HIKAYAR MAI GASKIYA AWOJO FUJITSINA
Daga Sadiq Tukur Gwrzo
A karni na gona sha biyu a Japan, lokacin da ɗan sarkin kasar mai suna Hojo Fukurima ya gaji sarautar yankin yana da shekaru goma sha huɗu, anyi wani mutum mai gaskiya. Sunan sa Awojo Fujitsina.
Rannan, Sarki Hoji yaje babban wurin bautarsu na mabiya addinin Bhudda a Kakurumi, sai bacci ya kwasheshi gar yayi wani mafarki alhalin baccin nasa.
A mafarkin ne wani mutum yake shaida masa cewa yakai Wannan Sarki, hakika shekarunka sunyi matuk'ar kankanta wajen mulkar wannan gawurtacciyar k'asa mai tarin al'umma, saboda haka ina umartarka daka nemo wani amittaccen mutum ka ɗorashi a matsayin wazirinka damin ya tallafa maka wajen gudanarwar mulki. Sunan wannan mutumi Awojo Fujitsina.
Da sarki Hojo ya farka daga baccinsa, sai ya samu kansa yana ta nazari akan mafarkinsa. Daga bisani dai, ya samu kansa yana mai gaskata wannan mafarki, yana Cewa hakika Ubangijin danazo bautawa ne yayi min wahayi, don haka tilas nayi aiki da wannan umarni.
Babu jimawa sarki yasa akayi masa cigiyar Awojo Fujitsina aka kawo masa shi gabansa.
Bayan Awojo ya gurfana a gaban Sarki, sai Sarkin yake shaida masa mafarkin da yayi jiya da dare.
Bayan Awojo ya gama sauraren sarki tsaf, sai Yace ya mai martaba, haka ai ba zata yiwu ba. Idan har zaka bani mukami domin a mafarki ance ka bani, to hakika wata rana zaka yayyanka mu da wukake domin cika umarnin da aka baka acikin mafarki.
Sarki Hoji ya tuntsure da dariya, sannan yace Ina fatan hakan ba zata kasance ba, amma dai yanzu tilas ka karɓi wannan mukami.
Abinda akayi kenan, Awojo Fukatsina ya zamo babban waziri ga Yaron Sarki Hojo, ya zamo shine mafi faɗa aji, shike rike da baitul mali, kuma sahun masu bada shawara akan harkokin mulki.
Rannan Awojo yana tafiya izuwa baitul mali domin ya kai wasu sulallan kuɗi da sarki ya bashi ajiya, sai kuwa yayi tuntuɓe ya faɗi kasa, jakar kuɗin ta zube kasa warwas gar kuɗin suka tsiyaye.
Awojo yayi sauri ya mike, ya fara tattara kuɗaɗen. Sam bai kula da lafiyar saba, ta waɗannan kuɗaɗen kurum yakeyi.
Bayan ya tattara ne ya lissafa, sai yaga sule hamsin ya ɓata acikin kuɗin. Dubawar da zaiyi sai yaga wani kwararo wanda ya nufi babban kogi mai wucewa, nan take ya gamsu cewar sulai hamsin ɗinnan tanan yabi ya faɗa cikin wancan kogi.
Anan kuma sai ya soma tunanin abinyi. Shin ya cika wannan sulai hamsin ɗin a kuɗinsa izuwa baitul mali, ko kuwa lalle ya shiga neman wannan wanda ya ɓata?.
A karshe sai ya yanke shawarar tunda amanace ta sanya aka bashi wannan matsayi, to bai kamata ya yaudari gwamnati da sauya mata dukiya ba. Don haka tilas ko nawa zai kashe sai ya nemo wannan sulai hamshin.
Da gama yanke wannan shawara, sai ya bazama izuwa gabashin kogin. Akwai wasu yan kauyuka da mutane ke rayuwa, kuma akasarinsu masuntane. Yayi shela izuwa garesu yace yana neman taimakonsu, kuɗinsa ne ya faɗa cikin wannan teku, kuma duk wanda ya nemo masa shi zaiyi masa kyauta mai daraja.
Abinda akai kenan, mutanen kauyukan suka bazama cikin teku suna lalube. Rannan dai yini akayi ana nema. Sai can da yammaci wani masunci ya gabatowa da Awojo sulai hamsin yana cewa kaga iya abinda na samu a kuɗin, watakila ragowar sun zurare ne zuwa wani wurin na daban.
Awojo Fukatsina ya cika da farin ciki harda rungume masunci, yace ai daman abinda nake nema kenan. Sannan ya zaro jaka huɗu na kuɗin Yen a kuɗinsa ya baiwa masunci yana masa godiya.
Masunci ya cika da ta'ajibi, yace kai kuwa wanne irin mutum ne, akan sulai hamsin kasa muka ɓata lokacin mu alhali kai kanka kana da ninki-ba-ninkinta?
Awojo Fukatsina ya dukar daki kasa cikin nutsuwa yace "Ka sani ba darajar sulai hamsin ɗin yasa na ruɗe har nasa ku binciko min ita ba, darajar amincin da yasa aka bani ajiyar sulai hamsin ɗin na duba.. Wajibin mune mu kula da kayyakin gwamnatin mu da amana da gaskiya".
Ai kuwa kamar wutar daji haka labarin wannan aiki na gaskiya da rikon amana ya yaɗuƴ a kasar ta japan, mutane sukai ta mamakin gaskiya da rikon amanar sa. Shikuwa Sarki Hoji murna yayi gagaruma dajin wannan labari tare da karawa Fuji Fakutsina matsayi, tayadda sai da ya zamo amintacce mai faɗa aji sama da kowa a wurin Sarki.
Kunji aikin gaskiya. Dafatan 'Yan uwa zamuyi riko da gaskiya, za kuma mu alkinta kayan gwamnatinmu da Amana gami da kyuttawa. Amin.