*MAKARANTAR AZUMI 018* //
📌 SAHUR
Allah Ya wajabta mana Azumi ne kamar yadda aka wajabta shi akan waɗanda suka gabace mu daga cikin Ma’abota Littafi (Yahudu da Nasara), Allah maɗaukaki Ya ce: ( *(Ya ku waɗanda kukayi Imani, an wajabta muku Azumi kamar yadda aka wajabta shi akan waɗanda suka gabace ku don ku zamo masu tsoron Allah)* ) Suratul Baqarah: 183
Sai ya kasance lokacin da hukuncin yayi daidai da yadda aka wajabta shi akan ma’abota littafin, cewa kada su ci, kuma kada su sha, kada su sadu da matan su bayan sunyi Bacci. Wato idan ɗayan su yayi Bacci da Daddare to ba zai ƙara cin komai ba, sai wani daren ya zagayo, sai aka wajabta wa Musulmi wannan hukunci, to da aka shafe wannan hukunci, sai Manzon Allah (SAW) Ya Sunnan ta Sahur domin bambance tsakanin Azumin mu da Azumin ma’abota Littafi, domin a cikin shi akwai albarka kuma Allah da Mala’ikun Sa suna yin Addu'a ta musamman ga masu yin Sahur, sai dai ana so ne a jinkirta Sahur ɗin zuwa dab da Al-fijir.
✍ *ANNASIHA TV*