10. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
bukarmada.blogspot.com
...
Suka tasa ni da yarona a gaba sai ka ce fursuna, sai Dina, garin da dan Ali ke zaune. Muka same shi da mutanensa suna alwala, suna shirin salla. Na yi gaisuwa, amma ko dubana bai yi ba. @bukarmada Maimakon amsa gaisuwar sai ya jefo mini wata tsohuwar bindiga, ya ce in gyara masa. Na ce da yarona Demba, wanda ke mini tafinta, ya gaya masa ban san yadda a ke gyaran bindiga ba. Da jin haka sai ya ce karya na ke yi, sai da kyar dai ya yarda. Amma ya ce im ban iya gyarar bindiga ba, to, sai im ba shi wuka da almakashi. Na ce a gaya masa ba ni da irin wadannan abubuwan. Yaronsa bai gama rufe baki ba sai muka ga dan Sarkin nan ya suri wata bindiga, ya dura harsashi @bukarmada ya dana, ya kuwa kawo bakinta daf da kunnen Demba, Ba domin dai Larabawan da ke tare da shi sun yi maza sun fizge bindigar ba, da ya harba.
Mutanen, da fizgewa, sai suka ce mu kau da jiki, muka tashi. Demba ya firgita, ya kadu, ya gigice, ya ga mutuwa kusa. Da dare sai ya yi kokarin tserewa, amma Larabawan da ke gadimmu ba su ba shi dama ba. Domin duk inda za su kwana, sai su tura mu daga kurya, su kuwa sai su baza kansu daga kofa, @bukarmada yadda babu mai iya wucewa sai ya taka daya cikinsu. Da haka har muka kai Benaum.
ALI YA MAISHE NI FURSUNA
Da na ji aka ce Ali shi ne Sarkin kasar Ludamar duka, kuma a Benaum ya ke zaune, sai na zaci zan ga gari ne ginanne wanda ya fi duk sauran biranen Bakar Fata da na wuce. Amma ba haka ba ne. In ka hango garin sai ka ce wani sansani ne, don babu gidaje, sai tanti aka kakkafa. @bukarmada Da isarmu kofar garin, mutane suka faso maza da mata da yara suka rufe ni. Wadansu suna kama mini riga za su fige, wadansu suka fige hulata daga kaina. Da haka dai har muka kai tantin Ali da kyar.
Muka sami Ali yana zaune a kan shimfida, yana yanke gashin bakinsa, ga wata mace ta rike masa madubi yana dubawa. Kewaye da shi kuma ga fadawa, kowa ya buga @bukarmada harde. Dattijo ne a fuska, ko da ya ke bai tsufa ba. Kuma da dubansa za ka san Balarabe ne na usuli, ba kamar sauran Larabawa na kasar ba. Mutum ne mara walwalar fuska, mai alamun mugun hali. Ya yi mini duban tsabta, daga nan bai sake ce kome ba.
Amma mutanen da ke kewaye da ni su suka sha mini kai kwarai, tun dai ba mata ba. Babu irin tambayar banza da ta wofi da ba su yi mini ba. Bayan haka suka caje jikina kaf, suka tura hannu cikin @bukarmada aljihuna, suka tilasta ni na tube rigata wai don su ga farar fatar jikina. Kai har yatsuna na kafa da na hannu sun kidaya, sai ka ce dai sun ga wata halitta dabam, ba dan Adam ba. Ana cikin haka aka kira salla, kafin mutane su watse sai bawan Ali wanda ke mini tafinta ya ce wai ga abinci Ali ya ce a kawo mini. In waiwaya haka sai ga wani katon alade Ali ya ce in yanka in ci. Ko da ya ke ina jin yunwa kwarai da gaske, amma na ga ba daidai ne in ci wannan dabba da Musulmi ke kyama a gabansu ba. @bukarmada Saboda haka sai na ce ai ni ban taba cin alade ba. Sai suka kwance aladen suka koro shi wajena, zatonsu wai da alade da Kirista ba su jiyayya. Amma sun ga ba haka ba ne don shi aladen da jin an sake shi sai ya yi ta fada wa kowa da cizo, ya fasa taron, ya shiga karkashin karagar Sarki ya kwanta.
Da mutane suka watse, ni kuma aka kai ni tantin babban bawan Ali. Amma aka ce in zauna a kofa kada in shiga, kada kuwa in taba wani abin da ke cikin @bukarmada dakin. Na ce a taimake ni da abinci, yunwa ta dame ni sai aka kawo mini tsabar dawa dafaffiya, daga ita sai gishiri. Da na ci aka shimfida mini tabarma a waje nan na kwana tare da mutane ba iyaka.
Da gari ya waye, sai ga Ali da kansa bisa doki, ya ce a kai ni wani daki da aka shirya domina. A lokacin Fatima matarsa ba ta garin. Ali ya ce in zauna har ran da Fatima ta komo, in ta gan ni sa'an nan zai sallame ni. Na sami dakin @bukarmada kewayayye ne, kuma da karan dawa aka yi shi, aka dibiya jinka. Don wulakanci sai na tarar an daure mini aladen nan a ciki. Na san yadda Larabawa suka dauki alade, babu wulakantacciyar halitta a gare su kamarsa, kuma ba mai cinsa sai Nasara. Watau sun nuna mini ga ni ga abincina ke nan! Da dare ina kwance, idona ya kasa barci, sai na ji duddugen mutum ya shigo. Can sai aka taka ni a kafada. Na yi wuf na tashi zaune, shi kuwa wanda ya shigon ya koma zai fita da gudu, sai ya yi karo @bukarmada da yarona ya fadi. Ashe ya fada a kan aladen nan ne, aladen kuwa da ya ji zafi ya duntsi hannun mutumin nan da hakora. Barawo sai kara! Kafin a yi haka mutane sun kewaye rumfar, wai wadansu zatonsu ni ne zan gudu.
Da na dubi yadda mutanen nan ke wulakanta ni sai ka ce ba mutum ba, sai na yi mamaki. Na ga dai ni bako ne, ba ni da kowa, ba ni da karfin tsare kaina. Amma kuma da ya ke ni Kirista ne a tsakanin Larabawa, ba za a yi mamakin @bukarmada duk irin abin da suka yi mini ba. Ban kara firgita ba sai da na ji aka ce wai dalilin da ya sa aka tsare ni don ana zaton rahoto ne ya kawo ni. A cikin wannan tsoro da tashin hankali na zauna. Kullum, da cewa gari ya waye, mutane za su rufe ni, suna sa ni ina yin abubuwan da ba su kamata a sa mutum ya yi ba. Kai, ba shi dai yiwuwa im @bukarmada bayyana irin miyagun halin mutanen nan, amma tun ran da na ke ban taba ganin masu yin takama da iya mugunta kamar Larabawa ba. Sun mai da mugun hali wani ilmi ne musamman, har koyonsa su ke yi a tsakaninsu, wanda ya gwanance har ya rika alfarma.
An ce zamana bako ko Kirista duka ba su suka sa Larabawan nan su ke wahalshe ni ba. Wai dalili dai ke nan, gaya wa Ali da aka yi wai rahoto na ke yi, na zo ne in duba kasarsa in koma gida im ba da labari. Alkalami ba ya iya rubuce dukan bakin ciki, da @bukarmada wuya, da wulakancin da ke samun wanda aka sa wa wannan mugun laihi na rahoto, saboda haka irin abin da na sha a hannun Ali na bar wa mai karatu sani. Na dai yi duk irin abin da bako ke yi na jure wulakanci. Larabawan nan sun wulakan ta ni, sun zage ni, sun munana mini, duk kuwa na daure, wai dai don in ji dama dama. Amma ina? Wayewar gari ke da wuya, ba na sake samun sukunin kaina sai kwanciyar barci. Ni dai tun ran da na zo duniya ban taba ganin wuya irin wannan ba, ban ko taba ganin marasa @bukarmada imani kamar Larabawan nan ba a duk duniya!
NA ZAMA WANZAMI!
Larabawan Benaum, ko da ya ke su kansu ragwaye ne, masu son jiki, duk da haka ba su barin wanda ya shiga hannunsu ya yi sukuni. Yarona Demba shi a ke turawa kullum ya samo wa dokin Ali ciyawa. Nikuwa bayan an jarraba ni a sauran ayyuka duk an tarar ba zan yi amfani ba, ran nan @bukarmada sai aka ce in zama wanzami. Na zama Sarkin aska, don an ce a fada zam fara aski, kuma a kan wani dan yaro, autan Ali, zam fara nuna gwanintata. Aka nuna mini wuri na zauna, yaron kuma ya zauna a gabana. Aka dauko mini wata 'yar aska, tsawonta kamar inci uku, aka ce in shafa ruwa, im fara. Na shafe kan duk da ruwa, don Larabawan @bukarmada wannan jiha su kan aske kan 'ya'yansu ne duk. Na kuma danki aska na shiga aski. Abinka da mai koyo, da farawa sai kuwa askar ta yanki yaron kadan a kai, sai jini.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
bukarmada@hotmail.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada