5. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
...
Da muka tashi daga Tallika, ba mu yi tafiyar da ta fi mil biyu ba sai fada ya kaure tsakanin makeri da daya daga cikin mutanemmu, suka yi ta yi wa @bukarmada juna mugun zagi mara dadin ji. A wannan fada na fara gane abu daya game da Bakin Mutum, watau yana iya daurewa don ka buge shi, amma kana bude baki kana zaginsa ko wa ka ke, ba ya kyale ka sai ya rama. Sau da yawa na kan ji bayi, @bukarmada ga su a kangi, a buge su, a mangare su, ba su ce kome ba, amma da ce ubangijinsu ya zagi iyayensu sai su rama. Su kan ce, "In za ka buge mu, buge mu kawai, amma ban da zagi."
Mu kwana mu tashi har muka kai wani dan gari a ba kin Falema. Mutanen wurin masunta ne. Na tafi har bakin kogin, don in ga yadda su ke yin su. Da na dawo masauki, sai ga wani Balaraben @bukarmada arewa ya ce ya zo ne ya yi mini addu'a. Ya ce in kawo farar takarda ya rubuta mini wata aya. Na ba shi 'yan warkoki, ya rubuta, kuma ya yi mini addu'a muka Shafa. Shi wannan Balarabe sun sadu da Manjo Houghton lokacin da ya zo, har ya ce a kasarsu Houghton ya mutu.
Na tashi garin da azahar, muka dinga tafiya har kamar misalin karfe takwas na dare, kana na kai wani gari wai shi Nayemowa. Sarkin wannan gari mutumin kirki ne kwarai, ya yi mana masauki mai kyau, ya ba mu sa, muka yanka. Ni kuma na ba shi amba da dutsen wuya. @bukarmada
Mun shiga Birmin Fatekonda, ran 21 ga Disamba. Da ya ke duk Afirka babu gidan baki, tilas im mutum ya je bakunta ya nemi masauki. Da shigarmu garin, sai wani farken bayi ya kai mu gidansa, ya saukad da mu. Jim kadan sai ga Jakada daga fada ya ce da ni wai Sarki yana son ganina yanzu-yanzu, in dai ba gajiya ta yi mini yawa ne ba. Na bi Jakadan, muka tafi da tafintana Johnson. Jakada yana gaba, muna biye, har kotar gari. Na ga mun fita bayan gari, muka wuce gonaki, muka fara shiga daji. Kai, sai jikina ya fara sanyi, @bukarmada na yi zaton kila 'yam fashi ne suka yi mini tarko, ba Jakadan Sarki ba ne. Sai na tirje, na ce da Jakadan ni ba zan daga ba. Sai ya nuna mini mutum a gindin wata itaciya, ya ce Sarki ne. Al'adarsa ce da maraice ya zo bayan gari ya zauna. Haka kuma in yana son ganawa da wani babban bako. Ya ce daga shi, sai ni, sai tafintana kadai aka yarda mu tafi inda Sarki ya ke. Na dai daure na tafi.
Na yi gaisuwa, Sarki ya amsa da murna. Ya tambaye ni ko ina bukatar sayen bayi, ko zinariya. Na ce ni ba ciniki ya kawo @bukarmada ni nan kasar ba, zuwa na yi in ga yadda kasar ta ke, in ga irin mutanen da ke cikinta da al'adarsu.
Sarkin nan ana kiransa Almami, amma Arne ne, ba Musulmi ba ne. Na kuma ji mugu ne kwarai, domin ya cuci Manjo Houghton, ya sa aka washe shi karkaf ko ni kuwa ban yizaton zai kyale ni ba, ganin irin duban da ya ke yi mini. Saboda haka na tsorata kwarai. Na kai masa gaisuwa ta akwati daya na albarushi, da amba, da ganyen taba, da laimata, don in tsere wa @bukarmada muguntarsa. Kuma da ya ke na tabbata za a yi cajin kayana, tun kafin in zo gabansa sai na kwashe duk kayan amfani, na hankada jinkar dakina na boye. Da muka kare gaisawa na yi sallama na komo gari.
Kashegari da safe Sarki ya aika aka kira ni. Da na tafi kofar fada, aka ce in shiga. Tafintana da yaron Sarkin suka cire takalmansu, bisa al'adar kasarsu. Da muka shiga, muka sami Sarkin a zaune bisa tabarma. Ya sake tambayata dalilin wannan tafiya da na ke yi, na sake tabbatar masa cewa ba ciniki ya kawo ni ba, ganin kasa ya kawo ni. @bukarmada Ya tsaya shiru, sa'an nan ya ce shi a wurinsa ba shi yiwuwa a shiga wannan hadari don ganin kasa kurum. Ya ce in dai mutum ba ya yi hauka ne ba, ba zai tura kansa cikin halaka haka ba. Muna cikin wannan magana, sai ya shiga yaba kyaun wata shudiyar riga da na ke saye da ita. Na ga dai yabon ya cika yawa, har na gane lalle rigar ya ke so. Ko da ya ke a cikin rigunana babu mai kyau kamarta, amma tilas sai na cire na @bukarmada ba shi. Don kuwa in na ki, yana iya sawa a tare ni a yi mini fashi a kanta.
Ni kuma ya ba ni guzurin abinci mai yawa, ya ce in tafi gida, gobe in komo. Da gari ya waye na zo, sai na same shi kwance a kan gado, wai ba shi da lafiya, yana so in rage masa jini, Sai na yi shirin aiki, ina ta murna don tun ran da na koyi aikin Likita ban taba yi wa Sarkin yanka magani ba sai yau. Na ce ya miko dantsensa, ya miko na daure. Da na ga jini ya taru sosai, sai na bude akwatina @bukarmada na jawo aska. Sarki yana ganin kyallin aska zayau, sai ya karai, ya kwace hannunsa. Ya yi ta rokona im bari sai da maraice, wai ya ji sauki, ba kamar da ba. Sai da ya ga na mayad da askar sa'an nan hankalinsa ya kwanta, muka shiga tadi.
Bayan mun taba 'yar hira da shi, sai ya ce wai matansa suna so su gan ni. Na shiga. Da shiga, na same su a wani babban gida, wajen su goma sha biyu. Suka rufe ni da, kallo. Wadansu suna taba jikina, wadansu suna taba hancina. Suka ce farar fatan nan tawa ta karya ce, ba haka Allah ya yi ni ba. Suka ce wai tun ina yaro ne a ke tsoma ni a cikin madara, shi ya sa na yi fari haka. @bukarmada Hancina kuwa suka ce tun ina karami uwata ke jansa, dalilin da ya yi tsawo ya yi tsini haka ke nan. Tun ran da Allah ya yi ni, ban taba ganin matan da ba su jin kunyar roko kamarsu ba. Babu abin da ba su ce im ba su ba a jikina, hatta gashin kaina sai da wata ta roke ni, wai don yana da yauki, zai yi kyaun ado. Saboda haka sai na ba kowace dutsen wuya, amma ban yarda na ba da gashin kaina ba. Sarkin kuma ya ba ni awon zinariya biyar, muka yi sallama.
KASAR KAJA'AGA
Da dai na sami kaina, na fice sharrin wannan mugun Sarki na Fatikonda, ko tsayawa rana ta karya ban yi ba, sai na bar garin da tsakar rana. Muna tafe har muka kawo kan iyakar kasar Bondu da ta Kaja'aga. Aka gaya mini wai wannan kasa ce mai hadari kwarai ga fatake. Sai wani cikin jama'armu ya ce ya kamata mu saki hanya mu fasa ta daji, kuma dare za mu rika bi. @bukarmada Na kuwa ga wannan shawara mai fita ce ainun, na yarda. Saboda haka sai muka tsaya a inda mu ke, a kan iyaka muka huta. Can da dare ya yi sosai sai muka tashi, mu ka kimsa kai cikin kungurmin daji, dadin abin dai akwai farin wata kamar rana.
Ba ka jin motsin kome, daga na busasshen ganye da mu ke takawa sai kukan namun daji. Sai kuwa kowane jimawa ka ga kura, ko damisa, ko kyarkeci sun gitta. Cikimmu dai babu mai cewa kala, ko tari mai karfi ba mai yi. Haka muka kwana muna @bukarmada cikin wannan irin fargaba har gari ya yi shaa, sa'an nan muka isa wani gari wai shi Kimu, muka sauka muka yi kalaci, muka yi gaba.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
bukarmada@hotmail.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada