JARUMA YAZILA 3 COMPLETE

J


  ARUMA YAZILA Littafi na Uku Na Abdul'aziz sani madakin gini Created and design by:- Shuraih Usman Publishing shuraih 99% From http://shuraih.wapsite.me . . Lokacin da tsoho kasim yayiwa dabira da dakarunta jagora izuwa cikin daji domin yin farautar irin wadannan tsuntsaye da ya harbo sai ya ci gaba da wucewa kan gaba zuciyar sa nata. Bugawa da karfi domin baisan inda yakamata ya kaisuba har a sami irin wadannan tsuntsaye. Haka dai suka wanzu suna nausawa cikin daji har tsawon sa'a daya da rabi bai tsaya a ko ina ba. Al'amarin daya sa jaruma Dabira ta kosa kenan ta dubi tsoho kasim ta daka masa tsawa tace "ya kai wannan maharbi ina zaka kaimune haka, har yanzu bamu isa dajimba ne?" Koda jin wannan tambayar sai tsoho kasim yaji kamar hantar cikinsa zata fito ta baki. Cikin karkarwar bAki yace, "ya shugabata ai muna dab da shiga dajin da tsuntsayen suke". Koda gama fadin hakan sai ya sunkuyar da kansa kas yana tunanin yadda zaibi ya sulale yagudu ya barsu a dajin tun da asirinsa yana daf da tunuwa. Hakika allah shine mai rufawa bawansa asiri, idan kuwa ya tona masa, tofa koda duniya kaf zata taru babu wanda ya isa ya rufamasa ba. Kwatsam! Bazato ba tsammani sai ga irin wa dannan tsuntsayen sak! Suna shawagi a saman su dabira. Tsuntsayen sun kasance masu yawan gaske tamkar shagalin biki suke, Koda ganin tsuntsayen sai dabira da dakarunta suka tsaya cak a waje daya suka dana kwari da baka suka dinga harbo tsuntsayen suna fadowa kasa shima tsoho kasim sai ya faki ido ya watsar da wadannan tsuntsaye guda bakwai na kan dokinsa. Suna zubowa kasa sai suka bace bat cikin hanzari ya harbo wasu guda bakwan ya dora akan dokinsa. Dayake su dabira sun shagala da harbin tsuntsayen basu lura da abinda tsoho kasim yayiba. Bayan an sami nasarar harbo tsuntsayen da yawa sai sauran tsuntsayen suka tsere. Nan take kowa ya debi nashi tsuntsayen ya dora akan dokinsa cikin mutukar farinciki jaruma Dabira ta dubi tsoho kasim tace, "madallah da wannan tsoho mai bayani na gaskiya. Yanzu sai mukoma da baya mukoma birnan mu domin nacika maka alkawarina agareka kuma zanso na baka masauki agidana da kaina domin kayi koda kwana biyune rak a gidana kaga irin yanayin rayuwarmu ta birnin misra". Kodajin wannan batu sai tsoho kasim yayi godiya yana mai nuna matukar farin ciki Nan take jaruma Dabira ta kada linzamin dokinta baya ta wuce kan gaba tana mai jerawa tare da tsoho kasim suka bi hanyar komawa birnin misra sauran tawagar na rufamusu baya Haka dai akaci gaba da tafiyar inda hira karde tsakanin Dabira da tsoho kasim inda taringa tambayarsa tarihin rayuwarsa dakuma irin gwagwar mayar da yasha a rayuwarsa a cikin daji bisa wannan sana'a ta farauta. Koda jin wannan tambaya sai tsoho yai tashara karya kala-kala haryana ta bayani irin gumurzun da yayi da manyan dabbobin daji yana samun nasarar kashesu. Kodajin wadannan labarai sai mamaki yakama jaruma dabira ta dubi tsoho kasim taga babu alamar sadaukan taka atare tashi saita aiyana aranta cewa duk yadda akai wannan tsoho da kuri yakeyi kawai donhaka sai tace aranta, "Nikuwa in allah ya yarda sai na kure wannan tsoho na gwada iyakar jarumtakarsa na gani lokacin da yarage saura tafiya kadan a iso kofar birnin misra sai jaruma Dabira ta sake nausawa cikin wani dajin daban al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan daya daga cikin dakarun dabira yadubeta yace "ranki yadade meyasa kika komar damu cikin daji alhalin gashi farautar tayi kyau munsamo abinda muka fito nema, koma kinsani cewa wannan daji dakika shiga damu dajine mai hadarin gaske wanda ke dauke da mugayen dabbobi?" Koda jin wannnan tambaya sai dabira tayi murmushi ta dubi mai tambayar tace , tace """ai ganinayi mun fito bamu sha wahalar komai ba mun sami tsun tsaye ai yana da kyau mu dan motsa jini?". Dajin haka sai hankalin sauran dakarun ya dugunzuma domin sunsan halin dabira idan tace tana son motsa jini dai-dai yake data ce tana son tayi yaki. Shikuwa tsoho kasim ko gezau baiyi ba sai kawai yakara kaimi ya wuce kan gaba ma a cikin dajin. Al'amarin daya baiwa kowa mamaki kenan har ita kanta dabira kuwa tce a ranta "yanzu shi wannan bushashshen tsohon gani yake zai iya wani abukenan ? To ai inda bakasa anan ake gardamar kokawa. Zamuga iya kar koka rinsa Abinda ya kara baiwa su dabira mamaki shine tsoho kasim ya sakarwa dokinsa kaimi ya zabureshi da gudu ba tare da shakkar komaiba Kwatsam! Sai gasu sun iso tsakiyar wani babban fili dazuwa sai suka ga wadansu manyan kuraye ayari guda akan bishiya. Tsoho kasim ne yafara farga da dabbobin don haka sai yaja linzamin dokinsa yayi turjiya ya daga hannu yana mai yiwa su dabira nuni da su tsaya. Nan take kowa yaja tunga ya tsaya. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin kuraye da tsoho kasim Kurayen sun kasance manya-manya masu matukar kwarjini da ban tsoro sai gurnnani suke yi suna wangame baki gami da dalalar da yawu kamar suci babu. Kai dagani kasan cewa yunwa sukeji kamar suci babu. Nanfa kuraye suka fara motsa jikinsu alamar cewa akoyaushe zasu iya daka tsalle su fado kan kasim Tsoho kasim ne yafara zare takobinsa daga cikin kube. Sannan sauran sauran dakarun dabira ma suka zare tasu takobbinsu itakuwa dabira komotsi batayiba daga kan dokinta sai murmushi take yi kawai tana kallon kasim da dakarunta alamar cewa tayarda da kanta su takeji. Koda kuraye sukaga su tsoho kasim sun zare takubbansu sai suka dako tsalle gaba dayansu alokaci guda asama suka fado kanu aka rugun tsume da a zababben yaki. Sai gashi kuraye sun jeho yaran Dabira daga kan dawakansu su duka kuma suka turmushe su suna kokarin cinyesu. In badamma dakarun sun kasance zakakuran gaskeba da farad daya kura yen zasu gama dasu. Nan fa akacigaba da bakin artabu ya zamana cewa kuraye sunfara yiwa dakarun Dabira rauni suna kartar jikinsu da faratan hannayensu da kafafunsu kuma suna kai musu cizo suna kaucewa da bugun bakunansu da takobi. Al'amarin tsoho kaasim kuwa, abin al'ajabin dayakeyine yasa Dabira takasa motsawa daga inda take ta kaiwa dakarunta dauki kawai sai tabude baki tana kallonsa cikin tsananin mamaki. Tunda kurayen suka afkawa su tsoho sai yazama kamar shaidani a tsakiyarsu ya dinga ra gargazarsu da takofinsa yana kaftara musu sara yana tarwa tsasu suna faduwa kasa, amma saboda naci da taurinkai irin na kurayen saikaga suna dada tasowa suna afkawa tsoho kasim duk da cewa jikinsa yai fata fata da jini. Nan dai tsoho kasim shika dai ya zamewa kuraye alakakai alokacin da suka gallabi sauran dakarun Dabira. Yayinda kuraye. Suka ga tsoho kasim yana yi musu muguwar barna sai duk suka bar da karun dabira suka yiwa tsoho kasim rubdugu gaba dayansu suka lullubeshi. Da yake sarkin yawa yafi sarkin karfi sai nan da nan kuraye suka fara ruda tsoho kasim saboda suna kai masa muggan hare-hare ta kowane bangare. Inbadan ma yana yana da tsananin zafin namaba da tuni sun ya galgala shi. A nan cikin wannan gumurzu ne wadansu kuraye guda uku masu mugun naci suka shammaceshi suka karci jikinsa da faratan hannayensu lokaci guda. Daya ta dankara masa sara akirjinsa waje uku, wajen ya dare har jini yai tsartuwa daya a gadon baya taimasa saran iri daya dana kirjin nasa, dayar kuma a cinyarsa, saboda tsananin zafi da zugin da tsoho kasim yajine ya kwala ihu kuma ya fusata ainun kawai sai yadaka wawan tsalle sama na bammamaki sannan ya sallamo kasa kafafunsa na sama kansa na kasa. A haka ya dinga gididdiga kurayen. Duk wadda yayiwa sara daya sai kaga ya fille mata kai ta fadi kasa mutacciya nan fa jinin kurayen ya dinga fantsama har yana. Bata jikin Dabira. Kafin ta ankara jikinta gaba daya ya rine da jini. Babbar jarumtar da tsoho kasim yayi shine tunda ya fara sare kan kurayen a sama hannunsa ko kafafunsa basu taba kasaba asaman yayi shawagi a kan kurayen tamkar tamkar tsuntsu mai fuka fukai sai da ya gama kashe kurayen gaba daya ya zamana babu guda daya mai rai sannan ne ya duro bisa kasa. A sannan ne dabira ta lura da wadansu tsofaffin manyan raunika a jikin tsoho kasim wadanda tuni sun warke abin da fara fadowa Dabira a rai shine ta yaya wannan tsoho yake irin wannan jarumta irin ta masu jini a jika wato matasa masu karancin shekaru ? Nan take taji cewa lallai akwai a yar tambaya akan tsohon. Abu na biyu wadannan tabon data gani a jikinsa da gani kasan gumurzu yayi da wani gagarumin sadaukin da ya illatashi. Dabira ta kudurce a ranta cewa lallai sai ta tambayi tsoho kasim yadda akayi yasami wadannan raunika. Bayan tsoho kasim ya gama kashe kurayen nan sai yaji Dabira tayima tafi gami da jinjina nan take dabira ta sakko daga kan dokinta ta taho izuwa inda tsoho kasim yake. Sai da tazo daf dashi har suna jin numfa shin juna sannan tatsaya cak tadube shi tace "ya kai wannan gwarzon jarumi kasani cewa rabon da naga jarumta irin taka tun sa'adda nayi gumurzun karshe da babbar abokiyar gabata Jaruma Yazila ta birnin kisra". Koda jin wannan batu sai tsoho kasim yaji zuciyarsa ta buga da karfi ya tsorata ainun domin ya zata Dabira ta gano ko wanene shi. Kawai sai yaji dabira ta kyalkyale da dariya sannan tace, "ka gafarceni yakai wannan jarumin tsoho, ka sani ina sani nace a shigo wannan dajin domin na gwada iyakar jarum takarka bisa labarin daka bamu kan hanyarmu bisa irin gwagwarmayar Da kayi. Tabbas yan zu na yarda kai jarumine a bin kwatance. Amma duk da haka zan sake yimaka wata jarrabawar ta karshe wadda ina ganin asannanne zanga karshen jarumtakar taka. Koda gama fadin han sai jaruma dabira ta bude jakarta ta guzuri ta dauko wani magani ta mikawa kasim tace, "ga wannan sai kasa a cikin raunin naka ". Nan take kasim ya karbi maganin ya shafa a raunikan da kurayen suka jimasa. A sannanne suma da karun dabira suka yiwa kansu magani bayan kowa ya kimtsa sai aka hau dawakai aka nufi hanyar birnin misra. Humaira na zaune a cikin harabar gidanta tana hutawa wadansu kuyangi hudu sun zagayeta suna tayata hira kawai sai ta hango Dabira da tsoho kasim sun taho gareta, wani bawa na rike da tsuntsayen da suka farauto. Tun daga nesa da Humaira tayi arba da idanun tsoho kasim sai taji zuciyarta tabuga da karfi. Ba komaine ya haddasa hakan ba jface jida tayi a jikinta cewar kamar ta taba ganin irin idanunnan arayuwarta amma sai ta kasa tuno a inda ta taba ganinsa. Shima tsoho kasim tun daga nesa ya kurawa Humaira idanu ko kiftawa bayayi. Koda suka iso daf kuwa sai yaji idanunsa sunkico da kwalla suna neman su zubo da hawaye. Babu shiri kasim ya sunkui da kansa kas. Nan take Humaira taji kaunar tsoho kasim ta shiga zuciyarta tamkar dama can tadade da sabo dashi. Cikin fara'a Humaira ta dubi dabira tace "yake 'yata wannan kuma wanene haka kika zo mini dashi?" Kafin dabira ta budi baki tace wani abu sai tsoho kasim ya zube kasa gaban humaira yace "Ni bakone daga birnin rum yake wannan matar sarki. Na zo gareku da salama kuma da yardar allah zan barku a cikin salama da karamci ina fatan zaku karbi bakun cina na kwanaki kadan cikin jin dadi?" Koda jin haka sai Humaira ta sunkuya. Da sauri ta kama kafadun tsohon kasim ta tashehi tsaye a lokacin da ta sake kura masa idanu tace, "haba ya kai wannan tsoho saboda me zaka durkusa min alhalin ka haifeni a haife?" Koda jin wannan tambaya sai idanun tsoho kasim suka sake cikowa da kwalla ya dubi Humaira yace, "ai duk inda 'ya mace take dole ne namiji ya girmamata tun da kune kuka haifemu. Duk da cewa shekaruna sunfi naki ina ganinki na tuno da ainahin mahaifiyata wadda kaddara taa rabamu". Dajin haka sai hankalin Humaira ya dugunzuma ta kasa sakin kafadun tsoho kasim tace, "wacce kaddara ce ta rabaka da mahaifiyarka?" Sa'adda kasim yaji wannan tambaya sai hawaye ya zubo masa yace, "makiyane suka rabamu tun ina jaririya har yau har gobe bamu sake saduwaba. Babban abikin cikina shine yanzu idan ma haifiyata na nan araye ko mun sadu ba zamu shaida junaba tunda bata sanni ba nima ban santaba". Koda Jin wannan batu sai hawaye ya zubowa Humaira tace, "ya kai wannan tsoho kayi sani jininka jininkane har abada. Ina tabbatar maka dacewa koda mahaifiyarka bata shaida kaba indai kukayi arba da juna saikun ji wani abu ajikinku, tabbas na tausaya maka matuka bisa jin labarinka domin al'amarine mai ban mamaki"". Lokacin da HUmaira tazo nan a jawabinta sai Dabira ta cika da tsananin mamaki domin a iya rayuwarta tare da humaira bata taba ganin ta zubar da hawayeba sai yau. Abin daya kara daure mata kai shine Humaira ta sha jin labarai na abubuwan tausayi wadanda ma suka fina tsoho kasim amma bata yi kukaba. Menene dalilin daya sa Humaira tayi kuka a yanzu bisa jin labarin tsoho kasim?" Tambayar da Dabira takasa bawa kanta amsa kenan. Nan dai dabira ta baiwa humaira labarin yadda ta hadu da tsoho kasim da duk abubuwan da suka faru a tsakanin su a daji. " Koda jin haka sai humaira ta kamu da tsananin farin ciki ta sake yiwa tsoho kasim barka da zuwa sannan ta umarci wata kuyanga safina ta tafi da tsoho kasim izuwa dakinsa kuma a kai masa ruwan dumi yayi wanka gami da abinci. Nan take kuyanga safina tatafi da tsoho kasim suka nufi bangaren da ake saukar baki. Har suka kuLe tsoho kasim bai daina waigowa ba yana kallon Humaira tamkar baya son rabuwa da ita. Kai kace 'yar uwarsa ce ta jini. Ita kanta Humaira sai taji bata son tsoho kasim yayi nesa da ita amma sai ta rasa dalilin hakan, mussamman a duk sa'adda ta dubi idanunsa wadanda take ganin cewa basu dace da shiba domin idanune irin na matasa masu karancin shekaru dabasu kai ashirin ba shi kuwa gashi ya kasance tsoho dan kimanin shekaru tamanin da doriya. Bayan kulewar kuyanga safina da tsoho kasim sai dabira ta dubi Humaira ta Baiyana mata sakon sarki cewar yana son a dafa masa wannan tsuntsu kuma zai zo da kansa bayan magariba yaci naman tsuntsun a turakarta. Koda jin wannan sako sai Humaira taji zuciyarta ta buga da karfi kuma ta cika da tsananin mamaki domin ita a zatonta sarki bazai taba zuwa kusa da ita ba sai bayan cikar shekaru ashirin da zuwanta birnin misra. Cikin sanyin jiki da yake HUmaira ta dubi Dabira tace, "shi kenan zan cika wannan umarni na abbanki" Nan take Humaira ta juya ta nufi turakarta itama dabira sai ta nufi tata turakar zuciyarta cike da tunani da wasi-wasi. A bin da yafara fadomata a rai shine wai shin menene ya kawo sauyin al'amura ne a yau tsakanin mahaifiyarta Humaira da abbanta sarki Raihan alhalin hakan bata taba faruwaba ? Anya kuwa sauyin al'amarin ba shi da nasaba da zuwan wannan bakon tsoho? Koma dai menene zan gani da idanuna kuma zan yi aiki da shawarar abbana nasa ido sosai akan wannan bakon tsoho don kada ya mamayemu ya cutar damu duk da dai yace shi musulmine, ai dole ne mu tabbatar da musuluncin nasa da kuma amanarsa. Wannan shine abinda ya faru tsakanin jaruma Dabira da iyayenta bayan ta tsinto tsoho kasim a can bayan gari. Al'amarin tsoho kasim kuwa lokacin da aka kaishi masaukinsa aka shigar da. Shi cikin wani daki mai kyau aka kai masa ruwan wanka kewaye kuma aka kawo masa abinci sai ya mike tsam yaje ya rufe kofar dakin yasa sakatu sannan yarufe duk tagogin dakin gaba daya suma ya samusu sakatu. Bayan ya tabbatar da cewa babu ta inda za a iya hangoshi daga waje sai yayi girgiza nan take ya rikide ya dawo izuwa ainahin siffarsa ta gaskiya, wato siffar JARUMA YAZILA. Nan take yazila ta shiga kewaye ta cire tufafin jikinta gaba daya sannan ta shiga cikin baho tayi wanka. Bayan ta fito daga wankane taje gaban madubi ta tsaya tana kallon fuskarta. Koda taga irin kyawun da allah ya bata kuma ta tuna yadda ta sauyawa kanta kamanni ta zama tsoho tukuf ta boye ainahin kamanninta ga mahaifiyarta Humaira sai ta fashe da kuka. Dama tun sa'adda yazila ta taho izuwa birnin misra tayi bincike a cikin tsafinta har ta gano cewa lallai mahaifiyarta na nan a raye a cikin gidan sarauta kuma.duk wadda tayi mata jagora izuwa wajenta itace 'yar uwarta ta jini wadda aka haifesu tare. Bisa haka ne yazila ta gane cewar lallai Humaira ce mahaifiyarta kuma Dabira ce 'yar uwarta wadda take dokin gani. Yanzu gashi tana son taga fuskar Dabira a matsayin 'yar uwarta ba akan matsayin abokiyar gabarta ba tana son dabira ta gane cewa ita 'yar uwarta ce ta jini. Tayaya zata biya duk wa dannan bukatu a cikin kwanciyar hankali? Sa'adda yazila tazo nan a zancenta sai ta fashe da kukan bakin ciki kuma hankalinta ya dugunzuma ainun domin ta sancewa a koda yaushe a sirinta zai iya tonuwa idan kuwa asirinta ya tonu kafin humaira da dabira su gano cewa ita jininsuce tata takare wata kila ma zata iya rasa rayuwarta a wannan lokaci. Koda yazila ta aiyana haka a cikin zuciyata sai ta sake fashewa da matsanancin kuka. Bayan an yi sallar isha'i sai Humaira ta caba ado sannan ta shirya kasai taccen abinci akan teburin dake falonta wanda aka yi shi da farfesun irin wannan tsuntsayen da su dabira suka farauto a daji. Lokacin da Humaira ta gama wannan kintsi sai ta sallami dukkan kuyanginta suka fice daga cikin turakarta gaba daya sannan ta zauna tasa wannan abinci agabanta tana kallonsa kawai a lokacin da jikinta ya kama tsuma saboda mamaki da fargabar zuwan sarki Raihan. Tana cikin wannan hali ne taji anyi mata sallama. A razane ta amsa sallamar ta dago kai tayi arba da sarki Raihan a tsaye shima ya caba ado na kure a daka fuskarsa Cike da annuri. Nan take kamshin turaren jikinsa ya cika falon gaba daya. Koda ganin sarki Raihan sai Humaira ta mike tsaye zumbur a lokacin da jikinta yaci gaba tsuma, yayinda sarki raihan yaga Humaira a cikin wannan hali sai shima ya kasa bude baki yace wani abu har ya zo kusa da ita ya tsaya. Tsawon 'yan dakiku suna tsayen dayansu baice uffan ba kuma kowannensu kansa na sunkuye suna kallon kas, sai sarki Raihan yayi gyaran murya sannan yace, "ya ke ummul Dabira shin na iya zama akan wannan kujera?". Koda jin wannan tambaya sai Humaira ta dago kai ta dube shi cikin mamaki gami da murmushi tace, "ya shugabana ai da wannan kijera da kuma wannan dakin duk a karkashin ikonka suke. " Koda jin haka sai sarki raihan yayi 'yar karamar dariya sannan yace, "A'a ina shakka. Na yarda cewa da wannan kujera da wannan daki a karkashin ikona suke amma banda mai dakin. Ya ke Humaira ki tuna cewa tun da kika zo garinnan tsawon shekaru goma sha takwas ban taba umartarki da wani abuba sai yau, kuma yau ne karo na biyu da muka taba kebewa tare. Kin ga kuwa ashe ke ba a karkashina ikona kike ba, kina dai karka shin alfarmata. Na san zaki yi matukar mamaki bisa ganina ayau na kawo miki ziyara har cikin turakarki, kuma bama keba hatta gaba dayan hadiman gidannan suna mamaki don gudun zargin wani abu shi yasa ban rufe kofar wannan daki ba leka bayanki ki gani". Cikin sauri humaira taleka bayan sarki sai ta hango wadansu dakarunsa mutun biyu a tsaye suna hangen duk abin dake faruwa tsakaninta da sarki amma kuma basa iya jiyo abin da suke tattaunawa koda ganin haka sai humaira tayi murmushi sannan tace. ” Haba ya shugaba ai shi kansa shaidan ba a ko ina yake samun nasara ba na yarda da imaninka da tsoron allahnka don haka ina da yakinin cewa babu wani mugun abu da zai shiga tsakaninmu face alkhairi yanzu sai ka zauna kaci wannan abinci wanda ka umarceni da na dafama maka ”. Koda jin haka sai sarki raihan yayi murmushi yace. ” Na yarda zan zauna naci abinci amma bisa sharadin cewa zaki cire dukkan tsoron dake ranki ki daina tsuma haka”. Da jin haka sai humaira tayi yar karamar dariya tace. ” Na amince amma ai bai kamata kaga laifina ba domin kwarjininka ne da mamakin wannan ziyara taka ta bazata su suka janyo mini lokaci guda duk su biyun suka yi dariya sannan suka zauna a tare zamansu ke da wuya sai sarki ya bude kwanukan abincin dake gabansa kamshi ya doki hancinsa ya shaki kamshi cikin farin ciki koda ya wanke hannunsa acikin bakinsa ya yanko loma guda ta abinci ya sa acikin bakinsa ya tauna ya tsaya cak ga barin cin abinci ya kurawa kwanon abinci idanu kawai al amarin da ya dugunzuma hankalin humaira ke nan tayi zaton ko abincin ne bai yi dadi ba. Dag cai saita ga hawaye ya zubowa sarki raihan cikin kaduwa humaira ta dubi sarki kuma ta dubi baki da kyar tace. ” Yake umma dabira kiyi sani cewa baki yi kuskurekomai ba a cikin wannan girki ?” Koda jin haka sai sarki raihan ya gyada kai sannan yasa daya hannun nasa ya share hawayensa ya dubi humaira yace. ” Yake umma dabira kiyi sani cewa baki yi kuskure komai ba acikin wannan girki kuma tsananin dadin girkin ne yasa na tuno da matata marigyiya da kuma yar uwarta ina so ki sani cewa rabona da cin abinci mai dadi irin wannan tun daga ranar dana rasa wadannan masoya nawa saboda bakin ciki rabuwa dasu. Ina so ki sani cewa nuni da cewa idan har ban zo bana baiyana miki wata muhimmiyar magana dake raina tsawon shekaru a yau bato har abada ba zan sami damar hakanba. Yake ummul dabira kiyi sani cewa tundaga ranar da mutane suka zo dake tare da jaririyarki dabira naji ina matukar kaunarki a zuciyata, amma sai naji bazan iya furta miki ba saboda tausayinki bisa ganin halin da kike ciki na bakin ciki rashin mijinki wanda aka kashehi a gabanki dakuma yadda kika bani labarinki naji cewar kin rabu da daya 'yar taki wato usainar Dabira wacce kika bayar da ita ga 'yar uwarki Nuzaira. Tun daga sannan na ji na kamu da tsananin tausayinki da kuma kaunar dabira, shiyasa na rokeki akan cewa komai dadewa kada kisanar da dabira cewa bani ne na haifeta ba har sai bayan shekara ashirin alokacin da zatayi aure murabu da ita an nuna mini a mafarki cewa a gobe-gobennen allah zai kawo wani sadaukin jarumin musulmi daga can nashiya daban wanda yafi Dabira jarumtaka kuma suna haduwa zasu kamu da son junansu akan wannan daliline na yi kundun bala na shirya wannan haduwa tamu domin na bayyana miki sirrin zuciyata. Idan harkin amince da tayina ina son a daura aurena da ke gobe". Koda jin wannan batu sai humaira ta fashe da kukan farin ciki taji kamar ta rungume sarki raihan humaira ta budi baki domin tace wani abu sai kawai suka ga dabira ta fito daga cikin turakar humaira idanunta sun yi sharkaf da hawaye. Cikin firgici da matukar mamaki sarki raihan da humaira suka mike tsaye suka kura mata idanu. Dabira tasa hannu ta share hawayen ta sannan ta dubesu daya bayan daya tace, "me yasa kuka buye mini wannan sirri tsawon shekara da shekaru ? Na rantse da girman allah duk inda 'yar uwata take sai na tafi nemanta! Waye ya kashemini mahaifina? Kuma ko waye ya kashe mahaifina sai na bincikoshi duk inda yake na hallakashi! Ina tabbatar muku da cewa bazan taba yarda nayi aure ba face na cika wadannan burika ". Koda gama fadin haka sai taji ta tsani birnin kisra da duk mutanen cikinsa saboda jin cewa asalin mahaifiyarta humaira daga can take. Koda sarki raihan da humaira suka ga dabira ta fashe da kuka sai han kalinsu ya dugunzuma suka yunkura zasu je gareta domin su rarrasheta amma saita ruga waje da gudu ta nufi turakarta. Da zuwa sai ta shiga can cikin dakinta mai kofa ta rufe ta sake fashewa da sabon kuka. Cikin sauri humaira da sarki raihan suka karaso kofar dakin dabira suka yi ta rokonta akan ta bude kofar amma taki, duk suka hakura suka koma turakar Humaira suka zauna. Tsawon lokaci duk su biyun sukayi tagumi basu ce komai ba. Daga can sai sarki ya mike tsaye ya dubi Humaira yace, "yanzu muna cikin tashin hankali da damuwa saboda haka sai gobe naji amsar tayin dana yi miki " Koda gama fadin hakan sai sarki yajuya ya fice daga cikin falon gaba daya. I ta kuwa Humaira ta bishi da kallo kawai cikin damuwa da tunani. Har dare ya raba sosai Humaira bata rintsaba saboda fargaba da tunani bisa jin abinda Dabira tafada cewar duk inda 'yar uwarta take saita tafi nemanta kuma sai ta nemi wanda ya kashe mahaifinta. Shima shi. Abinda ya tayar wa da humaira hankali shine, tasan irin bala'in sarki Daksur da sadauki Zaihar da irin sadaukantakar da karfin tsafinsu,don haka yana tsoron karonta da su don tana ganin cewa zasu iya hallaka farat daya muddin ta kai kanta inda suke. Haka dai humaira ta kasance acikin tsananin tashin hankali ta kasa zaune ko tsaye ta dinga kai komo acikin turakarta. Tana cikin wannanhali ne ta tuno da batun tsoho kasim au yi ` yar hira nan take ta aiyana zuwa dakin tsoho kasim ta tasheshi koda kuwa barci yake yi. Batare da bata lokaciba humaira tafito daga cikin turakarta acikin dare da durfafi bangaren da dakin tsoho kasim yake duk inda ta ratsa sai taga dakaru a tsaitsaye suna kan aikinsu na gadi kuma gaba dayan gidan sarautar a haskake yake da fitilu gwanin ban sha awa duk inda tazo giftawa sai dakaru su ratse su bata hanya babu inda aka dakatar da ita har ta iso kofar dakin tsoho kasim. Da zuwanta sai ta iske kofar dakin a kulle take ruf. Haka ma gaba dayan tagogin dakin. Koda ganin haka sai jikin humaira yayi sanyi ta tuna cewa yau fa tsoho kasim acikin matukar gajiya yake sakamakon artabun da yayi da kurayen nan har maya sami raunika saboda haka bai kamata ta tasheshi daga barci ba nan take humaira ta juya da baya da nufin ta koma turakarta. Amma sai ta jiyo sautin kuka acikin dakin tsoho kasim kuma sautin na muryar mace ne. Al amarin daya matukar bata mamaki ke nan domin ita a saninta ai tsoho kasim ne aciki wannan daki to mene neya shigar da mace cikin dakinsa ? Cikin fargaba da sanda ta koma izuwa kofar dakinta leka ta cikin kafar kubar ai kuwa tana lekawa ta hango zabgegiyar kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance zaune akan kujera tana faman sharba kuka a gefe daya daya ga wadannan tufafi na tsoho kasim ajiye a gefe daya wadannda akansu an dora layu da guraye na tsafi humaira ta kurawa fuskar budurwa idanu kawai sai ta lura da idanunta taga iri daya ne sak! Dana dabira. Koda ganin wannan al amari sai zuciyar humaira ta buga da karfi ta dafe kirjinta da hannayenta biyu ta juya baya cikin ajiyar numfashi tace a ranta. ” Duk yadda aka yi wannan yata ce ussainar dabira tazo mana a cikin kamannin tsoho kasim mene ya kawota garin nan ? Shin tazo neta cutardamu ko kuwa ta gano cewa mu jininta ne ta zo domin mu sadu ? ” Nan fa humaira ta kasa baiwa kanta amsar wadannan tambayoyi cikin tsananin fargaba da tashin hankali humaira ta koma dabaya don ta koma turakarta. Lokacin da ya rage saaura kiris ! Ta iske kofar turakarta sai kawai taga dabira tsulum ! A gabanta kamar daga sama ake jefota kafin humaira ta budi baki tace wani abu sai dabira ta dubeta tace. Yake ummata menene ya kaiki dakin bakonmutsoho kasim ? Kai sani sani cewa nida sarki duk bamu yarda da tsoho kasim Ba kuma na funkanci cewar akwai wata alaka tsakanin da shi. Da shi saboda haka gobe kafin na bar garin nan zaki yi mini cikekken bayani akan rayuwarki kafin ki baro birnin kisra ki da dawo nan misra da wannan kalami nake miki sallama allah ya tashe mu lafiya ” koda gama fadin hakan sai dabira tajuya ta koma izuwa cikin dakinta tamai da kofa ta rufe nan fa humaira ta sake rudewa ta kidime ta rasa abin da ke mata dadi a duniya domin bata san bayanin daya kamata ta yiwa dabira da sarki ba a goben. Da kyar humaira ta koma cikin dakinta ta kwanta taci gaba da tunani da zullumi. Har aka yi assalatu bata sami damar yin barciba. Kamar yadda humaira ta kasa barci hak shima sarki raihan ya kasa barci saboda tsananin damuwa har yaje masallaci da asuba. Ya dawo turakarsa bairintsaba. Itama dabira bata rintsa ba wato dai duk su ukun basu yi barciba amma wani ikon allah ita jaruma yazila batasan saadda barci yasace taba daf da lokacin daza ayi sallar asuba. Lokacin da aka idar da sallah a masallaci sarki ya waiga ko ina bai ga tsoho kasim ba sai jikinsa ya sake bashi lallai akwai wani boyayyen al amari a kansa don hak sarki na baro masallaci sai ya tura aka kirawo dabira yace da ita ta tafi izuwa dakin bako tsoho kasim ta fada dakin cikin shammace taga a halin da yake ciki domin baizo masallaci sallar asubaba lallai akwai wani abu na shin gaskiya a tare da shi. Domin tun da ya garin babu wanda ya ga yayi sallah koda jin wannan batu sai dabira tatafi izuwa dakin tsoho kasim a fusace wadansu dakarunta guda biyu na biye da ita. Tana sanye da hularta ta karfe. Da zuwan kofar dakin tsoho kasim sai tasa kafarta guda ta daki kofar. Take kofar ta burma ciki ta fadi kasa. Karar dukan kofar na yasa yazila ta farka firgigit! Kafin tayi wani yunkuri sai kawai taga jaruma dabira tare da dakartunta biyu tsaye akanta rike da makamai koda su dabira sukayi arba da yazila sai suka cika da tsananin mamaki. Gashi dai agefe daya kuma suka ga wannan tsufaffun kayan tsoho kasim ga layu da gurayen tsafi akansu sai al'amarin ya daure musu kai. Nan fa Dabira ta kurawa yazila ido tana tunani a zuciyarta. Abinda ya fadomata a rai shine, ta san fuskar yazila tun da sun gwabza yaki ba sau dayaba, amma bata taba yimata kallon kurilla ba sai yau. Tabbas dai yanzu ta gane cewa abokiyar gabarta ce tayi bad-da-kama ta shigo birninsu domin ta cutar dasu. Amma kuma me yasa a bokiyar gabar tata take kama da ita? Anya kuwa yazila ba ita ce 'yar uwarta ba? Ai waka abakin mai ita tafi dadi,bari naji daga bakinta. Nan take dabira ta dubi yazila tace, "wace ce ke, kuma meyasa kika batar da kamanninki kika shigo birninmu?". Koda jin wannan tambaya sai yazila ta bushe da dariya tace, "Nice jaruma Yazila babbar abokiyar gabarki! Kuma na shigo wannan birnin naku ne domin kawai nayi yakin karshe dake mu bambance tsakanin aya da tsakuwa!!!". Da jinhaka sai itama Dabira ta bushe da dariya sannan ta hade rai tace, "ke tsohuwar abokiyar gaba kiyi sani sani cewa kinka wo kanki GIDAN MUTUWA! Lallai bazamu kashekiba da azaba ko taron dangi ba, lallai nida ke zamu raba raini a yau dinnan. A matsayin ki na mai laifi, dole ne yanzu nasa a kamaki akaiki kurkuku a tsare ki inyaso yau da farkon yamma yammaci afito dake izuwa filin fada inda zamu fafata yakin karshe ni dake inda za arufe mu a cikin keji har sai dayanmu ya wanda duk ya rayu sai ya bude kejin ya fito. " Koda gama fadin hakan sai dabira ta dubi dakarunta dake tare da ita tace dasu su sawa Yazila ankwa sannan su tafi da ita kurkuku, Bisa mamaki sai dabira taga yazila ta tsaya kyam! Ansa mata ankwa a hannayenta da kafafunta batare da tayi wani yunkuriba sai murmushi kawai take har aka tusa keyarta a gaba aka tafi da ita. Al'amarin daya matukar jefata cikin tsananin mamaki kenan da wasi-wasi domin a sanin dabira yazila jarumace ta gaske ko ita kanta bata isa tasa mata ankwa ba cikin sauki, amma sai gashi dakarunta sunsa mata ankwar sun tafi da ita. Abin dabata saniba shine yazila tana sane ta saki jiki aka kamata saboda dalili uku. Dalili na farko shine tana son su fafata yaki domin dabira ta cire mata wannan laya dake wuyanta dalili na biyu shine tanason takai dabira kas har ta cire wannan hular karfe ta kanta domin taga kamanninta dalili na uku shine bata son dabira tace zata bita sutafi izuwa birnin kisra don daukar fansa akan sarki daksur shiyasa taki gayamata cewa ita yar uwartace ta jini Bayan an tafi da yazila izuwa kurkuku sai dabira ta tattara wadansu layu da guru na tsafi ta kunna musu wuta nan take suka kune kurmus ! Suka zama toka. Har tajuya zata fita daga cikin dakin sai taga jakar guzurin yazila a rataye ajikin bango kai tsaye ta nufi inda jakar take zata dauko ta duba abin dake ciki sai kawaitaji an kira sunanta. Tana waigowa sai taga ashe sarki raihan ne a tsaye da kansa. Sarki raihan ya dubeta fuskarsa babu walwala yace " yan zu kin daina fushi damuzaki iya sauraron bayanin dazan yimiki ?” Koda jin haka sai idanun dabira suka ciko da kwalla. Tace. ” Ka gafarceni yakai abbana. Kayi sani cewanima nayi nadamar nuna muku fishina. Ina fatan zaku gafarceni ? ” Koda jin wannan batu sai sarki raihan yayi murmushi yace. ” Babu komai yake. Yata yanzu dai kizo muje fada akwai wani gagrumin abu daya taso wanda zamu zauna mu tattau tare da sauran yan majalista hukuncin da kika yanke yanzu akan wannan abokiyar gaba tamu dataso ta yaudaremu yayi kyau ”. Koda jin haka sai dabira ta taho wajen sarki raihan ta ruke hannunsa suka jera suka fice daga cikin dakin ya zamana cewa gaba daya ta manta da batun wannan jaka ta yazila. Ita dai wannan jaka babu komai a cikinta face wadansu kayayyakin tarihi wadanda da zarar humaira tayi arba zata shaidasu. Domin kaya nena yar uwarta nuzaira wanda ayanzu haka tana da irinsu aajiye kuma kullum sai ta kallesu don tunowa da yar uwarta ta. Banda wadanda kayan tarihi kuma. Akwai rigarda aka sawa yazila aranda aka haifeta kuma dabira ma tana da irin rigar wacce har yanzu humaira nanan da ita aajiye don tarihi. Dabira ta sha ganin humaira tana dauko rigar tana kallenta kawai har tana kwallah amma duk saadda ta tambayeta dalili sai tace da ita kawai ta tuno wahalar data sha ne a lokacin data sami cikinta saadda ta haifeta. Lokacin da sarki raihan da jaruma dabira suka iso fada sai suka iske gaba dayan yan majalistar a zaune. Suna jiran karasowarsu al amarin daya razana dabira kenan domin ta san cewa duk saadda taga yan majilista sunyi irin wannan taro ya zamana cewa kowa ya zo to lallai akwai wani abu gagarumi al amari daya taso. Ko dai annoba ta barko. Ko kuma yaki zaayi. Da shigowar dabira da sarki cikin fadar sai suka je suka zauna inda suka saba zama. Zaman su keda wuya sai wazirin sarki Raihan yayi kyaran murya sannan yace, "yaku 'yan majalissar wannan birni namu mai albarka, da yawa daga cikinku sun san dalilin taruwarmu anan. Ga wadanda basu saniba, yanzu sai su sani. Wannan al'amari ba komai bane face a yau dinnan kimanin sa'a daya data shude mun sami rahoton cewar abokan gabarmu mutanen birnin kisra sun taho da zugasama da dakaru miliyan dari hudu da hamsin domin su yakemu. Wannan zuga ta hada da dakarun gudummawa daga sauran kasashen kafirai na wannan nashiya, kuma sun taho da alwashin cewa wannan karo adan za a shekara ana wannan yaki bazasu janyeba har sai sun tabbatar da cewa sun baje birnin mu sun kashe mazajenmu sun kama matayenmu da yaranmu a matsayin bayi sun kwashe dukkan dukiyoyinmu. Ku sani cewa adadin wadannan dakarun abokan gaba ya ninka namu sau goma, wato gaba dayanmu bamu wuce kaso daya ba a cikin kaso gomansu ba. Yanzu menene abinyi? Tabbas idan muka ce zamu fita mu tari waddannan abokan gaba za su iya murkushemu a cikin dakika kadan. " Sa'adda waziri yazo nan a jawabinsa sai Jaruma Dabira ta mike tsaye zumbur! A fusace, kuma ta zare takobinta a lokacin da jikinta ya kama tsuma. Cikin fushi ta dubi waziri tace, "yakai waziri kayi sani cewa bamu da wani karfi wanda yawuce karfin allah katuna cewa bayau ne karo na farko da muke fita yaki da abokan gaba da kuma ya zamana sun fimu yawa, amma sai kaga mun yi RAGAS dasu kokuma musami nasara akansu. Duk bawan da yayarda da allah kuma ya sallama al'amuransa a gareshi tabbas allah zai iya masa abinda ya gagareshi. Ina tabbatar muku da cewa koda abokan gaba yawansu ya kai cikin duniyar nan gaba daya idan ni kadai ce na rage musulma a wannan birni na rantse da girman Allah sai na fita na yakesu dan kare martabar addinin allah koda kuwa zasuyi gutsin-gutsin da sassan jikina. Na sani nan dagobe wadannan abokan gaba zasu iso kofar birninmu don haka zan jagoranci dakarunmu mufita mu yakesu wanda duk yake ganin zai bi bayana yabi, wanda ba zai bi ba yayi zamansa!". Koda dabira tazonan azancenta sai sarki Raihan ya zare takobinsa yace, "Ina bayanki ya ke 'yata, lallai dani za ayi wannan yaki gobe!". Koda ganin haka sai fiye da rabin 'yan majalissar ma suka yi abinda sarki raihan yayi. Kalilanne daga cikinsu basu yi hakan ba, domin sun gama tsorata da wannan yaki daza ayi, kuma imaninsu ya raunata. Wannan shine a binda ya faru a fadar sarki raihan bayan 'yan majalisar kasar sun yi taro na musamman. Al'amarin yazila kuwa, lokacin da aka kaita kurkuku aka kulleta sai taji ko kadan bata damu ba face kawai tana zumudin yamma tayi a fito da ita a kaita filin fada inda zasu yi yakin keji ita da jaruma Dabira. Har rana ta take Yazila ta kasa tsaye ta kasa zaune a cikin kurkukun. A lokacin ne aka kawo ma ta abincin rana. Ko kallon abincin batayi ba bare ma taci. Ai kuwa bayan an idar da sallar la'asar da kimanin rabin sa'a sai aka bude kofar kurkukun aka tasa keyar yazila izuwa fada. Tana tafe tana jan sarkar da aka daure kafafunta da hannayenta, dakaru na biye da ita. Lokacin da aka iso filin fadar da jaruma YAZILA sai taga filin fadar ta cika makil da jama'a fiye da kullum, harma mutane sun rasa inda zasu tsaitsaya sai akan katangau. A tsakiyar fadar kuwa, an ajiye wannan katon kejin karfe mai tsawo da fadi wanda aka yi masa 'yar karamar kofa ta shiga. A can gefe daya kuwa, sarki RAIHAN ne da 'yan majalisarsa a zaume kuma daf da shi JARUMA DABIRA ce a tsaye cikin gagarumar shigar yaki fuskarta a rufe cikin hular karfe kamar kullum. Koda aka ga anzo da YAZILA sai aka yi sauri aka bude kofar wannan keji. Cikin hanzari aka kwancewa yazila sarkokin dake hannayenta da kafafunta aka bata takobi sannan aka ingizata izuwa cikin kejin. Nan take Jaruma Dabira ma ta baro inda su sarki suke ta nufi inda kejin yake. Koda ganin haka sai fadar ta rude da kabbara aka rinka yiwa Dabira Jinjina har ta shiga cikin kejin aka rufe kofar kejin. A sannan ne aka yi tsit! A fadar gaba daya tamkar mutuwa ta gifta. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin jaruma Dabira da Jaruma YAZILA. Jaruma Dabira ta dubi yazila cikin murmushi tace, "yau mun hadu a inda babu damar gudu, kuma babu yankewar yaki face dayanmu ya sami nasara akan daya. Ina so ki sani cewa tuni na kona gaba dayan layoyinki da gurayenki na tsafi yanzu dame kuma za kiyi dogaro?". Koda jin wannan tambaya sai Yazila ta bushe da dariya tace, "ke yarinya, aikin kashe micijine baki sare kansa ba. Kin ga wannan laya dake wuyana wani malami ma'abocin addininku ne ya bani ita bayan an bashi dukiya mai tsananin yawa. Kuma ya tabbatar mini da cewa in dai ina tare da ita babu wani mahaluki daya isa ya sami nasara akaina ". Koda jin haka sai Dabira ta fusata ta zare takobinta ta afkawa yazila suka ruguntsume da azababben BAKIN ARTABU wanda ya dugunzuma hankalin kowa a wajen, domin su biyun babu wanda ke da alamun samun nasara akan abokin gwaminsa. WAYE ZAI SAMU NASARAR WANNAN GAGARUMAR HADUWA DA AKAI ? SHIN DABIRA ZATA CIRE LAYAR WUYAN YAZILA ITAKUMA TA CIRE HULAR KANTA? IDAN SUN SAMI NA SARAR HAKAN ME ZAI FARU ? YAUSHE ZA A KWABSA YAKI TSAKANIN RUNDUNAR BIRNIN KISRA DA RUN DUNAR BIRNIN MISRA? A WANNE HALI HUMAIRA MAHAIFIYAR DABIRA TAKE CIKI? SHIN DABIRA DA YAZILA SUNA GANO CEWA SU 'YAN UWAN JUNANE ? IDAN SUN GANO ZASU JE DAUKAR FANSA ABIRNIN KISRA AKAN SARKI DAKSUR? Muhadu a littafi mai suna BAKIN ARTABU don jin cigaban wannan kasaitaccen labari Alham dulillah a yau na kawo karshen littafin jaruma yazila 1-2-3 kamar yadda nagaya muku tun farko shine a hannuna ban sami cigaban saba amma idan na sami cigabansa zan kawo mukushi. JARUMA YAZILA Littafi na Uku Na Abdul'aziz sani madakin gini Created and design by:- SSuleiman zidane kd. WhatsApp 09064179602

1 Comments

Post a Comment