MUNGO PARK MABUDIN KWARA 02




2. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
...
NA SAUKA A GAMBIYA
Da komowata daga Tsibiran Indies, sai na sami Iabarin taron dattijan nan, da irin bukatar da su ke da ita game da bude kasar Afirka. Na kuma ji labarin mutane biyu da suka tafi, amma duka mutanen Afirka sun kashe su. Wannan labari, maimakon ya firgita ni sai ya kara karfafa mini zuciyar tafiya. Babu abin da na ke so sai in tafi wannan rufaffiyar kasa, in ga yadda ta ke, da yadda mutanenta su ke, da yadda su ke zaune. Na sani zan iya jure wahalar tafiyar, kuma ina da kuruciya da karfi, yadda zan iya jure ciwo im ba babba ne ba. Ba ladan kudi na ke kwadayin samu ba. Ni dai muradina in taimaki ’yan Adam da sanin asirin da ke boye cikin Afirka. In zan wahala, in wahala cikin i da nufina. In kuwa na iya bude wannan kasa ta Afirka, na fito da ita da mutanenta fili, na sani dattijai ne suka sa ni wannan aiki. Saboda haka ba zan yi wahaIar banza ba.
Da na yarda zan tafi, aka sa mini ranar tashi. Na bar Ingila ran 22 ga watan Mayu, 1795, a jirgin ruw. Ran 4 ga watan Yuni na fara hango duwatsun Afirka. Ran 21 ga watan jirgimmu ya isa Jilifiri, wani gari a bakin kogin Gambiya. Ran nan ne na fara taka kasar Afirka.
Muka kwana uku a garin. Da muka tashi, muka rabu da teku, muka shiga bin tsawon Kogin Gambiya, har muka isa wata tasha da a ke kira Jokakonda. Wannan gari masafarta ne kwarai na bayi da hauren giwa.
To, kafin im baro Ingila am ba ni wata takarda in kawo wa wani Bature dan ciniki, ana kiransa Dr. Laidley, yana zaune a wani gari mil goma sha shida daga Jokakonda. Sunan garin Pisania. Sai na ciro takardar na ba Kyaftin na jirgimmu, nan da nan ya aika masa. Gari na wayewa, sai ga Dr. Laidley ya zo ya tarye ni. Ya samam mini doki, na hau, muka juya sai Pisania. Ya kai ni gidansa, ya yi mini masauki mai kyau. Da na kwana biyu na huta, sai na tasam ma koyon harshen mutanen kasar. Aka gaya mini wai tun daga bakin teku har zuwa nesa cikin kasa babban harshen da ya kamata mutum ya koya shi ne Mandingo, don duk inda ka tafi ka sami abokin tadi. Aka ce muddin ban san Mandingo ba, ba yadda zan san kasar, ba yadda zan gane zaman mutanenta. Babban malamina shi ne Dr. Laidley, don kuwa shi ya dade a kasar, har in yana magana da Mandingo sai ka ce dan kasar ne. Nan da nan dai na fara ganewa.
Na ji an ce ko wane Bature ya zo kasar Afirka, sai zazzabi ya yi masa wani mugun bugu sa’an nan zai saba da kasar. Na ga na dan jima amma ko ciwon kai, sai na fara kada gindi ina murna, wai ni na haye tudun-mun-tsira. Ashe ba haka ba ne, tawa saukar da Afirka ke ba bakinta na Turai tana nan tafe! Ran 31 ga watan Yuli sai rana ta kama wata. Na fita waje na zauna, na dade ina kallon hasufi. Ana raba kuwa a daren. Ashe na kwashi sanyi Kashegari ban iya tashi daga gado ba, na sami mura mai zafi. Sai da na yi kusan wata daya a kwance. Allah ya yi mini arziki ga Dr. Laidley. Ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai da ya ga na warke tangaran.
Da warkewata, sai na ce da Dr. Laidley ya kamata in yi abin da ya kawo ni, zama wuri daya ba zai yiwu ba. Ya tambaya ko akwai wani ayarin da zai tashi zuwa cikin kasa a lokacin, don ya gama ni da su, ba a samu ba. Fataken da za su tafi cikin kasa ba su kare shiri ba tukuna, saboda haka ba a san ranar tashin ayarinsu ba. Da na ji haka, sai na ce to, ni zan yi gaba ni kadai, domin ba zan yarda in zauna ina tsammanin warabbuka ba. Saboda haka na shiga shirin tashi zuwa cikin Afirka. Sai dai kafin in ci gaba gara im ba ku labarin yadda mutanen bakin wannan mashahurin kogi na Gambiya su ke.
YADDA NA SAMI KASAR GAMBIYA
Ko da ya ke akwai mutane iri iri a wannan kasa, amma dai manyan kabilun da na tarar su ne Feluf, da Jalof, da Filani, da Mandingo. Galibinsu duk Addinin Musulunci su ke bi. Feluf mutane ne marasa hankali, marasa son mutane. An ce in sun kama fada tsakanin wannan da wannan ba su dainawa har jikoki. Kamar yadda a ke gadon dukiya wurin iyaye in sun mutu, haka su ke gadon fadan da ubansu ya bari. Har an ce im mutum ya mutu wurin fada, abin da dansa zai fara yi shi ne ya dauki faden uban. Su zai rika sawa sau daya tak a shekara, watau in ranar mutuwar uban ta zagayo. Daga wannan ranar kuma in ya cire, sai badi. Domin wannan wai don ya tuna da gayyar da zai rama, ya kuma tuna wa Wanda ya yi kisan. Amma wannan mummunar al’ada ta rashin yafe laifi ba ita ce kadai halinsu ba. Su mutane ne masu nuna godiya kwarai da kauna ga wanda ya yi musu alheri. Bayan wannan kuma duk babban kyakkyawan halinsu shi ne rike amanar da aka ba su. A ce dai yadda mutanen nan su ke da wadannan kyawawan hali, kuma sun san amfanin saka mugunta da alheri, su rika yafewa, ai da ba za a sami mutane nagari kamar su ba duk duniya.
Jalof kuwa su mutane ne masu karfin hali da jaruntaka. Sun iya saka ainun, kuma suna da baba mai kyau. Kyawawa ne dogaye, kamar Filani. Daga su sai Filani, wadannan ko’ina ana ganinsu, da shanunsu su ke yawo kasa kasa.
Bayansu sai Mandingo, su kuwa sun fi sauran kabilun kasar duka yawa. Harshensu kuma ya fi kowane harshe yaduwa. Suna da Sarki, amma Sarkin nan ba shi da mulki kwarai kamar Sauran sarakunan Afirka. Don na ga kafin ya hukunta kome sai ya tara majalisarsa ya shawarce su. Mandingo mutane ne masu dadin zama, masu son mutane. Galibinsu dogaye ne, samun gajere dukur a cikinsu da wuya, ga su da kokarin aiki da jure wahala. Matansu kuma kyawawa ne, masu son ado ga kuma fara’a.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.wordpress.com/
http://bukarmada.blogspot.com/
bukarmada@hotmail.com
BBM: 2bddd505
BBM: d1d74969
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)