MUNGO PARK MABUDIN KWARA 01




1. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
...
Mungo Park ya sayar da ransa domin neman suna, ya shigo Afirka domin warware wata tsohuwar takaddama da ta sha wa Turawa kai game da kogin Kwara (River Niger). A zuwansa na farko ya ci nasarar isa kogin Kwara, har ma ya sha daga gare shi, ya kuma yi wanka. Ya so ya bi tsawon kogin domin ya ga karshensa, amma saboda wasu matsaloli, bai samu damar yin haka ba, ya koma gida.
Bayan ya sake shiri, ya fito daga gida da zimmar sai ya ga kul uwar daka, watau sai ya ga inda kogin Kwara ya kare. Ya ratso kasahen Afirka da dama, yana biye da kogin Kwara. Ya sha bakar wahala, wanda daga karshe ya hadu da ajalinsa a hannun mayakan Yawuri ta kasar Kebbi, kusa da wani gari da ake kira Bussa. Mungo Park namijin duniya ne, wanda tarihi ba zai taba mantawa da shi ba. Shi ya sa ma Turawa ke yi masa lakabi da MUNGO PARK MABUDIN KWARA.
...
GABATARWA
AFIRKA kasan nan tamu, ta dade cikin duhu ga sauran duniya. Mutanen Turai sun yi shekara ta fi alfen da jin labarinta, amma labari ne kurum, ba su zo sun gane wa idonsu ba. Iyakar inda suka sani sai kasashen gefen Afirka na arewa na bakin Bahar Rum, sai kuma kasar Masar. Amma tsakiyar Afirka, ko Afirka ta Kudu, ko mu nan Afirka ta Yamma, duk ba su san mu ba, ba su san kome namu ba. Iyakar abin da ke kai wa kunnuwansu sai labarai irin na matafiya, masu ban tsoro. Wadansu sun ce tsakiyar Afirka babu kome sai daji kurum da duwatsu, wadansu sun ce sai bakaken Arna masu cin mutane. Wadansu sun ce duk Baturen da ya shigo, in mutanen kasar ba su cinye shi ba, cututtukan kasar za su kashe shi. Mu kuma a nan kasar, a lokacin in ka ji Iabarun ban dariya da kakannimmu su ke fada na Turawa sai ka san lalle suna da jahilcinsu kwarai.
Amma duk a lokacin nan babu abin da ke ruda mutanen Turai kamar labarin Kogin Kwara. Malaman labarin kasa, in suna cikin koyad da almajiransu, da ce sun zo kan wannan kogi sai su tsaya, su rasa abin cewa. Kamar shekara dubu biyu da suka wuce, wani babban malamin tarihi na Greece ya rubuta cewa matafiya sun gaya masa wannan kogi ya soma daga kusa da bakin teku ne, daga yamma, ya nausa ya nufi gabas, Daga baya kuma wadansu malamai, galibinsu Larabawa, suka rushe wannan magana, suka ce babu wani kogin da ya somo daga yammacin Afirka ya nufi gabas. Suka ce lallai akwai kogin da ake kira Kwara, amma daga gabas ya taso ya nufi Yamma. Galibi a kan haka aka tsaya, amma dai kowa yana ‘yar shakka a zuciyarsa ko haka ne, ko ba haka ne ba. Wadansu ma sun ce Kwara wutsiyar Kogin Nil ce. Wadansu kuma ma dungum suka ce babu wannan kogi a duniya. Wadan nan abubuwa su suka ruda duniya game da Kogin Kwara, da kuma ainihin yadda kasar Afirka da mutanenta su ke.
Ana cikin wannan tsinci-fadi, sai wadansu manyan mutane na Ingila suka hada kansu bisa niyyar bude kasar Afirka. Dalilin wannan niyya tasu kuwa don su san irin halin zaman mutanen kasar, su taimake su, su waye musu kai yadda za su ji dadin zaman duniya. Kamar shekara biyu kafin daura niyyan nan tasu, wadansu mutum biyu sun yi kuru sun zo don su duba kasar, amma dukansu babu wanda ya koma gida, balle ya kai labari. Daya daga cikinsu wai shi Manjo Houghton, za ku ji Mungo Park ya yi maganarsa nan gaba. Saboda haka su manyan nan suka yi shakkar samun mutumin da zai yarda ya sai da ransa ya zo Afirka. Suka dai sanad da jama’a bukatarsu. Sai wani Likita wai shi Mungo Park ya ce ya yarda ya zo. Wannan ba karamar kasada ba ce. Ba wadansu kudi aka ba shi wadanda suka tsone masa ido har ya zabi shiga wannan halaka ba. Zuciyarsa ce kurum ta dauki za ta yaye wa kanta duhun jahilcin kasan nan tamu ta Afirka. Saboda a ba da labarin wannan mutum shi ya sa muka rubuta wannan dan littafi. Amma za mu bar Mungo Park ya fadi labarin tafiyarsa da kansa, don an ce waka a bakin mai ita ta fi dadi. Sai dai kafin ya fara, bari mu dam fadi labarinsa daga haihuwa zuwa barinsa makaranta.
Mungo Park mutumin kasar Scotland ne arewacin Ingila, amma duka kasa guda ce da Ingila. Ubansa Mr. Park manomi ne. Ya auri wata mace, ita ma ’yar mutanen Scotland, wai ita Hislop. Ta haifi ’ya’ya goma sha uku. Mungo Park shi ne danta na bakwai. An haife shi ran 10 ga watan Satumba 1771. A gida ya fara karatu a hannun wani malami da uban ya ajiye don ya karantad da ’ya’yansa. Tun lokacin nan ya fara jin labarai masu ban tsoro, da na mutane masu karfin hali. Labaran nan su suka zauna masa a zuciya, suka karfafa shi ya zabi shiga wahalar zuwa nan kasar. Daga makarantar gida sai ya tafi makaranta ta sosai, daga nan kuma sai kolej. A can ya koyi aikin Likita. Daga nan ne ya fara barin gida ya kutsa kai duniya. Tafiyarsa ta fari ita ce wadda ya yi zuwa Tsibiran Indies a gabas cikin 1792. Da ya komo daga can ne ya zo nan Afirka. Bari mu ji abin da ya fadi cikin littafin tafiyarsa.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@hotmail.com
WhatsApp: +2348021218337
BBM: 2bddd505
BBM: d1d74969
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)