MAI KATOBARA!

MAI KATOBARA!



Mai katobara ya kasance daga cikin bayin sarki da a ke zaman fada da shi. Ba a taba zaman fada da shi aka tashi lafiya ba, sai ya fadi maganar da za ta sa dogarai su ba shi kasha. Wani lokaci kafin sarki ya cece shi har ya yi tabshi. Wata rana sai ya ce: “Da ma ’yan Boko Haram su kashe sarkin nan a nada wani sabo.” Saboda dukan da aka yi masa kan wannan magana, mai katobara sai da ya yi jinyar sati uku bai zo fada ba. Ranar da ya dawo fada, ko gyaran murya bai yi ba har aka tashi. Can sarki ya mike zai shiga gida, sai wani dogari ya ce: “Yau Mai katobara bai yi magana ba.” Shi kuwa sai ya ce: “Ka ga kuwa sai sarki ya sa a doki gyatumarsa ko?”

 
Post a Comment (0)