ILLOLINDA KYAWU KE JAWOWA MASU SHI

ILLOLINDA KYAWU KE JAWOWA MASU SHI



Kyau yana sa mutum ya samu cigaba a harkokin rayuwarsa amma masana tunanin dan Adam sun ce yana kuma da illolinsa da ke sa mutum cikin wani hali na daban.
Shin za ka iya kasancewa mai dan karen kyau? Wannan ba wata matsala ba ce da yawancinmu muke tunani domin dai ba shakka abu ne da za mu so idan hakan za ta yuwu.
Bincike ya nuna cewa likitoci ba su cika ba da wata kulawa ba sosai ga mutanen da suke da kyau.
Amma duk da haka amfani da kuma illolin kyau abubuwa ne da aka dade ana nazari a kansu a fannin ilimin tunanin dan Adam.
Shin mutanen da Allah Ya yi wa kyakkyawar siffa da kira, ma'ana masu dan karen kyau suna rayuwa ne a abin da za a iya cewa aljannar duniya, wato ba su da wata matsala, ko kuma rashin wannan dan karen kyau yana da ranarsa?
Lisa Slattery Walker da Tonya Frevert, masana a fannin ilimin tunanin dan Adam a jami'ar North Carolina da ke Charlotte sun gudanar da bincike akan wannan batu, kuma sakamakon binciken ba abu ne da za ka yi tsammani ba.
A haka za ka dauka kyau wani abu ne da ya ke tafe da duk wani alfanu da daukaka da alfarma. Za mu ga cewa Allah Ya azurta mutum da wani abu mai kyau a rayuwarsa, misali fuska mai kyau ko kira ko wani abu, daga nan
kuma sai kawai mu dauka cewa haka mutumin nan yake a sauran fannoni ma da wannan kyau.
'' Wannan shi ne daya daga cikin abubuwan da ke tattare da kyau da muka gano a yawancin binciken da muka yi.'' In ji Walker.
Wannan shi ne abin da masana tunanin dan adam ke kira al'adar daukar, duk abin da yake da kyakkyawar sura, yana da kyau.
To amma masu kallon wasan kwaikwayon nan na ban dariya mai suna 30 Rock za su iya daukar wannan a matsayin abin nan da Hausawa ke cewa kyalkyal-banza, ko ta-gina-ba-ta-shiga-ba.
A wannan wasan kwaikwayo na barkwanci, mutumin da ake kira Jon Hamms, bai iya aikinsa na likitanci ba duk da cewa ya gama makarantar koyon aikin. To amma saboda kyawun da Allah Ya yi masa, wannan ya ba shi damar yin
wannan makaranta har ya gama.
Sakamakon bincike da dama ya tabbatar da wannan abu da ake kwatantawa da kyalkyal-banza.
Misali a fannin karatu, Walker da Frevert sun gano tarin binciken da aka yi da ke nuna cewa malaman makaranta suna daukar daliban da suke da siffa mai kyau a matsayin wadanda suka fi sauran abokan karatunsu cancanta da
basira, kuma a kan haka suke ba su maki mai yawa.
Wani abu kuma shi ne mutanen da suke da kyau suna samun tasirin na kyalkyal-banza, inda suke ta cin moriyarsa wata kila tun daga farkon rayuwarsu har zuwa wani lokaci, kamar yadda Frevert ta ce.
''Za ka ga kana ta samun kwarin gwiwa da karfin hali da dama mai yawa a rayuwarka da za ka nuna cancantarka.''
A wurin aiki za ka ga kyawun fuskarka ya zamar maka alheri, saboda mutanen da suke da kyawu a ido za ka ga sun fi samun kudi domin an fi saurin daukarsu aiki da ciyar da su gaba a wurin aikin fiye da wadanda ba su kai su
kyakkyawar siffa ba.
Sakamakon wani bincike da wasu dalibai masu karatun digiri na biyu suka gudanar ya nuna cewa, akwai bambancin kashi 10 zuwa 15 cikin dari na abin da masu kyau suke samu tsakaninsu da wadanda ba su kai su kyau ba.
Walker ta ce, ''za ka ga idan kana da kyau kana samun dama a rayuwarka, tun kana dan makaranta har ka fara aiki.''
Wannan lamari har a wajen shari'a ma haka yakan kasance, domin hatta mutumin da aka gurfanar a gaban kotu idan mai kyawun siffa ne za ka ga zai iya samun hukunci mai sauki ko kuma ma ka ga ba a hukunta
shi ba gaba daya.
Haka kuma idan wanda ya kai karar shi ne mai kyakkyawar siffa, za a iya yanke hukuncin da zai dadada masa, ma'ana ya yi nasara a shari'ar, ko ma a ba shi diyya mai yawa.
Walker ta ce wannan abu ne da yake kusan a ko ina.
Komai da ranarsa;
To amma fa idan a yawancin lokaci kyau yana sa mutum ya samu dama wato ya ci gajiyar kyawun nasa a wani lokacin kuwa lamarin ya kan sauya.
Yayin da ake ganin mazaje da suke da kyakkyawar siffa za su fi samun damar aikin shugabanci ko jagoranci, su kuwa mata masu kyau za su iya gamuwa da matsalar kin daukarsu irin wannan aiki wanda ke bukatar nuna iko.
Kamar yadda aka sani mutanen da suke da kyau maza ko mata suna gamuwa da kishi.
Wani bincike ya gano cewa idan mutumin da yake maka jarrabawar daukanka aiki ya ga ka fi shi kyau da wuya ya dauke ka aikin, musamman ma idan jinsinku daya.
Babban abin damuwa kuma shi ne kyawunka zai iya cutar da kai a fannin kula da lafiyarka.
Mukan danganta kyau da lafiya, ma'ana ba sosai muke nuna damuwa ba idan wata cuta ko rashin lafiya ta kama wanda yake da kyawun siffa.
Haka kuma za ka ga likitoci ba kasafai suke mayar da hankali ba sosai idan suna yi wa mutanen da suke da kyau magani.
Wani abu kuma shi ne, kyau yakan sa a kaurace wa mutum;
Wani bincike da aka gudanar a 1975, ya nuna cewa idan mutane suka gamu da matar da take da kyau a hanya sukan dan kauce mata, watakila saboda su mutunta ta, amma kuma duk da haka sukan yi nesa-nesa da ita idan suna ganawa.
Kyau abu ne da ke ja da daukar hankalin mutane, to amma kuma fa, mutane da yawa sukan ji shayin yi wa mace mai kyau magana. Kamar yadda Frevert ta ce.
Shafin sada zumunta na intanet na OKCupid a kwanan nan ya tabbatar da haka, inda ya ce rahotanni sun nuna cewa mutanen da suke da dan-karen kyau idan suka sa hotonsu mai kyau a shafin ba sosai suke samun masu
sha'awar kulla mu'amulla da su ba.
Amma idan suka sa hoton da bai yi kyau matuka ba sai su rika samun masu sha'awarsu.
Kamar yadda watakila za ku iya dauka, kyau ba tabbaci ne na samun farin ciki a ko da yaushe ba, ko da ike dai yakan taimaka wa mutum.
Frevert da Walker sun kara bayyana hakan inda suka ce, ''mutane na da wata da al'ada akan kyau inda muke dauka cewa idan mutum yana da kyau sai mu dauka cewa yana da cancanta.''
Suka ce a takaice wannan wani abu ne kawai da muke rayawa a tunaninmu na gaggauta yanke hukunci akan matsayin mutum.
Kuma kamar sauran takaitattun hanyoyin da muka bi wannan ma ba abin dogaro ba ne wajen sanin gaskiya. In ji Frevert.
Ta kara da cewa idan da za a bayar da bayani akan yadda kokari ko abubuwan da wani mutum mai kyau ya yi a aikinsa a baya kafin a yi masa jarrabawar daukansa aiki to da hakan za ka ga ya rage tasiri da kyawunshi zai yi a
sakamakon da zai samu.
A karshe Frevert ta nuna cewa idan ka bayar da fifiko kan kula da fitarka, misali kayan da kake sa wa ko fuskarka ko makamancin hakan ta yadda za ka fito da kyau, hakan zai iya sa ka rika wahalar da kanka ba gaira ba dalili, ko
da kuwa kana da kamanni mai kyau.
Ta ce, ''idan ka damu matuka da kyau yadda za ka ja hankalin mutane, hakan zai iya shafar kwarewarka da kuma mu'amullarka.''
Ta kara da cewa,'' abu ne da mutane kawai suke damuwa da yin sa amma ba wani kyau duk da yad da ya kai da zai iya sauya yanayin yadda ake daukar mutumin da ba shi da kyakkyawar dabi'a.''
Kamar yadda wata marubuciya Dorothy Parker ta bayyana: ''Kyau a fata kawai ya tsaya amma muni ya kai har cikin kashi.''
DAGA DANDALIN AMINU YAHUZA 08080678100
Post a Comment (0)