KISAN GILLA 1 COMPLETE

K


 IS AN GILLA
Littafi na Daya (1)
Complete Book
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing ... Suleiman Zidane kd....
Whatsapp 09064179602
.
Labari ya isowa AA Misau cewa...
MARUBUCIN YA RARA DA CEWA,
A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude anyi
wani babban birni mai suna madinatul haswar
a cikin daular larabawa
birnin madinatul haswar ya bunkasa a kan karfin
arziki girman kasa, karfin mayaka da yawan al umma
sarkin dake mulkin birnin madinatul haswar ya kasance adali mai tausayi da jin kan
talakawa ana kiransa da suna HISHAM IBN UBAIDA
.
SARKI HISHAM yana da matar aure guda daya jal mai suna
shamilat wadda ta kasance yar wani babban sarki mai
mulkin wata kasa da ake kira da hushush ana kiran wannan
sarki da SAHIBUL HILAYAT
sai da sarki hisham ya auri shamilat da shekaru goma sha daya sannan Allah ya
albarkace su da samun juna biyu nan fa sarki hisham da shamilat suka cika da tsananin farin ciki
domin
a duniya basu da wani buri wanda yafi ganin sun sami haihuwa saboda a shekarun
baya babu abin da basuyi ba, domin su sami
haihuwar amma abu ya gagara,
lokacin da mahaifin
shamilat ya samu labarin cewa 'yarsa ta sami juna
biyu sai ya kamu da tsananin farin ciki fiye da ita
kanta shamilat din da mijinta saboda shi kuma bashi da burin da yafi yaga jikansa
kafin ajali ya riske shi kasancewar tsufa ya
riske shi
a ko yaushe ta Allah zata iya kasancewa
Al amin Ahmed Misau, Guyson nake magana,
bisa wannan dalili ne sarki sahibul hilayat ya
tashi manzanni da dukiya mai yawa ya aiko su izuwa ga sarki
hisham yace ga wannan ayi
renon ciki kuma idan haihuwa tazo daf yana son
shamilat ta je gida ta haihu, yayin da wannan sako ya isa ga
sarki hisham sai hankalinsa ya dugunzuma domin
baya son ya rabu da matarsa dai dai da dakika daya
amma kuma yana matukar jin nauyin surukin nasa don haka
sai ya amince da hakan ita kuwa shamilat sai ta kamu
da matukar farin ciki saboda a rayuwarta babu abinda
take so sama da ta kasance tare da mahaifinta a ko yaushe
saboda ita kadaice 'yarsa a duniya
sarki Hisham yana da dan uwa yarima ZAMARU wanda
ya kasance azzalumi kuma mara imani mai tsananin son duniya
uwa daya
uba daya suke dashi da hisham, a zahiri yarima zamaru
yana nuna cewa yana matukar kaunar dan uwansa
sarki hisham amma a karkashin zuciyarsa babu
abinda ya tsana sama da shi ba wani bane ya haddasa
wannan gaba ba a tsakaninsu face kawai hassada da
kyashi da kuma tsananin son KARAGAR MULKI
TUN mahaifin su sarki hisham na raye ya futa cewa hisham
ne zai gaje shi daga
wannan lokaci ne yarima zamaru yaji ya tsani
dan uwansa sarki hisham ya fara tunanin hanyar
da zaibi ya kawar dashi daga doron kasa sau bakwai
yarima zamaru yana bayar da kwangilar a kashe
hisham amma yana kubuta kasancewarsa sadauki mai
dakawa maza gumba a hannu
Guyson nake magana Al amin Kenan
Lokacin da yarima zamaru yaga ya kasa ganin bayan
sarki Hisham sai ya
zuba ido izuwa lokacin da tsufa zasu riskeshi har
rai yayi halinsa
saboda ya tabbatar da cewa indai babu sarki hisham
dole shine zai hau karagar mulki, ana cikin wannan hali ne
na jiran lokaci kwatsam sai shamilat ta sami juna biyu
hm Al amarin da ya kara dugunzuma hankalin yarima zamaru kenan saboda ya
san cewa idan matar hisham ta haihu to fa
sarautar ta kara yi masa nisa, a ranar da zamaru ya sami labarin cewa shamilat
ta samu juna biyu sai ya kasa zaune ya kasa tsaye
har dare ya raba bai rintsa ba
Babban abinda ya kara jefa
shi cikin bakin ciki shine shima matarsa ba ta taba
haihuwa ba don haka duk ranar da ya mutu shi
kenan bashi da magajin mulki, cikin tsakar dare yarima
zamaru na kai kawo a cikin turakarsa ya kasa barci sai matarsa sarima ta farka
daga barci koda taganshi a tsaye yana kai kawo saita dube shi
cikin tsananin damuwa ta mike da sauri tasha gabansa
tana mai rike kafadunsa, tace yakai mijina menene
ya tayar maka da hankali a yau har ka kasa bacci?
Koda jin wannan tambaya sai yarima zamaru ya yi ajiyar zuciya sannan yace
baki da labarin cewa matar sarki ta samu juna biyu ne?
Sarina tayi ajiyar zuciya tace haba maigida yanzu
a kan haka ne ka tayar da hankalinka har ka kasa bacci koda jin haka
sai zamaru ya rufe sarina da fada yana cewa bata da
hankali bata da kishin rayuwarta,
sarina ta bushe da dariya sannan ta ce ka kwantar da hankalinka mijina ina so ka
sani cewa ni na san abinda ba ka sani ba idan har kana so ka san abinda na sani yanzu ka
tashi mu tafi izuwa can bayan gari wajan wani bakon boka da yazo
cikin alamun karayar zuciya yarima
zamaru ya dubi sarina yace ke nifa na gaji da maganganun bokayan nan
tunda an dade ana ruwa kasa na tsotsewa kuma na gaji da gafara sa har
yanzu banga kaho ba
Guyson nake magana, sarina tayi murmushi tace aiko bokaye
suna suka tara wannan bokan ya wuce yadda duk kake
tsammani duk wani bayani da zan yi maka ba zaka
gamsu ba don haka gani ya kori ji kawai kazo muje wajansa
yanzu a cikin wannan daren cikin sirri
koda jin wannan batu sai yarima zamaru ya cika
da farin ciki kawai sai ya mike zumbur ya kama shiri
yayi badda kama itama sarina yasa ta ta batar da kamanninta sannan sukayi
hawa suka fice daga cikin birnin madinatul haswar a sirrance ba tare da kowa ya shaida su ba
sai da suka yi tafiyar kusan rabin
Sa a sannan suka iso gaban wani katon dutse
wanda a kansa akwai wata yar karamar bukka
abinda ya daurewa yarima zamaru kai shine ganin matattakalar bene a kan dutsen tamkar sassake dutsen akayi
aka samar da ita shi dai
zamaru ya san wannan dutse sama da shekaru
talatin baya amma bai taba ganin wannan matattakala
a jikinsa
ba tabbas wannan matattakala aikin aljanu ne
bana mutum ba abinda zamaru ya ayyana kenan a cikin
zuciyarsa
bayan zamaru da sarina sun tsaida dokunansu a gaban dutsen sun sauka
sai suka daure dawakan nasu a jikin wata bishiya sannan suka taka
wannan matattakala suka hau kan dutsen
suna isa gaban wannan bukka sai sukaga bokan tsulum ya
bayyana a gabansu yana kyakyata dariya al amarin da ya dan razana yarima zamaru
kenan ya dan ja da baya kadan , shi dai wannan boka
ya kasance dogon mutum garjeje mai kirar mutanan
farko jikinsa gaba daya a murde yake alamar
karfi ta bayyana karara a tare da shi yana da yar
faffadar fuska kyakkyawa cike da kasumba da gajeran gemu
babu riga a jikinsa face wata fatar damisa
wacce ya yafata bisa kirjinsa ta zagayo izuwa bayansa
daga cikinsa zuwa gwiwoyinsa a rufe suke
da bante irin na fatar damisar da ya yafa kuma
takalmin dake kafarsa ma anyi shine da wannan fatar damisa
gaba dayan damatsansa na hagu dana dama a cike
suke da gurayen tsafi , tabbas wannan boka yana da kwarjini da cika ido kai da
ganinsa kasan cewa murucin kan dutse ne wato bai fito ba
sai da ya shirya
bokan ya dubi yarima zamaru yayi murmushi yace
kada kaji tsoro ya shugabana ni mai taimako ne a gareka
ko ince zamu yiwa juna taimako ku biyoni
izuwa cikin bukkata mu zauna domin mu tattauna sosai
koda gama fadin haka sai bokan ya juya ya shiga
cikin bukkar nan take yarima zamaru da sarina
suka bishi a baya ba tare da fargabar komai ba
da shigarsu cikin bukkar sai yarima zamaru ya sake cika
da tsananin mamaki domin kansa ne ma ya kusan juyewa
saboda ya tsinci kansa ne a cikin wata makekiyar fada wacce
ta kawatu ainun ninkin
fadar sarki hisham sau uku wadansu kuyangin aljanu sunata hidima da kai kawo
bokan yaci gaba da tafiya a tsakiyar fadar ya nufi inda karagar mulki take
su zamaru na biye dashi amma basu isa inda karagar mulkin take ba sai
da suka yi taku dari da arba in, da zuwa sai bokan ya zauna akan karagar mulki yarima zamaru da sarina kuwa sai kuyangin aljanun
suka kama hannayansu suka kaisu izuwa kan wadansu
kujeru dake daf da karagar mulkin suka zaunar
dasu
nan da nan aka kawowa yarima zamaru da sarina
ruwan inibi a cikin tambulan na zinare da
kofuna suka fara jika makoshinsu a sannan ne bokan ya dubi yarima zamaru a karo na biyu yace lale maraba
da yarima zamaru dan uwan hisham sarkin gobe
Al amin Ahmed Misau
Guyson Sunana Kenan
koda jin wannan batu zamaru ya natsu sosai
bokan ya ci gaba da bayani yana mai cewa
ka kwantar da hankalinka ya kai wannan dan sarki
kayi sani cewa matarka tazo nan kafin kai kuma
mune mukace ta kawo ka
mun san duk abin dake damunka da kuma burin dake
zuciyarka
tabbas mune zamu magance maka dukkan matsalarka muddin muma zaka bi umarnin
mu shin ka amince da wannan sharadi?
Koda jin wannan batu sai yarima zamaru ya dubi bokan cikin alamun rashin
fahimta sannan yace menene sharadin da kake so ka gindaya mun
bokan yayi murmushi yace ina so ka dauki
alkawari cewar idan bukata ta biya zaka raba birninka
biyu ka bani kaso guda na mallakeshi haka kuma zaka bani rabin dukkan
dukiyarka
lokacin da yarima zamaru yaji wannan batu sai
hankalinsa ya dugunzuma ainun ya rasa abin dake masa dadi yayi shiru yana tunani
bokan ya tuntsure da dariya alamun da ya janyo katsewar
tunanin yarima zamaru kenan ya dago kai a
firgice
ya dubeshi yace ni ne Hizainu ibin Markasi masanin sirrin gobe,
yakai wannan dan sarki ina so ka sani cewa babu wani
abu da mutum ke samu a saukake kuma a banza face
ya rasa wani abu
ina mai shawartarka daka dauki sharadina ni kuma na
taimaka maka na sanar dakai duk abinda zaka yi ka
samu biyan bukatarka kuma
yanzu ne kadai damarka
idan ka bari wannan dama ta wuce ka har abada ba zaka samu wata ba
sa adda yarima zamaru jai wannan batu sai ya kawo gwauron numfashi ya ajiye gami da ajiyar zuciya ya sake yin dan guntun tunani
sannan ya dubi boka
hizainu yace na yarda idan ka taimakeni burina ya cika zan raba mulkina da dukiyata
gida biyu na baka rabi amma bisa shardi guda
sharadin kuwa shine sai dai kayi rantsuwa da girman
tsafi da kuma darajar iyayenka cewar a gaba ba zaka yi yunkurin
rabani da mulkina ba
domin ka mallaki kasar gaba daya kuma ba zaka taba cutar
dani ba ko wani nawa
koda jin wannan batu
sai idanun boka hizainu suka zazzaro ya kamu da tsananin
mamaki saboda bai taba zaton cewa yarima
zamaru zai daureshi ba da jijiyarsa haka, al amarin da ya jefa
shi cikin shakku da wasu wasi kenan ya kama muzurai yana
kallon kuyanginsa dake kai kawo a cikin fadar suna hidama
sai da yayi dan tunani da nazari sannan ya bushe da dariya
nan take yayi rantsuwa da girman tsafi gami da darajar iyayansa bisa kan cewa ba zai taba neman
wani abuba daban a wajan yarima
Zamaru a nan gaba kuma ba zai cutar dashi ba koda jin haka
sai farin ciki
ya lullube yarima zamaru yace shima ya amince da bukatar
boka hizaunu
boka hizainu ya kyalkyala da dariyar murna yace
gobe da safe idan kaje fada zaka iske dan uwanka sarki hisha,
a kwance cikin cutar ajali kuma ba zai wuce kwana bakwai ba a kwance rai zaiyi halinsa
abu na biyu da nake so dakai shine a yanzu haka
matar sarki hisham ta haifi da namiji kuma har ta
gama wankan jego ta baro can birnin
darul hushush ta taho izuwa nan birnin madinatul
haswar tare da jaririnta da kuma dakaru dubu biyar masu tsaron
lafiyarta
wadanda suka kasance zakwakuran mayaka fasa taro lallai ka shirya
wadansu zakwakuran dakarun da suka fisu
jarumtaka wadanda zasu je su yake su su kashe matar
sarki ya zamana cewa baka da wata barazana a mulkinka ina mai
tabbatar maka da cewa a daren da dan uwanka sarki hisham
zai mutu ne shamilat da jaririnta
zasu iso cikin garin nan
don haka duk yadda zakuyi kusa a tare su a can cikin daji
kafin su iso kusa da wuri, kuma kada ka kuskura ka shiga
cikin mayakan da zasu je yin wannan aiki kuma ka
tabbatar da cewar anyi wannan aiki a cikin sirri
ba tare da wani ya sani ba lokacin da yarima zamaru
yaji wannan batu sai hankalinsa ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe ma ya dubi boka hizainu cikin alamun tsananin
tsoro da damuwa yace yakai wannan boka mai daraja
yanzu a ina zan samo dakarun da zasu iya kashe
dakarun da sarki sahibul hilayat masu yiwa shamilat da
jaririnta rakiya izuwa nan birninmu? Ka sani
cewa dakarun birnin darul hushush mayaka ne na asali kada su ba wasa bane
boka hizainu ya sake bushewa da dariya lokaci guda
kuma ya turbune fuskarsa yace babu wanda zai iya
yi maka wannan aiki face sarkin yakinka amzadu ibn karlyas
koda jin haka sai yarima zamaru ya cika da tsananin mamaki gami da tsoro yace
to yaya amzadu zai amince yayi min wannan aiki alhalin kasan cewa ya kasance
babban aminin sarki hisham wanda a shirye yake ya
sallama rayuwarsa domin kare ta sarki da iyalansa
koda jin haka sai boka hizainu ya sake bushewa da dariya
sannan yace
da zarar sarki hisham ya mutu kaine sarki komai
ya dawo karkashin ikonka da mulkinka
a wannan lokaci kana da ikon sarrafa komai da kowa da karfin karagarka
a daren da sarki
hisham ya mutu ka tura akamo sarkin yaki amzadu da iyalansa a matsayin kana zarginsa
da laifin sawa sarki wannan ciwon ajali tunda kowa ya
san cewa dare da rana yana tare da sarkin
bayan an tsare su a kurkuku shida iyalan nasa sai
kasa a fito dashi shi kadai azo dashi har cikin
turakarka ka kadaita dashi a sannan ne zaka gaya masa
bukatarka ta son ya
debi zakwakuran yaransa suyi
bada da kama suje su kashe matar sarki shamilat da jaririnta
da duk dakarun da sukayi musu rakiya
izuwa nan birnin madinatul hashwar idan
kuma yaki koyayi wani abu ba dai dai ba sabanin umarnin da ka bashi
zakasa a kashe iyalansa idan kuma yayi aikin daidai
bisa nasara zaka bashi babban matsayi a fadarka fiye
da wanda yake da shi a yanzu.
Suleiman Zidane kd kenan.....
lokacin da boka hizaunu yazo nan a zancensa
sai yarima zamaru ya kamu da tsananin farin ciki
nan take ya kama kyalkyala dariya saboda murna sannan ya dubi boka huzainu yace
yakai wannan boka mai daraja hakika ka cika makiru uban masharranta na duniya
Hm
babu makawa wannan dabara taka saita yi nasara
shin yanzu ka tabbatar mini da cewa idan na koma gari zan iske sarki ya kwanta cutar ajali
koda jin wannan tambaya sai boka huzainu yayi murmushi yace yau fa
shekara bakwai kenan ina shiri da jiran zuwan wannan
rana saboda me ma zaka rinka shakku bisa furucina ku koma
gida kuje ku sha barcinku a cikin wannan dare lallai gobe da safe za a yi kiranka izuwa fada kaga zahiri
nan take yarima zamaru da sarina matarsa suka yi wa boka
hizaunu sallama suka fito daga cikin gidan nasa suka hau dawakansu suka koma
cikin birnin madinatul hashwar ba tare da wani ya shaida suba akan hanya
.hakika masu iya magana sunyi dai dai da sukace
tsafi gaskiyar mai shi kuma maso abinka yafika dabara
Kashe gari kuwa da sassafe aka tashi manzo daga gidan sarki ya ruga izuwa gidan yarima zamaru ya sanar
dashi cewar ya rugo izuwa gidan sarauta ana nemansa yanzu yanzu
a majalisa koda jin wannan batu sai yarima zamaru
ya dubi manzon cikin alamun tsananin mamaki
da tsoro yace lafiya ake namana a fada
da sassafen nan haka
Manzon ya risina yace ai sarki ne ya kamu da wani irin ciwo
farat daya ko mikewa zaune ma ya kasa, koda jin
haka sai yarima zamaru ya dimauce ya ruga da gudu izuwa cikin turakar matarsa
sarina
da shigarsa ya iske sarina a kwance tana shirin tashi
kenan
nan take ya labarta mata labarin da manzo yazo dashi
dajin haka sai sarina ta mike zumbur daga kan gado ta daka tsalle ta rungume
zamaru
tana mai kyalkyala dariyar murna tana cewa shi kenan
bukatar mu ta biya
nan dai zamaru yayi sauri ya kintsa sannan ya
bi manzo suka wuce izuwa gidan sarauta
da isar su ya wuce kai tsaye izuwa cikin turakar
sarki inda ya iske sarki hisham a kwance bisa gado fuskarsa ta cika
da wadansu irin kuraje babu kyan gani
ga likitoci da manyan bokayan garin nan
sun taru a tsaitsaye a gefen gadon
a daya bangaren kuwa gaba dayan yan majalisar
sarkine a zazzaune suma sunyi jigun jigun cikin alamun tashin hankali
koda shigowar yarima zamaru sai sarki hisham ya
dubi yan majalisarsa da dukkan likitocin sa da bokayan
nasa har dama duk hadimansa
dake cikin turakar yace kowa ya fita ya barsu yana son
ya gana da dan uwansa zamaru
a wannan lokaci sarkin yaki amzadu na zaune daf da sarki ya rike hannayan
sarki yana ta zubar da hawaye kuma ya kurawa
sarki hisham idanu kodajin umarnin da sarki ya bayar sai
kowa ya fice daga cikin fadar amma shi sarkin yaki amzadu saiya kasa mikewa
ya fita har saida sarki ya dubeshi ya budi baki yace yakai babban masoyina ka
sani cewa a rayuwata ban taba boye maka wani al amarina ba saboda
kauna da yardar dake tsakaninmu amma yau kuma bana son ka san wani babban sirri dake tsakaninmu da dan uwana
zamaru
saboda uwa daya uba daya ya wuce wasa don haka ina son ka fita ka bamu wuri
koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke sarkin
yaki amzadu domin irin haka bata taba faruwa ba
tsakaninsa da sarki
cikin sanyin jiki ya mike tsaye yana waigen sarki yana
zubda hawaye ya fice daga cikin turakar
kuma ya janyo musu kofa ya rufe
ta
faruwar hakan keda wuya sai sarki hisham ya dubi yarima
zamaru ya yafito shi da hannu ya sake budar baki da kyar
yace
matso nan kusa dani ya kai dan uwana rabin jikina
cikin nuna alamun tsananin damuwa har idanun
na zubar da hawaye zamaru ya je ya zauna agefen
gadon sarki daf dashi suka kurawa juna idanu
har izuwa tsawon yan dakiku
sannan sarki ya dubeshi yace
yakai dan uwana kayi sani cewa a daren jiya na kamu da wannan cuta farat daya
kuma likitocina da bokayena sunyi iya bakin kokarinsu akan
su gano abinda ya haddasa wannan cuta da maganinta sun kasa, tabbas jikina
ya bani cewa
mutuwa zanyia cikin yan kwanaki kalilan
ka sani cewa bani da wani makusanci wanda yafika sai kuma matata shamilat da abinda ta haifa
tuni mahaifin shamilat sarki sahibul hilayat na birnin darul hushash ya aiko da manzo
cewar shamilat da jaririnta data haifa sun taho nan birnin bisa
rakiyar dakarunsa kuma zasu iso a daren kwanaki bakwai masu
zuwa
koda sarki hisham yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubo masa yaci
gaba da cewa
a duniya bani da wani buri wanda yafi naga dana na cikina
wanda ban same shi ba sai bayan na shafe shekaru
goma sha daya dayin aure amma gashi burina ba zai cika ba
domin ina ji
a jikina cewar kafin shamilat ta iso garinnan ajali ya riskeni
Al amin Ahmed Misau, guyson nake magana
koda jin haka sai yarima zamaru ya rungume
sarki hisham yana mai fashewa da kuka yace yakai
dan uwana kayi sani cewa dukka mai rai baya
fidda tsammani rabo kuma babu wata cuta wadda bata
da magani a doron kasa don haka ni yanzu ina so ka bani dama na
garzaya izuwa makotan kasashenmu na nemo maka magani
koda jin wannnan batu sai sarki hisham ya busheda
dariya cikin
Matukar karfin hali da juriya, al amarin da yayi
matukar baiwa
yarima zamaru mamaki da tsoro kenan yaji a ransa
kamar sarki ya gane cewa yana da masaniya a kan
wannan ciwo da ya same shi, lokaci guda kuma sai yaga sarki hisham ya fashe da matsanancin
kuka na bakin ciki
da kyar zamaru ya rarrasheshi yayi shiriu
sannan ya dube shi yace yakai dan uwana tunda na hau
kan karagar mulki ban taba kamuwa da ciwon da ya kaini
ga kwanciya ba sai jiya fruwar hakan ce ta tabbatar mini da cewar nesa ta
matso kusa ina so ka sani cewa ba wani abu bane ya sa na sallami
kowa daga cikin dakin nan ba sai domin muyi wani sirri
guda daya wannan sirri ba komai bane face ina son na roke ka wata alfarma guda daya
ka sani cewa rayuwa ban taba tauye wani hakki naka ba
a matsayinka na kanina kuma baka taba neman wani abu a wajena ba wanda banyi maka shi ba tun daga kuruciyarmu
kawo izuwa girmanmu a lokacin da mahaifinmu ya ke raye da kuma ya mutu
koba haka bane?
Yarima zamaru ya gyada kai a lokacin da hawaye na gaskiya ya zubo masa
domin take yaji tausayin sarki hisham ya ratsa jikinsa
saboda sanin cewar gaskiyar ya fada sai yace
hakika ka fadi iyakar gaskiya yakai dan uwana
sarki hisham yayi dan guntun murmushi sannan yace
ni kuwa ban taba neman wani abu ba a wajanka kuma ka taba saka mini da kwara zarra ba koda karfin jikinka
bisa duk irin abubuwan alherin da nayi maka a rayyuwa
zamaru ya gyada kai yana mai nuna alamar haka ne
sarki hisham yaja dogon numfashi sannan yace alfarmar da nake nama a wajanka itace
idan har matata ta iso birnin nan a raye ita da jaririnta
kada ka sa a kashesu ko a boyesu a wani wuri bisa
tsoron nan gaba zasu iya rabaka da mulkinka
idan har ba zaka iya zama tare dasu ba kamar yadda na zauna tare dakai tsawon shekaru talatin alhalin na san
cewa baka kaunata ka tsaneni kamar yadda ka tsani mutuwarka
saboda karagar mulki
ina son ka tura su izuwa can kauyen limras su karasa sauran rayuwarsu a can a matsayin talakawan gari
kawai koda ba zaka taimaka musu da komai ba
na san wacece matata shamilat macece mai zuciyar maza ko
babu aure zata iya rike kanta kuma tare da abinda ta haifa
Guyson Sunana
Koda sarki hisham yazo nan a zancensa sai hawaye ya sake zubo masa a lokacin da ya kurawa
yarima zamaru idanu
nan take yarima zamaru yaji ya kamu da tsananin kunyar sarki hisham gami da
matukar tausayinsa har shima hawaye ya sake zubo masa
kawai sai yarima zamaru ya mike tsaye ya juyawa sarki hisham baya yace nayi alkawar idan har matarka da abinda
ta haifa sun shigo cikin garinan a raye lallai
zan zamo mai rike su da amana kamar yadda ka
rikeni har izuwa sa adda mutuwa zata rabani dasu
koda
gama fadin hakan sai yarima zamaru ya fice daga cikin turakar yana kuka da fitowarsa yana kuka yayi arba da sarkin yaki amzadu
a tsaye shi kadai a kofar dakin nan fa sukayi wani irin kallo kallo na rashin yarda kawai sai
yarima zamaru ya yiwa amzadu dan guntun
murmushi yyi tafiyarsa shi kuma sai ya bude kofar turakar
da sauri a dimauce ya shiga ciki
da shigarsa yayi arba da sarki
a kwance kamar yadda ya fita ya barshi dazu
cikin hanzari sarkin yaki amzadu yaje ya sake zama daf da sarki ya dubeshi a
firgice yace
ya shugabana me ya faru tsakaninka da dan uwanka na ga shima ya
fita yana kuka
koda jin wannan tambaya sai sarki hisham yayi dan guntum murmushi cikin
matukar karfin hali sannan yace Alhini ne na rabuwa
da juna ya sakaga duk muna kuka
domin mutuwa zata shammace
mu a lokacin da bamu taba zato ba tafi na sallame ka
wasiyata ta karshe a gareka ita ce ka tuna da duk
irin abubuwan alherin da nayi maka a rayuwa
a duk sa adda wata masifa ta taso kada ka kasance mai
yin butulci a bayana
sa adda sarkin yaki amzad yaji wannan batu daga bakin sarki sai ya kamu
da tsananin
mamaki kuma ya kasa fahimtar abinda yake nufi har ya budi baki da nufin ya sake
tambayarsa sai ya kasa
nan dai ya juya ya fice daga cikin turakar cikin tsananin
damuwa da tashin hankali wanda bai taba tsintar
kansa ba
.
Daga wannan rana sarki hisham ya ci gaba da ciwo wanda
ba sauki kuma babu alamar za a sami saukin
har saida ta kai cewa ko motsi da baki baya iya yi
abinci ma da ruwa idan aka dura masa baya shiga cikinsa
a ranar kwana na bakwai ne ciwon ya tsananta
ainun
hankalin kowa ya dugunzuma a tsawon kwanaki bakwan da sarki hisham ke kwance
cikin jinya yarima zamaru bai sake zuwa ya duba shiba
amma sarkin yaki Amzad kuwa dare da rana yana tare dashi
a ranar kwana na bakwan da magariba rai yayi
halinsa nan fa labari ya bazu a ko ina cikin kasar mutane
suka kama koke koke sai a wannan lokacinne aka
ga yarima zamaru ya shigo cikin fadar a lokacin da aka fara shirye shiryen binne
sarki ana ganin yarima zamaru hankalin kowa ya tashi
domin an san cewa dolene yanzu komai ya
sauya a birnin duk irin adalcin da ake yiwa talakawa
an daina kuma za a matsa musu a kan biyan haraji mai yawa za a rinka zaluntarsu
babu sauran masu jin dadi da kwanciyar hankali
face sarakai da attajirai wadanda zasuyi biyayya ga sabon sarki Yarima zamaru
nine dai Al amin Ahmed misau
Guyson nake
Bayan an gama jana izar sarki hisham an binne shi a cikin dakin da aka binne
sarakuna arba in da uku na
kasar sai yarima zamaru ya tara gaba dayan yan
majalisar kasa a dakin taro ya tabbatarmusu da cewa
gobene za ayi bikin nadin sarautarsa sannan kuma ya umarci sarkin yaki da ya tabbatar da tsaro a ko ina
a cikin birni da kewaye kuma ya sanar da dakarun dake tsaron
kofofin gari cewa ba shiga kuma ba fita daga yanzu har izuwa gobe sa adda za a kammala bikin nadin
sarautar tasa
koda jin wannan umarni sai kowa ya cika da tsananin mamaki
amma sai gaba daya yan majalisar sukayi shiru suna masu sunkuyar da kansu kasa saboda
tsoron yarima zamaru aka rasa wanda zaice kala sai sarkin yaki amzadu
ne ya dubeshi yace yakai sarkin gobe kayi sani
cewa wannan hukunci da ka yanke baiyi dai dai ba domin tsarin mulki bai yarda da hakan ba saboda bai dace ba ka
hana mutane zuwa cikin gari nan ba koda ka hanasu
fita a wannan lokaci da ake ciki na babban rashin da akayi na dan uwanka
ka sani cewa mutane da yawa zasu zo ne domin
su ziyarci kabarin sarki su nemi tabarrakinsa kuma suyi masa addu a wasu kuma zasu kawo ziyara ne izuwa
kallon bikin nadin sarautarka,
sarakuna da yawa daga makwabtan kasashe ma zasu zo wannan gagarumin biki
kafin sarkin yaki amzad ya gama rufe bakinsa tuni yarima zamaru ya tari numfashinsa
yana mai daaka masa tsawa yace wanene kai harda zaka gaya mini abinda zanyi
ka sani cewa in banda kana da matukar muhimmanci
da amfani da yanzu take zan sauke ka daga kan mukaminka
na sallameku kowa ya kama gabansa nan take kowa
ya kama gabansa jikinsa a sanyaye ya fice daga cikin dakin taron
aka bar yarima zamaru a zaune shi kadai
Al amin Guyson, lokacin da sarkin yaki amzad ya isa
kofar gidansa sai ya hango kofar gidan wayam babu dakarun
da suke yi masa gadi kuma kofar gidan a bude take wanwar al amarin da yayi matukar razana shi kenan yayi wuf ya sauko
daga kan dokinsa yana mai zare takobinsa kawai sai ya ruga da
gudu izuwa cikin
gidan yana mai kiran sunan matarsa
da danta himar wanda ya kasance yaro dan shekara
hudu amma shiru baiji sun amsa ba kuma baiji duriyarsu ba
,,,
Zidane kd...
Yana isa falo yayi turus saboda tsananin kaduwa
da mamaki bisa abinda yayi arba dashi ba wani abu ya gani ba face
yarima zamaru zaune akan
kujera cikin shigar yaki ya harde kafafu daya kan daya yana kallonsa cikin murmushi abuna farko da ya daure masa kai shine
yaya akayi zamaru ya riga shi zuwa nan alhalin a can gidan sarauta
ya barshi kuma yaushe ma ya canja kayansa har yazo nan din kawai sai amzad ya baiwa kansa amsa
yace tabbas wannan al amari ne na tsafi cikin alamun
fushi sarkin yaki ya dubi yarima zamaru yace ina iyalina
tuni
jikina ya bani cewar wani abu makamancin wannan sai ya
faru kuma yanzune na tabbatar da cewar kana da hannu
a kan ciwon da sarki ya samu wanda ya zama sanadiyar
ajalinsa
lokacin da yarima zamaru yaji wannan batu sai ya bushe da mahaukaciyar dariya
lokaci guda kuma ya turbune fuska yace ina son mutum mai
kaifin kwakwalw
da hasashe irinka
tabbas duk abinda ka fada haka yake gaskiya ne nine na
kashe sarki domin na sami wannan karagar mulki
wacce ta gagareni tsawon shekaru
ban zo nan domin muyi doguwar magana nazo ne domin na sanar dakai
cewar iyalinka suna hannunmu kuma mun boye su a inda babu wanda ya isa
ya gansu ko ya dauko su face mu da kanmu ina son
yanzu take ka debi dakaru dubu dari shida a cikin shigar badda kamanni ku nufi
jeji na bayan gari ku tari gimbia shaliat tare da dakarun mahaifinta
wadanda sukayi mata rakiya izuwa nan birnin
ina son duk yadda za ayi ka kashe su gaba dayansu
ban son mutum daya ya tsira
da jaririn da ta haifa ku tabbatar da cewa kun kashe shi idan kuka yi wannan aiki
dai dai zan dawo maka da iyalinka gobe da safe idan kuma ka ki bin umarnina gawar iyalanka zamu kawo maka
idan kunne yaji gamgar jiki ya tsira
kuma shawara ta rage ga mai shiga rijiya
Koda gama fadin hakan sai yarima zamaru yayi
girgiza ya bace bata daga cikin dakin yana mai
kyalkyala dariya tamkar bai taba wanzuwa ba a ajan
Al amin Guyson nake
nan fa sarkin yaki amzad ya dimauce
kuma ya fusata ainun bai san sa adda ya kurma uban ihu ba kuma ya fashe da matsanancin kuka
saboda tsananin bakin ciki da takaici daga can sai ya juyada sauri a guje ya koma
kofar gida ya kama dokinsa ya hau ya zabureshi da gudun tsiya
A can daji kuwa Gimbia shamilat na zaune a cikin keken
doki
rungume da jaririnta dakaru sun kewayeta gaba da baya
dama da hagu ana tafiya saboda kwarjinin wadannan dakaru da irin kayan yakin da suke dauke dasu
babu abinda zai gansu bai yi shakkarsu
ba , da yake duhu yayi gaba dayan dakarun sun kunna fitilun itace don haka hanya sai tayi haske
sai sauri ake
tayi saboda an san cewa saura baifi tafiyar rabin sa a ba
a iso cikin birnin madinatul hashwar
a wannan lokacinne shamilat na cikin tsananin farin ciki
sai yawan kallon
jaririnta take yi tana murmushi saboda tunanin cewa a yau ne sarki hisham zai ga dan cikinsa da idonsa abinda ya shafe shekara da shekaru yana burin gani
bai gani ba
saboda zakuwar da tayi taga an isa cikin garin har umarni take bayarwa a kan a karawa dawakai kaimi
nan fa aka ci gaba da gudu kai kace hari za a kai
kaico rashin sani yafi dare duhu ashe
wadannan zuga ba su san cewa mahallaka suke kai kansu ba lokacin da tawagar
gimbiya shamilat suka iso
dai dai wani fili mai fadi wanda tsakaninsa da karshen dajin bai wuce zira i arba in ba
sai kawai sukaji ana yi musu ruwan kibiyoyi ta gabas da yamma kudu da arewa wayyo Ajali idan yayi kira sai an amsa
babu makawa
Nan fa dakarun da dawakai suka rinka ihu da haniniya suna zubewa kasa matattu kafin su ankara an kashe kaso daya a cikin kaso uku
ita kanta gimbiya shamilat taga matukar tashin hankali domin ta gefen idanunta da kunnuwanta kibiyoyi
suka rinka giftawa da kyar aka sami wasu zakwakuran mayaka suka rinka kade kibiyoyin
da ake harbo mata da takubbansu
A sannan ne kuma dakarun suka yi wata dabara
wadanda keda
garkuwoyi sai suka yi kawanya a tsakiya suka kare sama da kasansu
aka sanya gimbiya shamilat da sauran dakarun a tsakiyar da irar duk da haka sai aka ci gaba da harbo kibiyoyin
har zuwa tsawon lokaci
a wannan lokaci jaririn shamilat na ta faman kuka itama gimbiya tana kukan sai da aka saina harbo kibiyoyin
sannan shugaban dakarun ya dubi gimbiya shamilat yace
ranki ya dade yanzu me ye abinyi
ba muga wadanda suka kawo mna wannan hari ba
har yanzu domin sun boye ne a cikin duhuwar bishiyoyi
shin zamu ci gaba da tunkarar birnin madinatul hashwar ne
wanda tazararmu da shi a yanzu bata wuce zira i arba in ba ko zamuyi kokarin komawa da baya ne
domin mu tserar da rayuwarki data wannan yaron naki
sa adda shugaban dakarun yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubowa gimbiya a lokacin da zuciyarta ta buga da karfi
kuma tsoro ya shigeta kawai sai ta dubi shugaban
dakarun ta ce sarki Hisham ya fadi ''
cikin kaduwa shugaban dakarun ya cubeta yace
ranki ya dade ya akayi kika sani?
Shamilat ta fara zubar da hawaye ta ce inda
mijina yana raye babu yadda za ayi a taremu a kan iyakarsa
domin a hallakamu
abu ne mai hadarin gaske muci gaba da tunkarar
cikin birninnan yanzu kawai muyi
Kokarin komawa da baya in munyi sa a mu tsira da ranmu
kafin gimbiya ta gama rufe bakinta sai kawai
sukaji sukuwar dawakai an durfafosu kafinsuyi wani
yunkuri dakarun masu yawan gaske ninkinsu uku sunyi musu kawanay
gimbiya shamilat ta fito daaga cikin keken dokinta a fusace
rike da jaririnta domin taga ko suwaye ne wadannan dakaru da suka kawo musu hari
kawai sai taga ashe dakarun sunyi shiga ne irin ta
bakaken kaya ba shigar kayan yakin dakarun birnin madinatul hashwar ba kuma duk
sun rufe fuskokinsu da bakin kyalle idanunsu kadai ake gani
a dai dai wannan lokaci ne shugabam dakarun gimbiya ya rugo gareta ya dubeta
cikin alamun tsananin tsoro da damuwa yace
haba ya shugabata yaya zaki fito fili haka gaban wadannan makiya
alhalin muna kare rayuwarki da ta jaririnki
shamilat tayi ajiyar zuciya tace ai zancen kare ni da
jaririna ya kare ka dubi wadannan dakaru ka gani ai sarkin yawa yafi sarkin karfi kuma ba zamu iya guje musu ba
duk mutuwa zamuyi ni kawai
yanzu ina son na san wanda ya turo a kasheni kafin na mutu
Al amin Guyson Sunana
don bana son na mutu cikin wasu wasi
koda gama fadin hakan sai gimbiya shamilta ta dubi wadannan dakaru masu bakaken tufafi
ta daka musu tsawa tace ku su waye kuma waye ya turoku ku kasheni
mtar sarkin birnin madinatul hashwas
dajin wannan tambaya sai bakaken dakarun suka dare
shugabansu ya ratso ta tsakiyarsu ya matso kusa da ita ya tsaya
duk da cewar fuskarsa a rufe take idanunsa kadai ake gani saida gimbiya shamilat ta shaida ko wanene shi nan take hawaye ya zubo daga cikin idanunta
ta dubeshi tace yakai Amzad yanzu dakai za a hada baki aci amanar mijina
Yanzu ashe dama zaka iya yiwa sarki butulci aashe zaka iya mancewa da duk
irin halaccin da yayi maka a rayuwa
sa adda shamilat tazo nan a zancenta sai sarkin
yaki Amzad ya kwaye fuskarsa sai ga hawaye na zuba masa a lokacin da suka kurawa juna idanu shi da ita
tsawon yan dakiku dayansu baice
uffan ba sannan Amzad yace ki gafarceni ni ya shugabata idan ban bi umarni ba nima zan rasa matata da dana
Koda jin haka sai shamilat ta fashe da kuka tace
haka ne rai baifi raiba amma kafin ku kashe mu
ina son ku fada mun iyakar gaskiyar menene ya faru ga mijina
dajin wannan tambaya sai hawaye ya sake zubowa sarkin yaki amzad ya ce mijinki ya mutu
koda jin haka sai jiri ya debi shamilat ta yanke jiki zata fadi kasa
cikin zafin nama amzad ya daka tsalle ya dira a gabanta ya tallafeta tare da jaririnta yana mai baiwa dakarunsa umarnin su hallaka dakarun gimbia
kaico Ajali ba a sa ma rana nan da nan dakarun amzad suka kama ragargazar dakarun shamilat
wuri ya hargitse banda ihun mazaje babu abinda mutum ke ji
duk da cewar sarkin yawa yafi sarkin karfi sai da aka jima ana gumurzu a karshe dai ragas aka yi aka karar da gaba dayan daakarun
kowanne bangare ya zamana cewa babu daya da ya rage a raye face
sarkin yaki Amzad a dai dai wannan lokaci ne gimbia ta farfado daga dogon suman da tayi idanunta suka bude tana mai gani
dishi dishi idanunta na washewa tayi arba
da sarkin yaki amzad a zaune daf da ita rungume da jaririnta
gaba dayan dakarun dake wajan na kwance a kasa sun zama gawa
shamilat ta mike tsaye zumbur ta rugo iduwa wajan amzad ta miko hannayanta
da nufin ta karbe jaririnta amma sai ya tokare da kotar takobinsa a kirjinta yace ya shugabata
kiyi sani cewa yarima zamaru ya umarceni da na kashe ku keda jaririnki in ba haka ba kuwa sai ya kashe matata da dana ba zan iya kashe ku ba
domin idan nayi haka naci amana
Koda yazo nan a zancensa sai ya durkusa bisa gwiyoyinsa agaban shamilat a lokacin da idanunsa suka
ciko da kwalla yace ina rokonki daki bar garin nan kuma karki koma birnin darul hashbush ki sanar da mahaifinki abinda ya faru
domin kina gaya masa zaice zai yaki sarki zamaru kuma kin
sani cewa mayakan mu sun ninka nasa sau goma a yawa da karfin makamai
cikin tsananin bakin ciki shamilat ta fashe da kuka
kamar ba zata daina ba daga can saita dago kai idanunta sunyi sharkaf da hawaye tace shi kenan ka bani dana nayi alkawarin
zan tafi izuwa wata nahiyar daban na reni dana a can har
abada ba zan dawo nan ba kuma ba zan taba gayawa dana matsayinsa ba
koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa sarkin yaki amzad ya dubeta yace
ba zan iya baki yarima ki tafi dashi ba
cikin razana shamilat tace yanzu kana nufin zaka rabani
da dana kenan wanda shi kadai ne abinda ya rage mini a duniya
amzad yace
kawar kuwa domin barinsa awajanki ba karamin hadari bane nayi miki
akkawari zan reni wannan yaro a cikin birnin madinatul
hashwar
kusa da karagar mulkinsa ba tare da ya san ko shi wanene ba
kuma komai dare dadewa in dai kina raye yana raye nima ina raye saina sadaku
zan tsare lafiyarsa da ransa kamar yadda na tsare na mahaifinsa wannan shine kadai
gatan da zamu iya yiwa kanmu da wannan jariri
naki idan har muna son mu tsira da rayukanmu
sa adda sarkin yaki amzad yazo nan a zancensa sai shamilat ta sake
fashewa da kuka daga can sai ta matso daf da amzad ta shafa kan jaririn ta sumbaci goshinsa sannan kuma ta ciro wata laya dake wuyanta ta
Daurata a wuyan jaririn ta dubi amzad tace
ina da laya irin wannan sak don haka ka gayawa dana
cewar duk ranar da yaga mai irin wannan laya ba wata ba
ce face mahaifiyarsa
koda gama fadin hakan sai ta karbi jaririnta ta rungumeshi
a kirjinta ta sake fashewa da kuka al amarin da ya karyar da zuciyar sarkin yaki kenan ya ji ya kamu da tausayinta fiye da ko yaushe
sai da ta jima a kankame da jaririn sannan sarkin
yaki ya karbeshi ta tafi izuwa inda keken dokinta yake tana waigen jaririn nata
tana zubar da hawaye
Wow nIma Al amin Guyson na tayata haka dai taje ta zauna a kan keken dokin
ta sakarwa dawakan linzami suka zabura da gudu suka nausa da ita cikin
daji suka nufi wani bangare daban wanda bai shafi nahiyar ba gaba daya
a sannan ne shima sarkin yaki Amzad ya tafi da jaririn izuwa inda dokinsa yake ya kama ya hau ya nufi
hanyar da zata kai shi cikin madinatul hashwar
a lokacin da yake bacewa a cikin duhun daren
tun kafin sarkin yaki ya iso kofar shiga gari ya boye jaririn a bayansa tamkar baya dauke da komai kawai ya wuce gaba masu gadin kofar garin
ba tare da jaririn yayi kuka ba
ai kuwa yana isowa bakin kofar sai masu gadin suka tare shi saboda basu gane shiba
sakamakon yana sanye ne da bakaken kaya kuma basu ga sa adda ya fice daga cikin garin ba tare da dubun nan daakarunsa saboda ta wata barauniyar hanya suka fice
masu gadin na tare shi sai yayi sauri ya bude
fuskarsa don kada su bata masa lokaci koda suka dallare fuskarsa da madubi
sukaga shine sai suka yi sauri suka bude masa kofa ya shigo suna masu binsa da kallo cikin alamun tsananin mamaki domin su dai basu ga lokacin da ya fita daga cikin garin ba kuma tunda suka ganshi a cikin shiga ta
bakaken kaya lallai sun san cewa wani aiki ne na sirri yaje ya gabatar
amzad na shiga cikin gari bai zame ko ina ba sai gindin wata karuwa wacce ake kira kimaratu
a wannan lokaci dare ya fara nisawa kuma sawu ya dauke ba a jin sautin komai face haushin karnuka amzad ya kama buga kofar gidan da karfi
a fusace kimaratu tazo ta bude kofar tace wanene nan yake neman fasa mini kofar gida ka kama gabanka
ina da abokin kwana a ciki
koda jin haka sai amzad ya daka mata tsawa yace bude kofar na shigo nine
sarkin Yaki Amzad
jikin kimaratu na karkarwa tayi sauri ta bude kofar nan take amzad ya mika mata
jaririn sannan ya danka mata jakar
kudi
cike da dinare yace wannan kudine dinare dubu dari uku ki rike su ki reni wannan jariri har izuwa lokacin da na bukaceshi
idan wani abu ya tafa lafiyarsa a bakacin ranki
.
SHIN SARKI ZAMARU ZAI CIKA ALKAWARIN DAKE TSAKANINSA DA BOKA HIZAINU.??
.
YAUSHENE SHAMILAT ZATA SAKE GANIN DANTA???
.
ME ZAI FARU IDAN DAN SHAMILAT YA GIRMA ???
.
MU HADU A LITTAFI NA BIYU
DON JIN CI GABAN WANNAN LABARI
DAGA MARUBUCIN LITTAFIN
ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI KANO
WANDA NI Suleiman Zidane kd nake kawo muku domin samun wasu littafan kuyi min magana ta whatsapp ta number nan.......
09064179602

Post a Comment (0)