MUNGO PARK MABUDIN KWARA 04



4. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
...
Zaki ya banke su duka, ya kakkarya su ya kashe, ya cinye. Mutanen Damasansa suka firgita. Har yanzu kuwa ba su sake karambanin kama zaki da ransa ba." @bukarmada
Ran 3 ga Disamba, misalin karfe daya na rana, muka yi ban kwana da Dr. Laidley da sauran 'yan rakiyata. Su suka koma Pisania, ni kuma na dauki hanya. Na dubi tafiyar da ke gabana, da irin dajin da zan ratsa, da irin mutanen da zan tarar wadanda ba su san halin da duniya ke ciki ba, ba su ma san wata duniya im @bukarmada ba kasarsu ba. Galibinsu ma ba su taba ganin Bature ba. Da sun gan shi sai su kewaye shi, suna ganinsa kamar ba mutum ba ne. Wadansu kuwa da dubansa sun ga abinci, watakila su kashe shi, su kwashe kayansa. Da na duba na ga na rabu da Bature dan'uwana, na ga na rabu da kwanciyar hankali, da ganin idon sani, sai zuciyata ta yi baki kirin. @bukarmada
Ina cikin wannan tunani sai muka hangi wadansu mutane a guje. Da suka iso wurimmu suka tsayad da jakunansu, suka ce sai mu je wurin Sarkin Wulli, ko kuwa mu biya su kudin fito kana mu cira daga wurin. Na yi iyakar kokarina in sanad da su ba ciniki ko neman kudi ya kawo ni ba, amma duk a banza. Suka ce su alala sai dai im biya. Suka ce al'adarsu ce kowa ya shigo kasar lalle ya ba da gaisuwar Sarki, ko kuwa @bukarmada ya juya da baya ya fasa tafiyar. Da dai na ga sun ki mu yi jiyayya, kuma sun fi mu yawa sai na jawo ganyen taba nadi hudu na ce su kai wa Sarki. Sa'an nan ne aka ce in wuce.
NA SHIGA KASAR WULLI
Wulli kasa ce mai tuddai. Mutanen kasar Wulli Mandingo ne wadansu cikinsu Musulmi ne, amma akwai Arna a ciki. Arnan sun fi yawa, kuma su ne Sarakunan kasar. Suna kiran Sarkinsu Mansa, a hannunsa asalwayin @bukarmada mulki ya ke. Mai masaukina dan'uwan Sarki ne. Ya ce mini in na je gaban Sarki kada in ce zam ba shi hannu, don kuwa wannan ba al'adarsu ba ce, ko ga bako. Yamma ta yi, aka kai ni gaban Sarki. Na same shi a bisa kan tabarma, mutane sun kewaye shi maza da mata. Na yi gaisuwa, na kuma gaya masa ina neman izni @bukarmada ne in shiga kasarsa. Ya ce ya yarda, bayan yarda ma har zai taimake ni da addu'a. Ya yi addu'a, duk mutanen wurin suka shafa. Har wa yau kuma Sarkin ya ce zai taimake ni da mutum wanda zai fisshe ni, ya kai ni har kan iyakar kasa tasa. Na yi godiya, na koma masauki. Na aika masa da @bukarmada gaisuwar barasa, shi kuma ya aiko mini da abinci mai yawa.
Kashegari na tai fada da sassafe, don in yi ban kwana da Sarki, kuma ya ba ni dan rakiyar da ya alkawarta mini jiya. Na same shi yana zaune bisa kirgin sa, ga wuta gabansa rigis yana jin dimi. Da shigata ya dinga yi mini maraba, kamar ran nan muka fara saduwa. Sa'an nan ya ce mini, "Abin da na ke so da kai, @bukarmada Bature, ya kamata ka fasa wannan tafiya taka. Kasar Bakar Fata muguwar kasa ce, domin da ka wuce iyakar mulkina za a kashe ka. Haka na shawarci dan'uwanka Manjo Houghton, amma da ya ki ji, ya tafi, sai aka kashe shi a hanya tun bai kai inda ya yi nufi ba. Kai ma kuwa in ka ki jin tawa, @bukarmada kashe ka za su yi." Ya ce kada in zaci mutanen kasashen gaba duk kamar mutanen Wulli ne, wadanda suka saba da ganin Bature suna ma'amala da shi. Na yi masa godiya Rwarai da wannan shawara, amma na ce masa na rigaya na yi niyya, wani hadari duk ba zai sa in koma da baya ba. Da ya ji haka, sai ya kada kansa, amma bai sake ce mini kome ba, sai dai ya ce in azahar ta yi dan rakiyana zai zo. Da ya zo, muka tashi. @bukarmada
Ga mu nan sai Konja, wani dan kauye. Na sayi rago muka ba wani Sarawulli cikin masu dauke da kayana muka ce ya yanka mana. Can bayan an kare fida sai na ji fada ya kaure. Ko da na reko sai na ga da shi mai yankan ne da Johnson su ke kokawa a kan kahon ragon. Na tambayi dalili, sai na ji wai a wannan @bukarmada kasa kahon rago yana da daraja kwarai, don ana yin laya da shi. Na yi mamakin jahilcin mutanen nan kwarai. Na yi, na yi in raba su, suka ki. Sai da na karbi kahon na ba Sarawullin guda, na ba Johnson guda, sa'an nan ne kura ta kwanta. Babban abin da na gani game da Wannan kasa ta Afirka shi ne jahilcin mutanenta ya yi zurfi, duhun kansu ya yi yawa, har sun dauki rubutu, @bukarmada kowane iri, kamar wani babban sihiri ne. Ni kaina na yi amfani da wannan jahilci a lokacin da abu ya kure mini, na kuwa ga amfaninsa. Nan gaba za ka ga har yadda na zama malamin tsibbu.
Bayan mun kwana daya mun huta, muka yi gaba. Ga mu nan har wani gari wai shi Kujar. Mutanen garin suka taso, suka kewaye ni da kallo. Da maraice suka aiko a gaya mini wai za su yi wasan kokawa, in ina son kallo in je in gani. Kokawa tana daga cikin manyan wasanni na kasar Mandingo duka. Lokacin yana yi sai na shirya na tafi. @bukarmada Na tarar 'yan kallo sun yi wa filin zobe, ga 'yan kokawar daga tsakiya, sai ganguna ke tashi, suna ta rawa. Da dubansu ka san ba ran nan suka fara wannan wasa ba, kila tun tasowarsu da ita suka tashi. Kowane ya tube, daga shi sai dam feto a gindi, ya shafe cikin nan kaf da mai, sai sheki su ke yi. In za a fara bugawa, masu kokawar ba a tsaye su ke matsar juna ba. Duk sai su duka, suna tafe bisa @bukarmada hannayensu da kafafunsu. In sun zo kusa da juna, sai su dade a duke, kowa yana neman makasa a jikin dan'uwansa. Can sai daya ya yi wuf ya, kama kafar dayan. Sai su mike, kokawa ta sarke, su yi ta murde-murde, suna majejewa a filin har a yi kaye, wadansu kuma su kama. Ko wane dan kokawa ya daura akayo a kafa, yana rawa a gaban masu ganga.
MUN SHIGA KASAR BONDU
Da muka tashi daga wannan gari, muka dauki hanya cikin wani kungurmin daji. @bukarmada Muka kwana a ciki, gobe kuma muka sake kwana, ran kwana na uku muka isa Tallika, gari na farko cikin kasar Bondu daga Wulli. Shi kuwa Tallika garin Filani ne duka, kuma Musulmi ne. Mutanen suna da arziki, ga su dai da shanu, ga su a kan karaukar fatake, suna sayad da abinci da hauren giwa. A garin akwai jakadan Sarkin Bondu wanda aka ajiye musamman don karban kudin fito. @bukarmada A gidan Sarkin na sauka, kuma tare da jakadan muka tafi Fatkonda, babban birnin kasar Bondu.
Da muka tashi daga Tallika, ba mu yi tafiyar da ta fi mil biyu ba sai fada ya kaure tsakanin makeri da daya daga cikin mutanemmu, suka yi ta yi wa @bukarmada juna mugun zagi mara dadin ji. A wannan fada na fara gane abu daya game da Bakin Mutum, watau yana iya daurewa don ka buge shi, amma kana bude baki kana zaginsa ko wa ka ke, ba ya kyale ka sai ya rama. Sau da yawa na kan ji bayi, @bukarmada ga su a kangi, a buge su, a mangare su, ba su ce kome ba, amma da ce ubangijinsu ya zagi iyayensu sai su rama. Su kan ce, "In za ka buge mu, buge mu kawai, amma ban da zagi."
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.wordpress.com/
http://bukarmada.blogspot.com/
bukarmada@hotmail.com
BBM: 2bddd505
BBM: d1d74969
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)