YA KAMATA KI GANE WANNAN!

🎍 *YA KAMATA KI GA NE WANNAN* 🎍


🎍➖Da ace mace zata iya bambance tsakanin *haƙƙoƙinta* da kuma *Ihsani ko kyautatawa* wanda mijinta zaiyi mata, lallaikam da ta samar da kashi 50% na zaman lafiyar da ake samu a zamantakewar Aure.

🎍➖ *Haƙƙiƙin ki* sune abinda zaki riƙa bibiya, karki bari a tauyemiki su. Amma *Ihsanin* da mijinki yasabayi miki, liƙaci zuwa loƙaci, kar kirika ɗaukarshi a matsayin *Dole* ko *haƙƙinki* ne sai ya yimiki, wanda kike mayar da shi idan har baiyi miki ba za ki iya cimasa kwala. Wannan fa ganin damarsa ne tare da kyautatawa irin ta zamantakewa.

🎍➖Lallaikam idan *mijinku* yasauke *haƙƙoƙin ku* da suke a kanshi, baiyi son kai ki son rai atsakani ba, to sauran kyautatawar da zaiyi muku kuma sunansu *Ihsani*, kuma shi *Ihsanin* ya danganta ne da yadda zai fifita wacce tafi nuna masa kulawa tare da tarairayarsa a matsayinsa na mijinta, wanda yasa zuciyarsa ke ƙaunarta fiye da ke.

🎍➖ Shari'ah zata tuhumeshi wajan fifita ɗaya akan ɗaya, wajan tauyewa ɗaya haƙƙoƙinta, amma *Shari'ah* ba zata tuhumeshi akan fifita ɗaya akan sauran wajan *Ihsani* ko yadda zuciyarsa zata *ƙaunaceta* ba, matuƙar ya biya mata haƙƙoƙin da suka rataya akansa.

🎍➖ Za ki iya samarwa da kanki cuta da rashin kwanciyar hankali matuƙar kika dâge akan dole sai mijinki ya nuna miki ƙauna kamar yadda yake nunaw Abokiyar zamanki ƙauna, ko dole sai ya ruƙa daidaita muku sahu wajan *Ihsani*, ya kamata kisan cewa wannan ganin damarsa ne ba wai haƙƙinki bane, ballantana har kiriƙa tayar da jijiyoyin wuya akansu ba. Baiwar Allah hankalinki bazai taɓa kwanciya ba, kinyi bankwana da nutsuwa matukar zaki riƙa sanya idanuwa akan *Ihsanin* da akeyiwa abokiyar zamanki, abinda yakamata kiyi shine kiyi *ƙoƙarin* karki bari atauye miki *haƙƙinki*, da kuma duban me takeyiwa mijin ne na kyautatawa da har yake kyautata mata sama da ke ? wanda ke ba kya yi masa?

Allah yakyauta kuma yakara tabbatar da dauwamammiyar soyayya tare da tsoron Allah atsakanin ma'auratanmu. Ameenn.

*Idris M Rismawy*
Post a Comment (0)