saman
gidan.Cikin sauri tayi ruf da ciki akan rufin saman
domin dakaru ta hango suna takai kawo a ko ina
cikin gidan sarautar don tabbatar da tsaro.Saida ta
shafe yan dakiku a kwance a saman ginin sannan
taga dakaru sun rarrabu saura mutum daya jak a
wani sako.Cikin hanzari ta daka tsalle ta duro a
bayan wannan badakare ta murde wuyansa ya
sulale
kasa matacce,kawai sai ta jashi izuwa cikin wani
sako mai duhu ta cire kayan jikinsa tayi canji da
nata,kawai sai ta bude wani kwandon shara na
karfe
ta jefa gawar badakaren a ciki ta rufe kawai sai ta
fito
daga cikin sakon ta kunna kai izuwa hanyar fita
daga gidan sarautar gaba daya kai tsaye ba tare da
shakkar komai ba ta saje a cikin dakarun gidan
sarautar masu fita.Duk da cewar ta saje da
dakarun
zuciyarta sai bugawa takeyi da karfi domin gani
take
yi kamar a koda yaushe asirinta zai iya tonuwa a
gane ko wacece ita.Wani iko na Allah kuma ta
gaban
wannan
hadimi daya kaita inda Sarki yake ta wuce harma
suka hada idanu amma bai shaidata ba.A Wannan
lokaci hadimin ya kagu yaga Sarki ya bude kofar
wannan gida ya fito amma sai yaji shiru.A wannan
lokacin ji yake kamar ya bugawa sarki kofa amma
saboda tsoron kada yayi laifi shi yasa bai buga
kofar
ba kuma yayi tunaniin ko har a sannan sarko bai
gama more rayuwarsa ba da Siyama.Har Siyama ta
iso bakin kofar karshe ta gidan Sarautar babu
wanda
ya tareta,amma tun kafin ta iso bakin kofar taga
masu gadin su hudu sun kura mata idanu suna yi
mata kallon rashin sani da rashin yadda.Nan take
Siyama ta gane cewa lallai idan ta karaso bakin
wannan kofa baza'a barta ta fita ba sai an
binciketa,in kuwa aka binciketa sai an gano wacece
ita.Koda ya rage baifi taku uku bata riski masu
gadin
sai ta daka tsalle sama ta makesu da kafafunta su
duka hudun a fuskokinsu a lokaci guda suka zube
kasa sumammu.Ai kuwa dakarun dake bayanta
suka
hango abinda ya faru suka falfalo da gudu,itama
Siyama tana durowa kasa bisa kafafunta sai ta
falfala
da azababben gudu na ban al'ajabi ta fice gaba
daya
daga cikin gidan sarautar.A sannan ne fa dakaru
suka bita duu!suna ihu suna harba mata
kibiyoyi.Idan mutum yaga yawan dakarun da suka
bi
bayan Siyama suna son su kure mata gudu,kuma
mutum yaga irin ruwan kibiyoyin da ake yi mata
dole ne yayi rantsuwa cewa babu yadda za'ayi ta
tsira da rayuwarta.A can kofar wannan gida na
cikin
gidan sarautar wanda Siyama ta kashe Sarki
Ruguzan a cikinsa.Koda wannan hadimi yaga
dakarun gidan sarautar gaba daya sun rude suna
ihu
kuma sun ruga izuwa can kofar fita daga gidan sai
shima ya dimauce yayi zargin ko Siyama ce yabi
ta
wata hanyar daban ta gudu,don haka hannunsa na
karkarwa yasa kuba ya bude kofar yaja wadansu
dakaru masu yawa suka ruga izuwa cikin
gidan.Suna
isa inda gadon nan na sarki yake sai suka iske
gawar Sarki Ruguzan soke a jikin katakon
gadon.Koda sukayi arba da gawar sai kowa ya
firgita
ainun kuma suka cika da tsananin mamaki.Nan
take
wannan hadimi ya kurma uban ihu mai tsananin
firgitarwa ya dakawa dakarun dake bayansa tsawa
yace maza kuje ku gayawa sarki yaki cewar 'yar
shugaba Sharwan ta kashe sarki kuma ta gudu.Nan
take wadannan dakaru suka juya da baya da gudu
shi kuma sai ya fara kokarin cire gawar daga jikin
katakon da take tsire.Saida aka shafe sa'a uku da
rabi ana tseren gudu tsakanin Siyama da
wadannan
dakaru su basu cimmata ba ita kuma ba ta bace
musu ba,tun ana cikin birnin kisra har aka shiga
cikin daji.Babu abinda ya daurewa dakarun kai yayi
matukar basu mamaki face ganin yadda Siyama ta
tsallake harin ruwan kibiyoyin da ake yi mata ta
sama da kasa kai kace aikin sihiri ne.Koda aka
shiga
cikin wani daji wanda Siyama ta saba yin farauta a
cikinsa tun tana yarinya karama ta lakanceshi
ainun
sai ta fada cikin wani surkuki mai yawan
duhuwoyi,hanyoyi barkatai gami da koramai da
kwazazzabai da kuma manyan ramuka da ciyoyin
fadamomi da koramu.Tana shiga cikin wannan
surkuki sai dakarun suka nemeta sama da kasa
suka
rasata tamkar anyi ruwa an dauke.Amma saboda
naci har gari yayi duhu Dakarun basu bar dajin ba
suna ta neman Siyama a cikin kowanne sako da
lungu har cikin kogon duwatsu shiga suke suna
haska ko ina da fitilun itatuwa.A karshe dai ba
basu
ganya ba sai sukayi hakurin dole suka koma izuwa
can gidan sarautar.Suna zuwa ne suka iske gidan
sarautar a cike da mutane ana gabatar da jana'izar
sarki Ruguzan.Da yawa daga cikin mutanen garin
murna sukeyi bisa mutuwar sarki Ruguzan saboda
tsananin mulkin zaluncin da yake yi musu,to
amma
saboda tsoron dan'uwansa Yarima Darwaz wanda
shine zai gaji karagar mulkin babu wanda ya nuna
farincikinsa a fili.
Babu wanda ya nuna farincikinsa a fili.A wannan
lokaci tuni an binne Sarki Ruguzan a cikin
kabarinsa,yarima Darwaz ya kwanta akan kabarin
yana ta faman rusa kuka da ihu.Da kyar da sidin
goshi fadawa suka bashi baki suka lallabeshi ya
tashi daga kan kabarin.Yarima Darwaz da Sarki
Ruguzan sun kasance uwa daya uba daya,kuma
yarima Darwaz ya girmi sarki Ruguzan,asali ma
shine ya kamata ya hau kan karagar mulki amma
saboda tsananin son da yake yiwa dan uwan nasa
Ruguzan ya hakura ya bar masa sarautar.A takaice
dai a duniya babu abinda Yarima Darwaz yakeso a
duniya sama da Sarki Ruguzan,don haka a wannan
rana yana cikin tsananin bakin ciki wanda ba zai
iya
misaltuwa ba kuma gashi ya kasance mutum mai
bakar zuciya gami da rashin imani fiye da Sarki
Ruguzan,don haka a wannan rana hatta fadawan
kasar ma a tsorace suke dashi suna baya baya
don
gudun kada ya huce haushinsa a kansu.Lokacin da
wadannan dakaru masu wadanda suka tafi neman
Siyama suka dawo sai suka zube kasa agaban
Yarima Darwaz suka sunkui da kawunansu kas aka
rasa wanda zaiyi bayanin cewar ba aga Siyama ba
wacce ta kashe Sarki Ruguzan.Koda Darwaz yaga
haka sai ya kara fusata ainun ya yunkura da sauri
ya
zare takobinsa da nufin ya hau Dakarun da
sara,kawai sai yaji an daka masa tsawa.A fusace
ya
waiga,koda yaga wanda yayi masa tsawar sai
jikinsa
yayi sanyi ya sauke takobin tasa kasa cikin sanyin
jiki.Ba wani bane yayi masa tsawar ba face
matarsa
ZUMAIRA.Zumaira ya karaso gaban Darwaz ta
karbe
takobin dake hannunsa ta dubeshi tace,idan ka
kashe wadannan dakaru bazaka sami sakamakon
komai ba face na dadin bacin rai da bakin ciki
tunda
asarace ga masarautarmu.Tunda dai Sarkin yaki da
manyan zakwakuran dakarunsa sun bi bayan
wannan Yarinya na tabbatar da cewar sai ka yanke
mata hukuncin daya dace da laifin data tafka.Koda
Zumaira tazo nan a zancenta sai Yarima Darwaz ya
zubar da hawaye sannan ya matsa gaban kabarin
dan uwan nasa ya dafashi yace,Na rantse da
kaunar
da nake yiwa Sarki Ruguzan sai nayiwa Siyama
mugun kisan gilla irin wanda ba a taba yiwa wani
mahaluki ba a doron kasa,kuma sai na shafe gaba
dayan kabilarsu daga kan doron kasa yadda har
abada ba za a sake tunowa dasu ba.Koda fadin
hakan sai Darwaz ya sake kwantawa akan kabarin
Sarki Ruguzan ya fashe da sabon matsanancin
kuka
har saida Zumaira tazo ta tasheshi tsaye ta shiga
rarrashinsa ta jashi izuwa cikin gidan Sarautar
sannan kowa ya kama gabansa.
¤¤¤¤¤¤¤
SARKIN YAKIn birnin kisra basu dawo daga bin
sawun Siyama da jama'ar kabilarta ba sai bayan
kwana uku.A wannan lokaci ma tuni anyi bikin
nadin
sarautar Sarki Darwaz ya hau karagar mulki amma
a
tsawon kwanaki ukun Sarki Darwaz bashi da wani
sukuni da kwanciyar hankali,burinsa kawai yaga
sarkin yaki ya dawo tare da Siyama.Da rana tsaka
su Sarkin yaki suka shigo fadar birnin kisra suna
shigowa fadar suka iske Sarki Darwaz zaune bisa
karagar ya sunkui da kansa kas,gashi ana ta tafiyar
da harkokin mulki amma shi Sarki Darwaz yayi
shiru
kamar bashi ne sarkin ba domin fadawa ne suke
zartar da komai.Koda Sarki Darwaz yaji sawun
dakaru da yawa sun shigo cikin fadar saiya dago
da
kansa da sauri amma dayaga sarki yaki akan gaba
babu Siyama a tare dashi sai jikinsa ya kama
tsuma,zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone
saboda tsananin fushi.Sarkin yaki ya zube kasa
gaban sarki Darwaz bisa guiwoyinsa yana mai
sunkui da kansa kas yace,ya shugabana munbi
sawun Siyama har izuwa sansaninsu a daji inda
muka isle babu ko kaza a wajen sun kwashe komai
nasu sunyi hijira.Mun sake bin sawunsu izuwa
cikin
dajin har tsawon kwanaki biyu amma ko duriyarsa
bamujiba domin sawunsu dana dabbobinsu ma ya
dauke.Al'amarin dayayi matukar bamu mamaki
kenan tamkar aikin sihiri.Koda sarkin yaki yazo na
a
zancensa sai sarki Darwaz ya mike tsaye a fusace
ya kwarara uban ihi wanda ya firgita kowa a cikin
fadar.Faruwar hakan ke da wuya sai ga Bokan
Garin
wanda ake kira HURGAS IBINI SALBARU ya bayyana
tsulum a tsakiyar fadar.Hurgas ya karasa gaban
Sarki Darwaz suka kurawa juna idanu sannan Boka
Hurgas ya risina yace Ya shugabana,Siyama da
sauran jama'arsu suna nan a cikin yankin kasarka
sun saje da mutane a cikin daya daga cikin
biranenka,bisa wannan dalili ne yasa ba a gano
inda
suka ba.Idan har ka bari suka fice daga cikin
wannan nahiya tofa har abada baza a dauki fansa
akansu ba kuma komai daren dadewa sai Siyama
ta
dawo kasar na ita da jama'arta ta rushe mulkinmu
sun karbi karagar kasar bisa taimakon wata
hatsabibiyar jaruma wacce zata addabi gaba dayan
sarakuna da attajiran duniya.Koda Boka Hurgas
yazo
nan a zancensa sai hankalin Sarki Darwaz ya
dugunzuma ainun fiye da ko yaushe ya dubi
Hurgas
cikin alamun tsananin damuwa yace,yakai abin
dogarona iyaye da kakanni maza ka sanar dani
birnin da su Siyama suke domin nayi shiri da
kaina
na jagoranci dakarun yaki masu yawa muke mu
shafesu daga doron kasa.Koda jin wannan batu sai
Boka Hargus yayi ajiyar zuciya cikin alamun
karayar
zuciya yace,ai nayi iya kokarina domin na gano
inda
suke amma na kasa saidai kawai na sami nasarar
ganowa cewa suna bangaren gabashin kasar
nan.Don haka ku hanzarta tunkarar dukkanin
manyan birane da suke gabas har izuwa karshen
iyakarmu.Koda jin wannan batu sai Fuskar Sarki
Darwaz ta fadada da murmushi na farinciki nan
take
ya dubi Sarkin Yaki Amzad yace maza kaje ka
shirya
mana sabuwar runduna ta mayaka dubu dari uku,ni
da kai zamu jagorancesu izuwa gabashin kasar
nan
kuma tun kafin mu tafi inason a tashi manzanni su
tafi izuwa biranen dake karshen iyakokinmu a
gayawa
shugabanninsu cewar su rufe kofofin garuruwansu
yadda ba shiga ba fita har sai na aiko da umarni.A
sannan ne fada ta watse kowa ya kama
gabansa.Har
Sarki Darwaz ya jiya zai shiga cikin gidan sarautar
saiya juyo da sauri ya dubi Boka Hurgas a cikin
alamun damuwa a karo na biyu yace,yakai abin
alfaharin birnin kisra waishin wace shu'umar
budurwar jarumar da idan ta hadu da Siyama zata
taimaketa har ta rushe mulkinmu?Koda jin wannan
tambaya sai boka Hurgas yaja dogon numfashi
gami
da ajiyar zuciya sannan yace hakika kayi tambaya
mai kyau kuma mai muhimmanci saidai a yanzu
babu isasshen lokaci wanda zai isa na baka labarin
wannan shu'umar jaruma wacce daidai take da
GUGUWAR ZAZZAGAR BALA'I ga dukkan sarakunan
duniya.Shawarar da zan baka kawai itace kayi
hakuri
zan baka labarin wannan jaruma ko da akan
hanyarmu ne ta dawowa bayan mun sami nasarar
gano inda su Siyama suke mun shafesu daga
doron
kasa.
A WANE HALI 'YAN KABILAR SU SIYAMA SUKE
CIKI?
SHIN SARKI DARWAZ ZAI CIKA BURINSA?
INA LABARIN SIYAMA DA TAKE GUDUN TSIRA?
SHIN
ZATA KOMA CIKIN KABILARTA?
A WANE HALI MAHAIFINTA DA MAHAIFIYARTA
SUKE
CIKI?
INA LABARIN ABOKAN TAFIYARTA DATA
UMARCESU
SUYI GABA,A WANE HALI SUKE CIKI?
Mu hadu a GUDUN TSIRA kashi na uku don jin
cigaban wannan kasaitaccen labari.
Da alamu littafin bai karbu ba ko Dan ba samun
comments.
Barkan ku da Sallah.Allah ya maimaita mana.Ameen.
Gudun tsira
Littafi na biyu 2
Na Abdulaziz sani m gini
Ebook creator::- SULEIMAN Zidane Kd.....
Whatsapp 09064179602.....



Post a Comment (0)